← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 49

Sashe 26

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba yanda ta iya haka ta koma tana yi tana hutawa,tana hawaye har ta samu ta karasa da rarrafe,
Bata ma iya wankewa ba amma ji take daga hannun ta har ƙafarta duk ciyo suke mata,

Tana fitowa shi kuma yana dawowa daga sallar la'asar.

Murmushi ya sakar mata"biyo ni"

Bata ce mashi komai ba tabi bayan shi,dan ita yanzun ba tada bakin magana,dan ji take ko tayi ba zama aji me take faɗa ba saboda rashin Energy,

Sun ɗan yi tafiya me nisa a ciki kafin su iso wani ɗan madaidaicin Flat
Ganin ya shiga ne yasa ita ma ta shiga,falo ne mai dan girma yana ji kamar office ne,dan harda kujeru a ciki,zama yayi a kan daya tare da nuna mata wata kofa"ga banɗaki can ki shiga ki yi wanka,ga kuma kaya nan a leda ki ɗauka sai ki canja,dan ba zan iya bin hanya dake haka ba kina warin kashi"

Bata ce mashi komai ba ta dauki ledar ta shiga banɗaki wanda taga an haɗa mata ruwan wanka har baho biyu duka masu zafi yanda zata ji daɗin gasa jikin ta,
Ta jima sosai a bayin kafin ta kammala ta canja kaya wanda na yanzun riga da sike ne na Atamfa mai kyau kamar an auna jikinta,sai babban mayafi baƙi,harda mai a cikin kayan,
Tana kammalawa ta buɗe ƙofar ta fito,

Daga kai yayi ya kalle ta yana sakin murmushi "yauwa Sumi Baby ko ke fa,har kin fito a Amaryar ki," Tashi yayi ya zo gabanta yana jan hannun ta"nasan kina jin yunwa,ga abinci na sa an kawo maki "

Jin yace abinci ne yasa ta bishi babu turjiya dan ba karamin yunwa take ji ba,
Shinkafa ce fara da miya sai naman rago wanda aka saka yanka biyu manya,

Kokarin daukar plate take ta zuba,ya amsa plate din a hannun ta"kawo na zuba maki"

Tana kallo ya zuba madaidaicin chokali biyu,ya zuba miya da nama ɗaya a sama ya miko mata,
Kin karɓa tayi ta noke,

Ƙara Miko mata yayi"karɓa mana"

Girgiza kai tayi tana turo baki "ni wannan yamin kaɗan ka ƙara min"

"Wai me yasa kin cika ci ne,kin ga wallahi ko ki amsa ko na zauna na cinye,kuma in kika bari na cinye kin ma kanki dan ba zan siya wani abinci ba sai gobe kuma"

Dan marairaicewa tayi kamar zata saka mashi kuka"dan Allah mana Jauro,ko kaɗan ne"

Ganin yana ƙoƙarin mai da abincin gaban shi ne yasa da sauri ta amsa"kawo "ta faɗa tana turo baki,dan ji take kamar ta mangareshi da duka,ita wallahi tsakanin ta da Maman Momy Allah ya isa domin ita ta haɗa ta da wannan fitina.

Haka tana ji tana gani ya kinkime kulolin ya fita dasu,ta jima tana juya abincin kafin ta daure ma zuciyarta ta shigaci a hankali,sai dai kwata-kwata bai wuce loma goma sha biyar ba da tayi abincin ya kare,Allah sarki Sumi harda kankare plate take,

Shigowa yayi ya kalle ta ya kalli plate din,tabe baki yayi"tashi muje"

Mikewa tayi tabi bayan shi,sai dai tana fito taga wata Arniyar mota ƙiran Jip sabuwa dal a fake,
Gani tayi ya buɗe ƙofar motar ta baya "Bismillah" Ya mata nuni dashi,

Ita fa tsakanin jiya da yau kaɗai wallahi Jauro lamarinsa ya fara bata tsoro,irin wannan manyan motoci fa,wannan ba irin na jiya bane daya kawo su,haka duk da bata san yanayin kuɗin Hotel ba amma ta tabbatar da ɗakin da suka kwana jiya ba karamin ɗaki bane,ita dai Allah yasa ba haɗa baki sukayi da shi da Maman Momy da Baba ba su saida ita,
Tana shiga cikin motar shima ya zagaya ya shiga in da take,yayin da direba yaja motar suka bar wannan gidan gonar da bata fatan sake zuwan shi.

A tunanin ta gidan su na jiya da aka kaita zasu koma,sai dai gani tayi an shigo dasu harabar Hotel din jiya,
Hakanne yasa ta kalle shi,duk da ta ga idon shi a rufe amma ta san ba barci yake ba,"ina ce gida zamu koma"

Kin bata amsa yayi kamar bai jita ba,

Kara maimaitamai ta yi "na ce ba gida zamu koma ba?

Ɗan buɗe ido kaɗan yayi" Hala dai ke kike biya min kuɗin daki,da zaki dame ni"gyara zama yayi da kyau yana buɗe idanun shi tar a kanta"me yasa wai ku mata kuna da matsala ne"

Katse shi tayi"ai duk matsalar mu bamu kai na wani ba,mai kai matar shi Amarya sharan kashin kaji a yinin ta na farko tare dashi"ta fada tana kauda kai kamar ba ita tayi magana ba,

Ɗan zaro ido yayi"me kika ce?

Ita ma kin kula shi tayi,sai ma buɗe ƙofar motar da tayi ta fita ganin sun iso,

"Zan yi maganin ki" Ya fada shima yana fitowa,

Ta rigashi isa kofar amma saboda makulli na hannun shi dole ta tsaya sai da ya iso sannan ya buɗe ƙofar suka shiga,

Faɗawa tayi kan kushin tana sauke numfashi tare ɗin "wash Allah baya na"

Tsaki ya ja "mutum sai lalaci"

Ita dai bata kula shi ba sai juye juyen da take yi kan kushin,dan ji take gaba ɗaya jikinta ciyo yane mata,har balle Kwankwaso,

Yana shiga daki wasu takardu ya ɗauka ya ƙara fita,

A nan kwancen da take tunanin Mama ya faɗo mata,yanzun ko a wani hali take,kila ma su Aunty Amina suje kai mata sauran kayan su iske gida ba kowa,Allah sarki Mama,
A fili ta furta"ina kewarki Mama "haka dai ta zauna a wannan dakin ita ɗaya,gashi ba tada waya balle ya ɗebe mata kewa ko ta kira gida taji muryar su,
Har aka kira sallar Isha'i tayi sallah bai dawo ba,
Anan in da tayi sallah ta kwanta saman darduma,nan take kuwa barci yayi gaba da ita,wanda tana yi ne tana juye juye,

Bashi ya shigoba sai kusan ƙarfe tare,
Yana ajiye ledan da ya shigo dashi ya shiga banɗaki yayi wanka ya saka kayan barci,

Kallon ta yayi yanda ta kwanta a kasa ta dunƙule da hijaba alamun sanyi take ji,

Daukar rimot din AC yayi ya rage sanyi,sannan ya ƙarasa in da take kwance,
A hankali cikin budara yanda ba zai tashe ta ba ya zame mata hijabin da ta rufe dashi,
Filon da ya dauko ya saka a gabanta ya dan guyata sai ya kasance kamar ta rungume filon ne ta bashi baya,
Hakan ne ya bashi damar zuge mata zip din rigar ta wanda ya tsaya iya Kwankwaso,ya zamana yana ganin fatar bayanta,

Kallon farin fatar bayan nata yake wanda yake fari tas dashi,kamar mai maganar zuci haka yake kyada kai,

Wani dan karamin gwangwani ya ciro a leda wanda daga dukkan alamu Oiltement ne na baya,
Lakuta kaɗan yayi a tafin hannun shi ya mussuka sosai sannan ya shiga yi mata wani irin tattausar danna yana yawo da hannun shi a bayanta har zuwa Kwankwaso,

Baiwar Allah,cikin barci taji kamar ana mata tafiyar tsutsa a baya mai daɗi ai tuni ta ƙara kifewa tana bashi damar Gara danna da ƙyau,

Ganin abinda tayi ne yasa shi murmusawa,

Ya dau tsayin lokaci mai yawa yana aikin danna mata jiki har zuwa hannayen ta da tafin kafarta,kafin a hankali ya kuma daukarta ya maida ita saman gado yana rufe ta da bargo,sai dai bai maida mata da zip din rigar ta ba kamar yanda bai cire mata rigar ba,ta yanda ba zai takura mata ba wurin barci.......

*ASUBA TA GARI SUMI JAURO*

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*34*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

Washegari da Asuba ta rigashi tashi,miƙa tayi tana karanto Addu'ar tashi daga barci,
Ji take gaba ɗaya jikinta ya sake ba inda ke mata ciyo,
Murmushi ta sake tana saukowa da ƙafarta a hankali ta mike sannan ta nufi banɗaki,
Wanka tayi ta fito ta canja kaya,wanda a lokacin ne ya tashi,
Kallon agogon dake manne jikin bango yayi da sauri ya maida kanshi kanta sannan ya zabura ya mike shima yayi bandakin,dan saura kaɗan ya makara,

Tana isar da sallar tashi tayi ta koma falo ta zauna,dan ji take gaba ɗaya zaman ya ishe ta,
TV ta kunna tana kallon labarai har kusan Ƙarfe tara.

Jin motsi a gefen ta ne yasa ta juyo tana kallon shi,ikon Allah,shi gaba ɗaya wai kayanshi na Gonjo ne,
Ya wani saka boturin riga har wuya sai kace ɗan zamin 1950,

"Me kike kallo na" Ya faɗa har da ɗaga mata gira,

Bata masan sanda ta fashe da dariya ba,dan wallahi abun ko kyau bai mashi ba,

Kallon ta yake yana nazarin me take ma dariya "Sumi Baby me kike ma ɗariya "

Nuna shi tayi da hannu"yanzun kai dan Allah ko kunyar fita a haka ba ji,
Ka ganka kuwa,wannan yanda kasan wanda aka dauko daga 1950" Ta faɗa tana kara fashewa da wata dariyar.

Kallon kayanshi yayi ya kalli Sumayya yanda take ta kwasan dariya kamar ta samu wawa,"amma dai kam Sumayya baki tsoron Allah,kin San kuwa yanda ƴan mata ke bina na aure su ?

"A'a Jauro karka shuto min tun da safiyar nan,ai ko ƴan matan ƙauye sun waye yanzun sun san wanka"

Ji yayi ranshi ya fara baci,dan haka bai kulata ba ya nemi guri kan kushin ɗin ya zauna shima,yana sauraren yanda take mai dariya,

Ganin bai kula ta bane yasa tayi shiru tana kyara zama"ni fa yunwa nake ji"

Gani tayi ya dauki Telephone ya danna wasu number sai kuma taji yana bada ordan abinda za'a kawo,

Kyaran murya ta yi tana ɗan marairaicewa "Jauro" Ta kira sunan shi,

Kin juyowa ya kulata yayi,sai ma ƙara kauda kai da yayi,

"Jauro" Ta kara fadada a ɗan shagwabe,

Nan ma bai juyo ba,

Ɗan langwabe kai tayi "please mana ka kula ni"

Juyowa yayi yana kallon ta sai dai bai ce mata komai ba,
Chapter 26 · 0% Book details