← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 49

Sashe 7

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga ranar da ya kira waɗannan Fulanin a gidansu shi kenan ya samu wurin zuwa wasa dan a gidan sunada yara sosai,
A cikin su a kwai wanda ake kira da Moha yaron zai kai shekara goma,yana da son karatu sosai,yana zuwa makarantar Boko dan alokacin yana primary four ne,
Tunda yaga yana karatu shikenan abun ya shiga ranshi ya manne mashi duk inda yayi yana like dashi wai sai ya koya mashi,
Washegari da safe kuwa tunda safe kuwa ya tashi ya tafi gidan su Moha,tare suka karya,sai da zai tafi makaranta labari ya canja,domin kuwa da kuka da ihu da komai aka raba su,

Ko da ya dawo gida ba karamin na ci ya dinga ma Baffa da Halima ba akan su bar shi ya dinga bin Moha amma sun ƙi amincewa,

Ko da Goggo Badejo ta shigo dakin yana kwance yana barci amma sai faman sauke ajiyar zuciya yake,

Kallon shi tayi ta kalli Halima dake zaune tana dama fura,
Zama tayi a kusa da ita tana nuna shi"shi kuma wannan ne akai masa da saffafen nen yake faman sauke a jiyar zuciya?

Ita ma kallon shi tayi tana tabe baki"kwana biyun nan rigima yake ji wai sai an saka shi makarantar Bokoko,ganin wani ɗan mikotan mu na zuwa"

"Oh Boko,ai makaranta ce,kuma bashi da wata illa,kinga ko mu a wurin mu yara na zuwa sosai,ni ma bana zan saka Muntari,kin ga ma shi yana so me zai sa kuma hana shi,kawai ku bar shi ya je"

Kallon ta tayi"to sai dai kima ubansa magana dan ni babu ruwa na"ta faɗa tana mika mata lafiyayyen kwaryan kindirmon data dama.

"A'a bana Jauro bane?

" Ke dai karɓi bari na dama mashi wani"

Amsa tayi,shi yasa duk cikin gidan tafi shiri da ita saboda ba tada rowa"an jima zan ma Dottiya magana gobe da kaina zan kai shi makarantar tunda yana so"
Da haka dai suka ci gaba da hira,
Haka kuma akayi,kamar yanda ta faɗa haka tayi ma Dottiya magana,kuma ya amince,tare da faɗin,ai idan ya gaji da kanshi zai bar zuwa,
Washegari kuwa da taimakon Moha ta je makaranta su dake Chancaga makarantar Government ne,ta kammala mai komai inda a lokacin kyauta aka bashi kayan makaranta harda takardu,sannan aka nuna mashi ajin shi aji Daya wato Primary one dan a makarantar Government ba suyin Nursery class,wannan kenan.

Ta ɓangaren Baffa Dottiya kuwa tambayar shi Baffa Bube yayi a lokacin suna dakin Inna Mari da safe sun haɗu wurin gaishe ta "ni ko Dottiya yanzun dabbobin ka sunkai guda nawa?

Kallon ɗan uwan nashi yayi" Garke biyu da yan kai,sai tumakai"

Duk kallon mamaki suke mai harda Inna "yanzun dabbobin ka har sun kai garke biyu bancin tumakai?

" Eh"

"Amma shine nawa dabbobin yanzun da suka rage ko garke daya basu kai ba,ko dai kana bin ta wata hanyar ne Dottiya"

"Ah to faɗa mashi,ni dai duk wanda ya dauko fitinar shi ta tsaya can a kan shi" Cawar Inna,

Kallon su yake cikin mamaki"yanzun ni zaku ma irin wannan zargin kuma har da ke Inna,haba sai kace bake kika haife ni ba"

"Yo ko ni na haife ka ai kullun cikin canza hali kuke,balle kai da kayi sheka hudu baka gida"

Kafin ma ya samu damar mata magana sai ji yayi Bube yace "To ni dai ina rokan ka bani kiyon iri koda shanaye guda ishirin ne"

Kallon mamaki yake mai "in baka fa kiyo kace,bancin naka wanda kake dasu"

"Kwarai kuwa ai kiyo nace ba kwayta ba"

"To ba zan iya ba" Ya faɗa yana mikewa,

Inna ce tace"kai ko ai kyauta ma kana iya ba dan uwan ka"

"Inna ki ƙyale shi yaje ya gani in dai ni ya ma haka"

Bai kula suba ya juya ya wuce yana kananun magana,dan bai zaci haka daga ɗan uwan shi ba,

A washegarin ranar ne Halima ta tashi da matsanancin ciyon ciki,wanda tun tana daukar abin da wasa har ya fara cin karfinta,gashi Dottiya ya fita cikin gari,shi kuma Jauro ya tafi makaranta,

Abu kamar wasa duk maganin da take tunanin zai taimaka mata tasha amma abu kamar ƙaruwa yake,ji take cikin jikinta ya dawo mata zuciya ya tsaya,
Tun tana iya tashi har yakai ta fara fita haiyacinta domin kuwa jini ne ya balle mata,gashi a lokacin cikinta ko wata tara bai gama shiga ba,
Dama kuma matan gidan ba shiga shiyan juna suke yi ba balle Allah ya kawo mata wani,dama ace Goggo Badejo na nan ne,to sai dai shekaran jiya ta koma,

Tana cikin haka ne Allah ya dawo da Jauro sai dai lokacin ko magana bata iya yi,gashi jini duk ya bata wuri,
Duk da kasan cewar shi yaro a lokacin yasan jini,domin yasan lokacin da Mamar su Moha suka sai Binta asibiti lokacin da take zubar da jini,

Dan haka da sauri ya fita yayi gidan su Moha,sai dai cikin rashin sa'a bai tarad da kowa ba a gidan,domin kuwa sun je suna a wani ruga dake gaban nasu,

Hakan ne yasa da gudu ya dawo gida ya shiga shiyan Binta,wacce ke zaune tana cin abinci,tsabar rudewa har yana mata ƙwallo da kofin ruwa dake gabanta,
Aikuwa ba tayi kasa a guiwa ba wurin dauke shi da mari"kai wani irin ɗan b.... Yaro ne,baka ganin gabanka ne"ta tureshi tana daga kofin ruwan gabanta"maza tashi ka barmin shiyana,kafin in balla ka,hala ma leken Asiri uwarka ta turo ka min"

Kuka ya fashe da shi domin marin ba karamin shigar shi yayi ba,
Duk da haka sai da ya ɗan maso kusa da ita cikin kuka yace"Innan Ɗan Fodiyo dan Allah kije ki duba Inna ta ba tada lafiya jini ya bata ɗakin mu "

"Me kace?

Nan ya kara maimaita mata abinda yace,

Wani harara ta zuba mai,wanda yasa sai da ya matsa baya" Dallah matsa ka ban wuri,ni lokacin da ciki na ya zube ina ce mamarka tana nan kuma tana kallo,dan haka ita ma nata cikin ya zube,taji yanda naji, fitar min a shiya munafiki"ta faɗa tana nuna mashi kofar fita,

Da kuka ya fita ya koma shiyan su,zuwa yayi ya tsaya a kanta yana kallon yanda take fitar da numfashi da kyar,
Tsugunnawa yayi a gabanta yana kuka ya rike hannun ta"Inna,Inna"ya kira sunan ta,
Da kyar ta iya buɗe ido ta kalle shi,
"Na je kiran innar su Moha babu kowa a gidan,da zasu kaiki inda suka kai Innan Ɗan Fodiyo,
Itama na naje kiranta tace ba zata zo ba," Gani yayi ta maida ido ta kara lumshewa,jijjigata ya yi"Inna ki tashi muje inda aka kai Innan Ɗan Fodiyo ke ma zaki samu sauki"ganin bata buɗe ido bane yace"bari na je na faɗawa Innan su Yabbale,

Sake hannunta yayi ya fita da gudu,bai tsaya ko ina ba sai shiyan Kande.....

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*10*

Bai tsaya ko'ina ba sai shiyan kande,
A lokacin tana kicin tana tankaden gari,da sauri ya rike hannun ta"Innan Yabale ɗan Allah ki zo ki duba Inna ta bata magana kuma jini ya bata ɗakin mu,"

"A'a Jauro sake ni kar kasa na zubar da garin tuwo,"

Matsawa gefe yayi ya tsaya yana kallon ta har ta kammala tankaden ta sannan ta kalleshi,ganin har yanzun kuka yake,"me ya sameta "

"Ni ma ban sani ba,sai dai bata magana"

Tsaki taja tana kallon aikin dake gabanta,gashi har ƙarfe biyu ta wuce ko tuwo bata gama ba,
Kara kallon shi tayi"Jauro,ina ganin ka je kawai idan na gama girki zan zo na same ka"

Gyada mata kai yayi yana juyawa cike da fatan ta gama da wuri ta zo,
Har ya kusa fita daga shiyan ta kuma kiran sunan shi,
Dawowa yayi,
"Jinin da yawa yaje zuba ne? Ta tambaya,

" Eh da yawa ne"

"To karka damu yanzun zan zo kaga har nayi talge saura tukawa sai nayi miya,

Nan ma kai ya gyada mata,
" Yauwa to ka faɗa ma Inna Mari kuwa?

Girgiza kai yayi,

"To kaje itama ka faɗa mata ko akwai wani iccen da zata ba ka sai ka jika ma innar ka,yi maza ka tafi"

Da sauri kuwa ya fita, duk da yana tsoron shiga shiyan sai da ya leka dan ya gani ko Binta bata tsaka gida,sai dai tana ma zaune ne a tsakar gidan,
Rasa yanda zai yi yayi dan haka dole ya samu wuri ya tsaya a ƙofar gidan yana jiran ya gani ko Allah zai sa ta shiga cikin daki,
A haka sai da ya kwashe kusan minti talatin kafin ya samu ta shiga daki,

Da gudu kuwa ya shige cikin gidan yana shiga dakin Inna Mari,wacce ke zaune tana saka mafecin rufe ƙwarya,
Allah sarki yaci kuka har hawaye ya bushe a idon shi,muryanshi ya shake baya fita sosai,
Tsugunnawa yayi a gabanta yana rike hannun ta"Inna Mari ɗan Allah ki taimaki Inna ta bata magana,sannan akwai jini a dakin mu,ɗan Allah muje ki ganta"

Ture shi tayi"kai matsa ka ban wuri,ni bani iya zuwa ko'ina dan yau da ciyon kafa na tashi ba zan iya zuwa ko'ina ba dauko min wancan ledan "
Da sauri ya dauko mata ledan,

Wani kullin magani ta ciro ta mika mai"amsa jeka jika mata ka bata tasha,ƙila nakuda take yi"

Amsa yayi yana kallon ta"to ba zaki je ki dubata ba Inna "

"Kai me yasa ka cika kunata je ka kai mata kawai ai tasan yanda zatayi dashi"

Tashi yayi ya fita daga dakin,yana kallon mugun kallon da Binta ke bin shi dashi,sai dai tunda ya kalle ta sau daya bai kara yarda ya kalle inda take ba har yabar shiyan,
Chapter 7 · 0% Book details