← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 49

Sashe 46

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ta ɓangaren shi kuwa sai bayan sallah Azahar ya kammala abinda zai yi,sannan ya shiga mota,bai tsaya ko'ina ba sai Limawa a ƙofar gidan Baba,
Ya jima a ƙofar gidan bai samu wanda zai aika ba,kamar ance mai ya kalli gefen shi sai gashi ya hango Auta tana tahowa Alamun daga aika take,
Ajiyar zuciya ya sauke,sannan ya sauka daga saman mashin din da yake,dan da mashin yazo,
Sunanta ya kira yana daga mata hannu "Auta,Aisha"

Jin ana kiranta ne yasa ta juyo,ai kuwa tana hangoshi ta hau washe baki da gudu ta karaso inda yake ta rungume shi tana dariya,
Shima dariyan yake"ina kika fito haka?

"Mama ce ta aike ni"
"To ƴar mama,ya jikin Aunty Amina?

" Ta ji sauki "
"Sosai? Ya tambaya yana son tabbatar wa.
Jinjina ki tayi" Sosai"
"Tana tafiya"
"Eh tana tafiya sai dai tana dingishi"
"To jiki ciki ki ce mata inji ni wai dan Allah tazo ina son magana da ita"
"To uncle Jauro,"
Da gudu kuwa ta shiga cikin gida ta shiga dakin su,
Mama dake tsakar gida tana fama da uban wanke-wanke na gidan yanda kasan na gidan biki,dan tana zaune Goggo ta shigo wai ta fito tayi wanke-wanke,ya ta iya haka ta fito dole tunda acikin gidan su take zaune,abincin dako Aisha ba'a iya ma tayin shi amma suna sata aiki saboda ta rabe su,
Jirjiza kai tayi domin ta hanata gudu amma baji za tayi ba,sai dai Allah ya shirya,

Gani tayi sun fito ita da Amina,"ina zaku"ta tambaya,dan har yanzun jikin Amina da zazzabi,shi yasa data nace akan sai ta bata wanke-wanke tayi ta hana ta,
Matsowa tayi in da Mama take dan taga yanda ƴan gidan suka wani maida hankali kanta,
A hankali ta faɗa mata sakon Jauro,dafe kirji tayi"Allah tasa ba wata magana Sumaiya ta dauko min ba?

"In sha Allah ba komai Mama,ai yaron nada hankali bari dai naje naji ko menene?

" Shi kenan"

Tana fita ta same shi a wani dakali na ƙofar gidan a zaune,
Sallamah ta mai "kanina ya ka ke"

Da sauri ya Mike tsaye yana nuna mata inda ya tashi"zauna nan Aunty mu"

Dan murmushi tayi tana jirjiza kai"A'a ba sai na zauna ba"

"Dan Allah ki zauna"
Ba yanda ta iya tunda ya haɗa ta da Allah,dole ta zauna,

"Ya jikin naki"
"Da sauƙi,sosai"
Jinjina kan yayi"gaskiya Dahir bai kyauta ba,in sha Allah sai ya gane kuran shi "

"Umm" Kawai ta iya cewa.

"Aunty Amina dan Allah so nake nayi magana da Mama,amma ban san ta yanda za'ayi ba,tunda gidan naga na jama'a ne,"

"Haka ne gaskiya kam,sai dai in zaka tsaya a ta cikin zaure sai na mata magana ta fito"

"Kina ganin babu damuwa!

" Eh babu,bari a mata magana "

"To,ina jira,amma har da kema ki dawo pls"

"To"

Komawa tayi cikin gida ta faɗa ma Mama yanda suka yi,kallon wanke-wanke dake gabanta tayi wanda ko rabi bata yi ba,
"Kira Aisha ta zo ta kama,ko ƙanana ne sai ta fara wanke wa"

"To Mama bari na ɗauko tabarma"

Ta riga Mama fita ta shimfida Tabarma sannan ta mai iso,
Yana ganin fitowar Mama ya mike tsaye da sauri,ya shiga gaishe ta bayan sun amsa sallamar ta shida Amina,

"Zauna mana Jauro"
Komawa yayi ya zauna,yana dukar da kai,

"Amina ta faɗa min kana son ganin mu,ina fata lafiya ba Sumaiya ɓace ta dauko min magana"

Murmushi yayi jin an kira sunan masoyiyar shi,"A'a Mama babu abinda tayi,tana ma barci na fita"

Gani yayi ta dafe kirji tana hamdala,Allah sarki duk sai ta bashi tausayi,

"Tun ina da Shekara takwas Allah yama iyaye na rasuwa,bansan daɗin mutum ya tashi da iyayen shi ba,na tashi cikin kewa da kaɗai cin su,ina rokon Allah ya bani mata wacce zata ɗebe min wannan kewar,sai Allah ya shigo da Sumaiya rayuwa ta,Mama ba zan ɓoye maki ba,ina matukar son Sumaiya tamkar rayuwa ta,duk wani abinda zai dame ta ya hana ta farin ciki ba na so,
Na roƙe ta akan ko zata yarda nima na zama daya daga cikin Ahalin ta,ta kuma amince min,
Mama ina rokon ki bani dama na zama ɗa a gare ki na har abada,bawai Siriki ba"ya faɗa yana dukar da kai,

Share hawayen daya zubo mata tayi tana godewa Allah "ni dama tuntuni kallon ɗa na nake maka Jauro,sai da tunda ka roƙi na zama mahaifiya a gare ka,ba zan kiba,domin ɗa na kowa ne,Allah ya maka Albarka,kuma a duk lokacin da kake da bukatar ganin mahaifiyar ka,kazo ka same ni,ka dai na min kallo a matsayin mahaifiyar matar ka,ka kalle ni a matsayin taka mahaifiyar,idan kana da matsala ka zo wurin mahaifiyar ka"ta faɗa ta tabbatar mashi da kalamanta.

Shi kanshi da Aunty Amina dake gefe duk hawaye suke"na gode Mama,na gode sosai,Allah ya bar mana ke"

"Amin Dana"

"Ina kuma mai baku haƙuri,da Jaje akan abun daya daru a jiya,kuma Aunty Amina nima ina bayan ki,ba zaki koma wannan gidan ba,mun gode ma Allah tunda Baban yaran da Kakansu na son su,ba zasu bari wani abu ya same su ba ko ya cutar dasu,in sha Allah zasu rayu babu matsala,
Sannan Mama dan Allah ina rokon ki akan karki ce A'a,ko Sumaiya bata San da wannan hukuncin dana yanke ba,
A kwai gidan dana siya a Padukwai zaku koma da zama can,na riga na saka an kammala kyara komai na gidan,wanda dama na siya tun last year ne amma ba kowa a ciki,
Ina ganin idan kun koma can hankalin ku zai fi kwanciya,Baba ba zai takura maku ba,har balle ke Aunty Amina kina bukatar hutu da kwanciyar hankali,dan Allah Mama karki ce haka a matsayina na ɗan ki "

"Tab,lallai Jauro ya iya daure mutum da jijiyoyin jikin shi,yanzun dai baza iya ci masa musu ba"

"Kana ganin babu matsala Jauro,bana son fa abunda zai je ya dawo"

"Mama in sha Allah babu komai na maki Alkawari"

Ajiyar zuciya ta sauke "shi kenan Jauro,yaushe zamu koma"

"Ai yanzun haka mota na hanya wanda zai zo ya dauke ku"

Duk kallon mamaki take mai"yanzun haka"

"Eh Mama,"

"Gashi Baba baya gida,sai dai zuwa yamma in ya dawo sai na mai bayani,sai mu tafi"

"To Mama,dan Allah karki faɗa masa komai,ina nufin karki fada masa ni na bada gida"

"In sha Allah mun kuma gode Jauro Allah Ubangiji ya maka Albarka,ya baka zuriya na gari"

Sosai yaji daɗin wannan addu'ar nata kafin ya mata sallamah ya wuce.

Baba bai dawo ba sai kusan biyar na yamma,
Har dakin shi ta shiga ta same shi,gaida shi tayi sannan cikin,ba tare data damu da yanda yake wani haɗe fuska ba,"Baba mun samu gida a unguwar Padukwai zamu koma yau,na gode sosai da karɓa ta da kayi a karo na biyu"

"Me yasa zaki kama haya,ko kin manta ba kiɗa gidan da yafi nan ne,ko kuma kin raina dakin da aka baki"

"A'a Baba,ba na son na sake jikina ne Alhalin gida na magada ne,ko yaushe suna iya buƙatar abin su,dama kuma ka ce na yi kokarin na koma gidan mijina tunda nan ba ni da gado,shi yasa nake son na bar nan kafin na manta hakan,ƴan kudin dake hannu na nayi amfani na kama mana haya,ina ga hakan zai fi,yanzun zamu tafi dama kai nake jira ka dawo saboda muyi sallamah,na gode Allah ya ƙara lafiya "

Gabaɗaya yama rasa me zai ce mata,jikin shi yayi sanyi,domin bai taba sammanin zata tashi nan kusa ba,bai yi sammanin maganar daya faɗa mata tare ke har ya mata ciyon da zata iya maimaita mai ba,tunda take dashi komai munin gorin da zai mata tun tana budurwa har zuwa yanzun bata taba daga kai ta kalle shi sai dai tace to,ko kuma tayi shiru,
Yau dai kam jikin shi yayi sanyi,ji yake kamar yace tayi haƙuri ta dawo,sai dai ba zai iya ba,yasan duk in da zata je ba zata yi karko ba dole dai ta dawo gida,

"To ita wannan yar taki haka zaki ta yawo da ita da auren ta?

" Auren ya mutu tun daga lokacin da ya daga hannu shida Uwar shi suka mata duka,"tana gama fadar haka ta tashi ta fita,

A tsakar gidan ta samu mutanen gida tsattaye suna kallon yanda wasu samari biyu ke fitar da kaya,

"Goggon ni zan wuce domin mun samu haya a unguwar Padukwai"

Amaryar Baba cikin bakin ciki,domin bata so haka ba tace"to yanzun ga wanke-wanke na hada amma sai kin tsaya kin yi min sannan ki tafi ko,tunda dazu kin ma goggo"

Bata bata amsa ba sai murmushi da tayi kawai ta kada kanta ta fita rike da hannun Allah yayin da Amina ke binda a baya,tana ƙara gode wa Allah.

Babu wanda yace bari ya bi su yaga ina zasu koma,dan haka suna shiga mota mai mota ya ja suka wuce,

Gidan bai da nisa da bakin titi,babban Get ne sai Flat guda biyu,sai dai ɗayan ba kowa,daya kuma shine nasu,dakuna uku ne aciki, sai wurin ajiye tarkace,da kicin da kuma dakin zuba abinci wanda babu kalan abinci da babu a ciki,harda jarkan manja dana man kyada,
Ɗakunan kuma na Mama yanda kasan dakin amarya,haka na Aunty Amina,ita kanta auta an kyara mata daki daya harda gado da dura irin wanda ake jera takardon karantawa,dakin yara ƴan gayu tsaf,sai tsalle take saman gado tana ihun murna,
Gabaɗaya ma ta rasa da wani baki zata saka ma wannan yaro Albarka,har Sujada tayi ta godewa Allah,
Dole kayan su a dakin ajiye tarkace suka jibgasu,sai abubuwan buƙata kamar dai kayan sawar su kadai suka cire,
Zuwa Magrib kuma sai da wata mata likita ta toro tazo ta yi treatment din Aunty Amina,tare da bata magunguna,ta kuma dauki duk in da ta ji ciwo hoto, sannan tai masu sallamah ta wuce.
*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*55*
Chapter 46 · 0% Book details