Sashe 24
Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ce mata tayi ta shiga,ita kuma ta jawo plate din tana buɗewa,wani irin soyayyen kwai ne wanda take ganen irin wannan suyar a wurin turawa,abu fari kar ba'a kife shi ya soyuba ga Yellow din ma har wani rawa yake alamar daka taɓa ruwan ciki zai fito,da sauri ta jayeshi gefe,ta dawo dayan,shi kuma ɗan yankan kankana ne karami wanda bai wuci loma biyu ba sai Apple madaidaici guda daya,
Ji tayi kamar ta fashe da kuka,hango fulas ɗan ƙarami da kofi ne yasa ta jawo shi,tana addu'ar Allah yasa koko ne a ciki,sai dai tana tsiyayawa taga ruwan Liptop ne a ciki,sai dai kuma sai kamshi mai daɗi yake fitarwa,hakan ne ya ja ra'ayin ta harta sha Liptop din wanda sai da ta juye duka karamin fulas din kofi biyu kenan,tas ta shanye amma ji take kamar ruwa kawai tasha,
Jawo plate din da Kankanan yake tayi,to shine ma data ci taji cikinta ya ɗan daga amma kaɗan,
Dan maganar gaskiya ta saba a gida ta ci malmala biyu na sauran tuwo da safe,in kuma Koko ne sai ta cika babban kofin silba,amma dan rai nin wayau shine yanzun Jauro zai haɗa ta da kayan kwalama a matsayin abin kari,gaskiya ba zata iya ba,ba tada jimirin yunwa,
Matar na fitowa ta dakatar da ita,cikin harshen Turanci take tambayarta "zan iya samun wani abinci bayan wannan?
" Eh me kike so"
Kallon Agogon bango na falon tayi,shadaya tayi"zan samu Sakwara da miyar ganye "
"Eh zaki samu,muna da ferfeson kifi dana rago,harma da kayan ciki,wanne kike so?
Nan take ta sake fuska ta shiga sakin lallausar murmushi" Ki kawo min ferfesun kifi,ki hado da lemu mai sanyi "
"An gama ranki ya daɗe"
Ba jimawa kuwa sai ga matar dauke da abinci a babban tire ta kawo mata komai kamar yanda ta faɗa,"Madam kudin abincin zaki bada yanzun ne ko a saka a lis dinku?
To ita ina taga kuɗi,"A saka a list in yazo zai bada "
"Yes mah" Matar ta fada tana barin dakin dan bata damar cin abincin ta.
Kyara zama tayi da kyau bayan ta sauko kasa a haucin abincin ta hankali kwance,sai da ta cinye sakwaran tas da miya harda lashe kwano,farfeson kifin ne dai duk yanda ta so ta cinye ta kasa saboda irin ƙoshin da tayi,
Ko mikewa ba tayi ba,ta ji an buɗe kofa an shigo,
Kallon_kallo aka shiga yi tsakanin ta dashi,yana kuma kallon plate din dake jere a gabanta,ya kalli list din da aka bashi na kusan dubu takwas,shi tunda garin Allah ya waye bai zauna ya kashe ma kanshi dubu biyu ba,amma ita gashi zama daya taci dubu takwas,to wallahi ba dashi ba,dole ya fanshe kuɗin shi yau a jikinta,kuma yanzun a yanzun nan babu ɗaga ƙafa ko kaɗan,
A hankali yake takowa yana nufo in da take zaune,yayin da yake raya abubuwa da yawa a kanta.......
*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*32*
*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*
Tsayawa yayi a gabanta,"kin kammala?ya tambaye ta hankali kwance,domin ya riga ya shirya ma abinda zai mata,
Ita ma kallon kwanukan tayi sannan ta kalle shi"umm "
"Yayi kyau,yanzun me zaki yi?
Wannan karon hararanshi tayi" Me kuwa zan yi,kamai da ni gida"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da tsugunnawa a gabanta "me yasa baki ci abincin da nasa aka kawo maki ba?
" Saboda banga abincin a wurin ba sai ɗanyen ƙwai "
"Amma dai kinsan cin irin wannan abincin mai nauyi da safe yana saka lalaci,dan yanzun na tabbata idan aka barki zaki iya niman wuri ki kwanta,wanda haka na iya buɗe ki cikin ƙanƙanin lokacin ki zama uwar mata,ni gaskiya bani ra'ayin mace me ƙiba,shi yasa ma na tsara maki times table na abincin da zaki dinga ci kar azo ki fi haka a kiraki da uwata,"
"Me kake nufi?
" Tashi muje mutsa jiki"
Kauda kai tayi "ba in da zanje"
Mikewa tsaye yayi yana dariyar mugunta,tare da cire rigar jikinshi yana ƙoƙarin kwance belet din wandon shi,
Zaro ido tayi"me zaka yi"
"Abinda kike tunani"
Mikewa tsaye take ƙoƙarin yi
"Duk in da zaki shiga a dakin nan ba in da ba zan iya shiga ba,Gara ma karki wahalar da kanki"
Har tana in_in_na "kaga tsaya,in dai Exercise ne muje wallahi a shirye nake basai ka cire kaya ba"
Murmushin gefen fuska ya sake "A'a ni nafi son karki je,kin ga sai muyi na kan gado dama gashi kin koshi wallahi Sumi tuni zansa kiji wata yunwar"yana ci gaba da ƙoƙarin cire balet din,
" To ba na ce zan je ba,dan Allah ka mai da kayan ka,"
Maida rigar shi yayi,da akwai abinda ya dawo dashi amma wallahi ya fasa,"tashi muje"
Tashi tayi ta shiga daki ta canja kaya ta saka hijabi ta fito,
Shi ya buɗe mata kofa suka fita sai cika take tana batsewa, bai dai kula taba har suka fito bakin titi,
A tunanin ta tafiya zasu yi su dan zagaya sai su dawo,amma sai gani tayi ya tare Abin hawa "Mekunkele nawa zaka kaimu"
Mai adaidaita yace"dari biyar "
Kallon shi yayi sama da katsa"dari biyu "
Mutumin bai ma bashi amsa ba ya ja adaidaitanshi ya wuce,dan ya lura wannan ɗan rainin hankali ne,ko dari uku ba zai iya zuwa ba balle wata dari biyu,
Kara tare wani yayi,shima dari huɗu yace,amma yace sai ya bar mashi dari biyu,haka shima ya tafi basu shirya ba,
Ita dai tana tsaye tana kallon shi gaba ɗaya takaici ya gama cika ta,amma ta san abinda zata mai,in dai takamarshi bai iya cire kuɗi,
Yana tare na biyar ya ce maikunkele sabon Titi,taji mutumin yace shiga muje,kafin yace nawa harta zagaya ta shige ciki ta zauna,
Kallon ta yayi"ke ai bamu shirya ba"
Kauda kai tayi ni na shirya"malam nawa?
"Hajiya bada ɗari shida"
"Angama," Kallon shi tayi"ka shigo mana"
"A'a wallahi ba da ni ba,ɗari shida fa,a ɗari huɗu banje ba sai a dari shida,kin ga fito,in dai bake zaki bashi kuɗin ba"
"Kai dai ka shigo tunda kaji na yi magana ai ni zan bashi"
Kallon tuhuma yake mata"ni fa ba zan biya ba"
"Ohh God,ɗan Allah Jauro muje"
Shiga yayi ba tare daya ce mata komai ba kamar yanda ita ma bata ce mashi komai ba duk da bata San in da zasu ɗin ba,
Nan ma tafiyace mai nisa sosai,kamar zasu bar garin Minna,harda ɗan dajuka take gani kafin taga yace ma mutumin yabi ta can,mutumin nabi sai gasu a bakin wani katafaren gidan gona babban gaske wanda ita bama ta iya ganin ƙarshen katangar shi,
Cewa yayi mutumin yayi parking a wurin,yana tsawa ta yi sauri ta fito ba tare da tace masu Komai ba ta doshi wannan Get din ta zauna a saman bancin da ta gani a wurin kafin ya gama biyan kuɗin mai Adaidaita wanda ta san sai ya dauki lokaci.
Dukkanin su da kallo suka bita har ta zauna kafin mutumin yace"malama kuɗi na "
Ɗan daga murya kaɗan tayi tana nuna mashi Jauro"ga mijina nan shi zai baka dan ni ba ni da ko sisi "
Wani ashar ya dura sai da mai Adaidaitan ya kalle shi,"ni zaki rai na ma wayau,bayan kin ce ke zaki biya?
Turo baki ta yi "to ban dashi,kawai ka bashi kudin shi mutafi,"
Kallon ta yake yama rasa ne zai ce mata,
"Mallam sallame ni in tafi"
Juyowa yayi"dan Allah ɗan uwa ka taimake ni na baka ɗari biyu mana,kaga banda kuɗi "
"Kan uba,wallahi baka isa ba,ai babu in da zanje sai ka biyani kudi na"
Jin zagin da yayi ne yasa cikin jin haushi yace"to wai ni na ce maka zanje,ina ce a gabanka ta yaudare ni tace in shigo zata biya,dan haka kaje can ta biya ka "
Kallon sama da kasa ya masa"ai kuwa baka isa ba tunda matarka ce,dole ka biya ni,"
Ji suka yi tace "Malam riƙe shi kuɗi ne dashi kar ka yarda sai ya biya ka"
"Hande min boni,Sumi Baby dama ke mumafuka ce ban sani ba?dake za'a haɗa baki a cuce ni"
Kwalo ta mashi da harshe,ai shi ya dauko ta ba da son ranta ba,ai ya shiga uku ba dai ta gane kuɗi ne bai son kashewa ba,to ya shirya (a zuciya ta nace in dai Jauro ne ke ma kishirya shiga uku)
"Wallahi ko dai ka ban kuɗi na kona maka saran kuɗi na"
"Kai yaro ni Doya ne da zaka sare ni ko kuma ni kabewa ne,dena ganina haka tsaf zan yi maganin ka"
"Ok haka ka ce ko" Mutumin ya fada yana daga kujerar gaba da suke zama,sai gashi ya ciro wata sharbebeyar Adda sabuwa fil har ɗaukar ido yake yi,yaci kwalan Jauro wanda bai lura da Addan,
A fusace ya juyo "kai dan ub...... " Ganin Adda na daukar ido ne yasabai masan sanda ya duka ba"dan girman Allah ka yi haƙuri ni dama wasa nake maka,haba dari shidan me,kaga amsa"ya faɗa yana ciro yan dubu_dubu a Aljihunshi wanda a kalla sun kai dubu biyar,
Ita kuma ganin Adda ne yasa cikin sanda ta tashi ta labe a jikin bangon tana leken su,
Fisge kudin mutumin yayi duka"ɗan rai nin wayau dama kanada kudi ka tsaya bata min lokaci,
Nan ya mai da Addan ya tada Adaidaitan shi ya bar wurin,
Kallon fuskar shi kadai da tayi yanda yake haɗa zufa yasa ba ta san sanda ta shiga sheka dariya ba har tana zaunawa a katsa,tana kuma nuna shi da hannu,