Sashe 16
Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Faace majina tayi da kyallen dake hanunta,"wata uku da suka wuce naje Asibiti likita ya tabbatar min da ina da ciyon hawan jini,ya ce ina bukatar wanda zai dinga kula dani yana taimaka min,in ba haka ba ina iya faɗuwa rabin jiki na ya shanye,
Na roƙe Alfarmar maman Sumayya akan tabarmin Baban Momy har zuwa lokacin da zanji saki,da fari ta amince har yayi wata uku a wuri na,amma shine yanzun cikin satinnan har gida tazo ta sameni da cikin mutunci kan ita ta fasa barmin baban momy,wanda kuma Yaya shi yake taimaka min da wasu abubuwa da yawa,tunda kaga Momy na makaranta,shi kuma Sanusi ƙarami ne,shi kanshi yana buƙatar kulawa,
Ɗan Allah ka taimake ni"
Duk abinda take faɗi yana jinta tare da jinjina kai,"wata uku,to ke har yanzun ba kiji sauki ba ne?
"Ko shekaran jiya munje Asibintin tare dashi an kuma auna jinin sai dai har yanzun bai sauka ba"
"To shikenan kukan ya isa haka,zan mata magana,yanzun kai ka kira min ita ma na"
"To yaya" Ya faɗa yana ciro waya a Aljihu ya kira number ta,
Mintuna goma sha sai gata ta iso,matar gidan ce ta mata iso har inda suke,
Tunda ta shiga taga yanda Yaya ya amsa mata gaisuwa tasan cewa akwai matsala,
Bata ce masu kala ba sai zama da tayi a gefe,cikin kissa maman Momyi tace"Maman Sumayya sannu da zuwa"
Bata kalle ta ba kuma bata ce mata Komai ba sai ma dauke kai data ƙara yi tana fuskantar Yaya,
Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar ta wanda har saida ɗan murmushi ya nuna a fuskarta da sun lura,domin dama addu'a take akan Allah yasa karta amsa mata gaisuwa,domin zata iya ƙara samun ƙwarin gwiwa da rashin amsawar ta,
Jinjina kai Yaya yayi,sannan ya kira sunan ta"naji bayani daga bakin Mijinki da kuma kishiyar ki,kuma na gamsu da bayanin su sosai,ɗan haka kuma ya yanke hukunci a kan abu na farko,shine Sumayya zata aure Jauro,batun girki kuma ita Maman momy zata cigaba da riƙe miji har taji sauƙi,domin ba tada mataimaki "
Kallon mamaki take mashi"amma Yaya ta ya hakan zai kasance,wata uku da bai san cin mu ba balle shanmu,sai dai idan ya zagayo ya zo yaci wanda na dafa ma yara,idan nayi magana yace yanada mara lafiya,to ni da ya'ya na fa,Yaya ta ya taka faɗi haka ɗan Allah,ni ban damu da batun auren Sumayya ba,amma ni amin adalci,"
"Bana son wata magana ki bi umurni na kawai"
Shiru tayi tana dukar da kai,wannan wani irin rashin Adalci ne,me yasa Yaya zai mata haka,bayan yasan tana jin kunyar shi,tana girmama shi,bata iya ci masa musu akan komai,"
Dago kai tayi"yaya ba komai Allah ya bata lafiya,sai dai ina rokon alfarma,ko da ba zai ba mu abinci ba,ina roƙon ka daka saka mana baki ya yafe ma Sumayya,ya kuma cire bakin da ya mata"
Kallon shi yayi"bana son shashanci,me yasa zaka ma yarka baki,wannan ba halin ƙwarai bane,domin duk abinda ya'yan mu zasuyi wata ƙila idan aka duba tarihin rayuwarmu munyi abinda yafi nasu,kuma iyayen mu basu tsine mana ba,dan haka maza idan ka maida matarka gida kaje ka samu yarka ku dai-dai ta"
"Insha Allah Yaya"
"Ku tashi na sallame ku"
Ta rigasu fita dan haka bata jira komai ba ta wuce gida,ko sallamar matan gidan bata yi ba,ta wuce,
Allah ne kaɗai ya kai ta gida lafiya,tana isa kai tsaye ɗakinta ta shige ta kwanta tana turo ƙofa,
Kuka ta fashe dashi tana kifa fuskarta acikin fulo,dan bata son ya'yanta su ji kukanta,
Ji tayi an buɗe ƙofar an shigo an maida an kulle,
da sauri ta dago kai tana share hawayenta,
A hankali ta tako ta zauna a bikin gado tana dafa ta,tashi zaune tayi daga kwancen da take tana kakaro murmushin yaƙe,"me kike buƙata,"
Rungume ta tayi a jikinta "Mama is not bad for a parent to cry in front of their children,ki yi kukan ki,bazan hana ki ba,kuma bazan yi ba,ɓalle in rage maki kwarin gwiwa rage raɗaɗin dake zuciyar ki"
Kamar jira take ta faɗa mata haka,nan kuwa ta fashe da kuka mai raɗaɗi tana ƙara rungumi Sumayya a jikin ta,
Tayi kuka sosai wanda har saida taji wani sanyi yana ratsa zuciyar ta da nasuwa,wanda bana komai bane face na sumun kafadar da tayi kuka
*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*22*
*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*
Sai da ta gaji dan kanta sannan ta dago tana goge idanunta da suka kunbura,
Cikin sanyin jiki tace"Mama dan Allah ki yi haƙuri ki yafe min,laifina nane,idan da nasan abin zai kai haka da banje gidan ta ba,dan Allah ki yafe min kar kiyi fishi dani "
Cikin shakakken muryarta wanda ya dushe da kuka tace"ba laifin ki bane Sumayya,nasan cewa dama kawai suke jira wanda zasu ci mutunci na,basu samu ba sai yanzun,amma babu komai haka Allah ya tsara min,a wasu lokutan da dama na kanji kamar na bar gidan mahaifin ku,na kama gaba na,saboda irin wulaƙancin da yake min na bayyane dana ɓoye,sai dai a duk sanda na kalle ku sai naji bazan iya tafiya na bar ku ba,saboda nina haife ku,na jure ko wani irin wahala tun daga na ɗaukar ciki har na raino,har kuka kai matakin da kuke a yau,sai dai har yanzun ban gama tarbiyantar da ku ba,akwai ƙananki ƙanana,idan na tafi wa zai kular min dasu,nasan ba a taɓa basu irin tarbiyan da nake masu kwaɗayin samu ba,wannan yana daya daga cikin dalilan dake kara sani in yi haƙuri,
A da mahaifin ku ba haka yake ba,mutumin kirki ne,wanda nake girmamashi sosai kamar yanda yake girmama ni,ya nuna min soyayya da kulawa,har ma daku,ya shayar da ni daɗi dai_dai gwargwado,wata kila shi ya manta,amma ni ban manta ba Sumayya kuma ina son shi har yanzun"
Rungume mahaifiyar ta tayi a jikin ta hawaye na zuba a idon ta"idan har ke mahaifiyar mu zaki iya sadaukar da farin cikin ki domin na mu rayuwar,mu a matsayin mu na ya'ya me zai hana mu sadaukar da namu farin cikin domin naku,Mama na Amince da auren Jauro,zan karɓe shi a matsayin miji,amma ba dan kowa ba sai dan ke mahaifiya ta"
Dago ta tayi"A'a Sumayya,ada dai nayi niyar kibi zabin mahaifinki,amma yanzun kam ban yarda ba tunda matarsa ce ashe tayi zabin ba shi ba,ba zaki aure shi ba"
Girgiza kai tayi"kar ki ce haka Mama,idan har ban amince ba komai na iya faru na sani kuma kema kin sani,bana son na kasance mai taurin kai a tsakanin ku,dan Allah ki cire komai a ranki kamar yanda nake kokarin yi yanzun,"
"Karki damu,yanzun zanje gidan matar kancila ta kai ni gidan wannan malamin,koma yaya ne ba za'ayi wannan auren ba"
Share hawayen da suka zubo mata tayi"Mama dazu fa da kanki kika ce Malamar ku tace bai da kyau zuwa wurin malami,tabbas gaskiya ta faɗa maki,ni kan na haƙura,nayi imani da ƙaddara,domin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa,idan zaka yi ruko,to ka roƙi Allah,haka kuma idan zaka ni me taimako,ka nime taimako a wurin Allah,
To Mama me yasa ba zamu nime taimako a wurin Allah ba,a gani na yafi mana zuwa wurin wasu malamai waɗanda sai mu ɓata kuɗin motar mu domin zuwa wurin su,sannan kuma su karbi kudin mu,Amma kuma shi Allah a duk inda kake,ko da kuwa a cikin kabari ne,in dai har zaka yi addu'a Allah zai karɓa maka ba tare daka biya shi ba,
Sannan yace (ka sani da za'a tare Al'umma domin su amfanar da kai da wani abu,ba zasu iya amfanar da kai komai ba sai abunda Allah ya rubutu maka, sannan yaci gaba da faɗin,Da za'a tara Al'umma domin su cutar da kai da wani abu,ba zasu iya cutar da kai da komai ba sai abunda Allah ya rubuta maka)na yarda da wannan hadisin,
Nayi imani Maman Momy bata isa ta min abinda Allah bai min ba,ki kwantar da hankalin ki,bazan so saboda ni ki sauka a kan hanyar bin Allah ba,domin idan haka ta faru bazan taɓa yafe ma kaina ba"
"Allah ya Albarkaci rayuwar ki Sumayya,idan har Allah yana karɓar addu'ar uwa a kan yarta,Ya Allah ina roƙon ka da kasa Albarka a rayuwar Ya ta,wannan auren idan har za'a yi shi da niyyar a tozarta mu ne,ya Allah ka saka albarka a cikin shi,kasa hanyar Arzikin sune,ka ba maƙiya kunya,Amin ya hayyu ya Kayyum"
_______ɓangaren Jauro kuwa,sai washegari da rana tsaka ya shiga ƙauyen,dan Allah ya gani mugun tsoro gare shi,karma yayi sammako ya haɗu dasu a hanya,ko kuma yaje da dare wani abu ya faru dashi,shi yasa ya gwammace ya tafi da rana ido na ganin ido,,
Ko da yaje ma ko awa biyu bai yi ba a cikin Rugan su ya fito,dan gaisuwa kawai da jage ya masu,sannan ya tafi gidan Malam Liman,shima yana ganin an idar da Sallar La'asar ya masu sallamah ya wuce,
Koda mai mashin din da ya fito dashi daga cikin ruga ya ajiye shi,a maimakon ya samu ɗan adaidaita ya maida shi gida sai cewa yayi mai a daidaitan ya kaishi Barikin Sale,wanda wannan Anguwarsu Sumayya,
Sam bai damu da yanda yayi butu butu da ƙura ra,saboda hanyar su ba kyau duk jar kasa tayi yawa,wanda yasa har ta suman kanshi ya canja kala zuwa ja,
Sai ya koma yanda kasan wanda aka tono daga kabari,
Sai dai shi ko a jikin shi,
Har kusa da kofar gidan ya sauka sannan ya kara so da ƙafa,Allah yasa yana zuwa ya haɗu da Aisha zata shiga gida,dan haka tare ta yayi,
"Kanwata zo in aike ki"