← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 49

Sashe 20

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiya ta fara"ai na faɗa maki ba ni da number shi,kuma in dai wannan ne zaki ce na faɗa maki,"ta faɗa suna fita tare.

Washegari sai gani suka yi ana shigowa da kaya niki_niki,ita a lokacin ma ta fito wanka ne tana so taje gidan Aunty Amina wacce tunda aka fara maganar bikin mijinta bai bari ta zo ba,
Daya daga cikin yaran Mama ta tsayar "kai waɗannan kayan kuma daga ina"

"Baban Aisha ne yace mu shigo dashi"

Shiru tayi tana kallon su har suka kammala shigowa da duka kayan,sannan ya shigo da dariya a fuskar shi,
"Yauwa ashe kuna tsakar gida" Nuna mata kayan ya yi"kinga ga kayan dakin Sumayya,sunyi kyau sosai ko,ai Maman Momy ba karamin ƙoƙari tayi ba har sai da ta cika dubu goma,zuwa yamma Sumayya ta shirya ta je ta mata godiya"

Ita Mama ta ma kasa magana sai kallon kayan da take yi,

Cikin tsananin takaici da ɓacin rai tace"Baba yanzun waɗannan kayan sune kayan daki na,sai kace na wata tsohuwar bazawara,kalli fa katifar duk jurwayen fitsarin yara,zanin gadon yayi baki kirin da dauɗa duk ya yayyage,Tukwane duk baki kirin alamun sunji jiki,duk cikin kayan nan babu na ar...."
Kuka ta fashe dashi wanda bata san sanda ya fito ba,ta juya da gudu tana shigewa daki,

Kallon Mama yayi baki buɗe "Amma yarinyar nan ba tada godiyar Allah,ki duba kiga duk irin kokarin da matar nan tayi amma abinda zata ce kenan,kalli wancen kulan me kyau dashi,to wallahi ki ja mata kunne,kin ga dai aure zata yi,in ba haka ba zan faɗa ma mijinta ya ringa mata dukan tsaya ko zata yi hankali, k....

Ita ma juyawa tayi ta shige ɗakinta ta bar shi nan a tsaye,

" Kai ni bansan me naye ma Allah ba daya jarabce ni da irin wannan matar da Ƴar,dole na koma Istigfari"ya ja tsaki yana barin gidan.

Ta kasa kuka ta kasa yin komai,kawai dai tayi shiru ne ta zauna wuri ɗaya ba tare da ta san tunanin me take yi ba,
Can kuma kamar wacce ta tuna wani abu,da sauri ta mike ta nufe dakin Sumayya,
Kwance take a bakin gado tana ta faman rusar kuka,a jiyar zuciya ta sake tana zama kusa da ita tare da jawo ta jikin ta"in sha Allahu wata rana sai labari,ki dai na kuka domin ba zai canja komai ba sai abinda Allah yayi,"

Cikin tsananin kuka wanda muryarta ma da kyar take fita"Mama me yasa Baba baya son mu ne,ko dai bashi bane ya haife mu?

"Subhanallah me kike faɗa ne haka Sumayya! Ba kuda wani Mahaifi da ya wuce shi,shine ya haife ku,kuma duk abinda kika ga yana yi bawai yana yi bane dan baya son ku"

Taran numfashin ta tayi"to don me yake yi? Me yasa baya ma su Momy?Baba yasan buri na tun ina kara na girma nayi karatu ta yanda zan iya taimaka maki,amma tun ina aji uku ya bar biya min kudin makaranta,ke kike biya min kudin har izuwa lokacin dana kammala NCE,a lokacin da nake ganin na kai matsayin da zan taimaka maki,a wannan lokacin shi da matar shi suka durkushe ni,suka tarwatsa burikana,
Ban taɓa sanin dalilin da yasa tun ina karama bana son Baba ba sai yau,saboda komai baya mana shi cikin adalci,"dago kai tayi daga jikinta suna fuskantar juna "Mama me yasa baki bar Baba ba kin gudu?me yasa baki koma gidan yan uwanki ba,Baba baya son mu,ɗan Allah mu gudu,ni na gaji ba zan iya ba"

Ji tayi wani irin hawaye me azaban raɗaɗi kamar Barkono ya zubo daga cikin idonta,wanda sai da ta lumshe idon na ɗan wani lokaci kafin ta dube sunyi jawur wanda shi zai tabbatar maka da irin azabtuwa da zuciyar ta keyi,da kyar ta iya buɗe bakinta wanda taji yayi mata ɗaci da nauyi "saboda mahaifinku shine rufin asiri na! Idan na bar gidan nan daku ina zanje?gidan waye zan je ya karɓe mu ni da ku?Sumayya kina ganin yanda ƴan uwa na suke,kowa na fama da kanshi,ba ni da wurin gudu,ni kai na nasan yana zaune da ni ne dan na zame masa tamkar dole,in da ace iyaye na nanan ne da hakan be faru ba,kiyi haƙuri Sumayya! Kiyi haƙuri,ba ni da yanda zan yi!ki taya ni karɓar wannan ƙaddaran dan Allah mu ci ta tare,kome kika gani kije kiyi haƙuri dashi dan Allah yata "ta faɗa tana haɗa hannayen ta wuri guda alamun roƙo.

Da sauri ta daura hannun nata saman na mahaifiyar nata," Mama!dan Allah ki dai na roƙo na,in dai ina raye sai kin bar irin wannan rayuwar,sai na zama abinda zaki yi alfahari,wata rana sai kin zauna a gidan ki na kan ki,in da babu wanda ya isa kiji tsoron shi ko kiyi tunanin wani zai iya koran ki,in da zai zame maki mafaka in Allah ya yarda"

Rungumi ta tayi tana saka mata Albarka,
Yinin ranar sun yi shine cikin rashin walwala da daɗin zuciya,

Sai da ya rage saura kwana uku biki sannan ƴan uwan Mama suka fara tuntuɓar ta akan ya maganar biki,shima sai da kanin Baban su ya saka baki shi ne fa suka zo,shima basu wani jima ba suka tafi dan ba wani aiki ko wani shagali da za'a yi,dan yace duk abinda zata yi sai dai ta tattara mutane ta su je gidan maman Momy dan ya bata komai na girki a can za'a yi taro,
Dasu Yaya Babba da Aunty Rahima suka tambayeta ta fada masu yanda suka yi dashi,cewa suka yi sukan ba wanda ya isa ya kai su gidan maman Momy bayan ga gidan Uwar yarinya,dan haka ba zasu je ba"ita ma bata da ba goyon bayan akan su je ba,kuma bata ji haushin su akan haka ba,

Washegari Alhamis wanda yayi dai-dai da gobe ɗaurin aure ne yan gidan Malam liman suka kawo kaya aƙwati dana saka lalli,sai da suka fara kaiwa gidan Maman Momy dan nan aka jwatanta masu kafin a saka ƙanin Momy ya masu jagora har kofar gidan ya juya,

An tarbe su cikin mutunci aka kuma shinfida masu tabarma a tsakar gida in da mutane ke zaune,Akwati ne guda biyu na fata,sai tirmun zani uku masu kyau dana roba biyu,Les daya shadda daya,
A ɗayan kuma ƴan kayan kwalliya ne da darduma sai Kur'ani,shi kenan,
Ba wanda ya nuna masu komai dan da zasu tafi harda dubu daya Mana ta bada aka basu,wanda ba karamin daɗi suka ji ba,

Bayan tafiyar su ne Aunty Rahima ta kalli kayan a wulakance ta sheke da dariya,"kai ke dai wallahi Wasila ba kida sa'a a rayuwa,ki duba yanda aka yi auren Amina,ko da yake har Gara na Amina akan Sumayya,ace duka ya'ya ba in da suka dace,wallahi ban iyawa da wannan kayan takaici "

"Ke wallahi suma matsiyata ne,ko da yake ke baki ga zubinsu ba daga dukkan alamu daga kauye suke,ƙila ma mai kiyo ne,kai Allah ya shirya Baban Aisha ko ina kuma yaje ya rarumo wannan mutumin oho,Allah yasa shi ba mai duka bane kamar Mijin Amina"

Haka dai sukai maganganu marasa daɗi a kan Mama da ya'yanta,sai dai ba tace masu komai ba,illa dai addu'ar da taita yi acikin zuciyar ta dan niman sassauci daga Ubangijin ta.

A washegari da safe ƙarfe goma jama'a suka shaida ɗaurin auren JAURO da Amaryar sa Sumayya, kamar yanda Allah ya halasta,

Yayin da Amarya take can kwance tana fama da a zaɓaɓɓen zazzabi dan har bata san wanda ke tsaye a kanta ba......

*To fa,yanzun Aka fara*

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*28*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

Ƙarfe huɗu na yamma Baba ya shigo da kanshi yace maza masu kai amarya su zo su tafi dan baya son tafiyar Magrib,

Aunty Rahima ce tace ma Mama tazo suyi sallamah da Sumayya,
Cewa kawai tayi su tafi da ita Allah ya bata zaman lafiya,

Tana kwance a ɗakin ta Salma da Aunty Amina suna tsaye a kanta,sun rasa yanda zasu yi da ita,domin gabaɗaya jikinta ba ƙarfi gashi yayi zafi sosai dan har kaduwar sanyi take yi,

"Wai me haka kuke yi ne a tsaye Amina,tun dazu ana jira ku fito da yarinya amma kun tsaya"

"Yaya Babba jikinta ne yayi zafi gashi tana rawar sanyi shi yasa"

Tsaki taja tana yaye lullubin da tayi"Oya tashi mu tafi"

Da kyar ta iya buɗe ido "yaya Babba ba zan iya tashi ba"

"Ke tashi bana son lalaci" Ta faɗa tana jawota ta miƙar da ita,tare da yafa mata mayafi Babba,sai dai taku biyu kawai suka yi ta yanke jiki ta faɗi,

Salati suka saka suna nufar kanta,amma ina domin tayi nisa,ruwa aka diba aka shiga yayyafa mata,amma shiru kake ji babu magana domin ko motsi bata yi ba,
Hankalin mutane ya tashi,dan haka dole aka dauke ta aka yi asibiti da ita,
Suna isa gado aka bata cikin gaggawa,kafin Aunty Babba ta kira wayar Baba,
Sai da tayi kira uku sannan ya ɗauka,"wake magana?

"Yaya Babba ce,so nake na sanar da kai muna Asibiti tare da Sumayya dan ta suma,kuma gashi har an bata gado,ka turo yaro da kudi Asibiti Mata ya kawo mana ko da dubu biyar ne"

"Me?dubu biyar?to ni nan ko ɗari biyar bana magani ɓalle wani dubu biyar,kinga Yaya Babba ki kira uwarta ko mijinta su turo kuɗin,sannan idan ta farka kar ku dawo da ita gida,akwai motoci biyu da mijin ya turo na ɗaukar Amarya, zan turo maku shi yanzun su zo," Yana gama faɗar haka ya kashe yawa.
Chapter 20 · 0% Book details