Sashe 43
Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lumshe ido tayi tana wasu hawayen na ƙara zubo mata,duk da ba karamin raɗaɗi idon ke mata ba,sai dai bai kai raɗaɗin da zuciyarta ke mata ba,
" Ada ina ƙoƙarin in ga na jure komai da komai,dan gudun bata ma Baba rai,da kuma tada ma Mama hankali,na ɗauka zan iya jurewa nayi haƙuri har nayi maganin matsalar da Addu'a,
Sai dai na kasa,na kasa Sumaiya,Dahir kashe ni kawai yake da buƙatar yi,nasan ni ba komai bace a wurin shi face abinda ya saka makudan kuɗi ya siya,a yanda yake gani,saboda irin kuɗin shi da Baba ta amsa,bai dauke ni da daraja ba,ni ban isa in hana shi duk abinda yayi ni ya ba,
Ban taba faɗa ma kowa irin niman matan da Dahir ke yi ba,amma yan uwan shi duk sun sani amma daura laifin haka suke a kai na har da uwar shi,
Har mata yake daukowa ya yawo min gida,ban isa in yi magana ba,basu taba faɗa mashi abinda yake ba kyau ba,amma sun daura laifi a kaina,
Yau kusan kwana shida kenan da Mamar shi yan uwan shi suka zuga ta wai ta dawo gidan mu da zama saboda Dahir duk abinda ya samu ni kadai da yaya na yake kashe ma,ba karamin daɗi nake ci ba kuma sai yanda nayi dashi,to yanzun ta dawo gidan mu da zama,
Shine yasa aka kyara mata ɗayan dakin shi,inda anan yake ajiye yan matan na shi,
Yau da misalin karfe goma sha ɗaya na safe na gama aikina na kwanta sai gashi ya shigo dakin wai in fito yayi bakuwa,
Kallon shi nayi na kalli yarinyar da ke da shirin banza a jikinta nace su zauna anan falo in da nake zaune suyi hiransu amma ba zan fita ba,
Zan hannun yarinyar yayi wai suzo su shiga Uwar daki na,su barni a falo,
Ba zan iya ba,ba zan iya jurewa ba,dakina na sunna,gadona na sunna,dan haka ba tare bakin kofa nace ni kuma basu isa su shigar min dakin ba,shine,shine"fashewa tayi da kuka ta faɗa jikin Sumayya "shine ya haɗa kaina da kofa ya buga,duka na ya fara yi dan kawai na hana shi aikata ɓarna a saman gadon sunnan mu,ya fini ƙarfi nisa ba kusa ba,ganin idan na zauna zai iya min rauni ne yasa da gudu na fita ina ihu na shige dakin Mamar shi,Sumaiya you can't believe if I tell you abinda ya faru a dakin Mama,"
"Na yarda da ke Aunty Amina,nasan ba zaki taɓa min karya ba,me ya faru dakin Mama"
Cikin shesshekar kuka tace"ina shiga na ɓoye a bayanta ina kuka ina faɗa mata abinda ke faruwa,sai gashi ya shigo,wai karya nake mashi,zagin iyayen shi nake rayi,sannan dan ya kawo abokiyar kasuwancin shi tazo mu gaisa shi ne yake ta zagin yarinyar na hana ta shiga daki na,
Shine Mama ta jawo ni daga bayanta ta shiga koda min Mari ita shi kuma suka shiga duka na,da kyar na iya kwace kaina na shige daki na na kulle ƙofa,har yana faɗa ma Mama dake kiran sai dai in ba zan fito ba,wai ta dai na wahalar da kanta in dai ni ce da kaina zan fito,in kuma naga dama na wuce gidan uba na kwadayayye yasan kona je gida dole zai dawo da ni,wallahi Sumaiya wannan karon Aure na da Dahir ya kare,ko da Baba zai kashe ni ba zan koma ba,bazan koma in da ba'asan daraja ta ba,ba a san mutunci na ba,na gaji ba zan iya ba kuma kashe ni suke son yi"ta faɗa tana ƙara rushewa da wani kukan mai taba zuciyar mai saurare balle uwa,
Rungume ta tayi"ba in da zaki koma,Allah ma ya gani kin masa biyayya fiye da inda zaki iya,dan haka wannan abun ya isa haka ke ma ya ce kamar kowa"
Dagowa tayi daga jikin Sumaiya tana kallon Mama dake tsaye bakin kofa tana jin su"wallahi Mama idan har Baba yace sai na koma guduwa zan yi sai dai na shiga duni.....
Da sauri Sumaiya ta rufe mata baki "ba zaki taba barin gida ba Alhalin shi shedanin daya aikata bai bar gida ba,ba zaki shiga duniya ba"
Ji sukayi Mama tace" Tabbas ko ni ba zan bari ki koma ba,koda kuwa zamu bar wannan gidan a tare"
Daga tsakar gida suka ji ance "ai kuwa sai dai ku bar gidan a tare,domin ba zata mai da ni mutumin banza ba,ta zubar min da kima,
Ina wurin aiki mijinta ya kira ni yake sanar da ni dibar Albarka da ta masu shida uwar shi,har da zagin rashin mutumci,dan haka kafin raina yakaiga baci maza zoki barmin gida ki koma gidan mijinki ki bashi haƙuri shida uwar shi"
"Wallahi ba zan koma ba,koda zaka kashe ni babu in da zan koma"
Cikin jin haushi ya doso in da take"ai kuwa ba dai a gina ba,dole ki koma kona miki dukan kawo wuƙa "
Tare bakin ƙofar Mama tayi"bancin irin wannan dukan da aka mata na jeki ki mutu,shine zaka ce zaka mata dukan kawo wuƙa,sai dai in kashe ta kake son yi,ni kuma ba zan yarda ba wannan karon dan ina ji ina kagi ba zan bari ka halaka min yata ba,tunda na lura ba kasan muhimmancin ta ba"
Na zato ba sammani sai jin saukar mari suka yi wanda ba fuskar kowa ya sauka ba face na Mama,
Duk zabura suka yi cikin tsananin mamaki da tsoro abinda basu taɓa gani ba,
"Ni zaki faɗa ma bansan darajar ta ba,darajar mace ya wuce gidan mijinta,dole sai ta koma ko kuma ta barmin gida"
"Ba dai tabar maka gida ba sai dai mubar maka gidan gaba daya"
Hannu ya daga zai kai mata wani marin suka ji karan tarwatsewar wani bokitin roba saboda bugun da ta kai masa da iccen dake hannun ta,
Ma tsowa tayi in da yake tsaye ta tsaya cikin bushewar ido da zuciya irin wanda takai makura wurin ɓaci,ta na kallon shi ido cikin ido"Saboda baka dauke dauke ta amatsayin matar ka mai kima wacce kuka sha wahalar gina rayuwarku tare ba,saboda ka maida ita da ya'yanta ba komai ba,saboda bata haifarma ɗa namiji ba,shi yasa kake mata haka,shi yasa kake kokarin salwantar mana da rayuwar mu,saboda muna ya'ya mata,kana ganin babu wanda zai iya tare mata,ni ban damu ba dan ka tsine min k zageni,sai dai ba zan bari ka kuma cutar min da uwa da yar uwa ba,wallahi tunda baka ji kunyar daga hannu a gaban mu ka Mari mahaifiyar mu ba to nima ba zan ji kunyar in buga maka wannan sandar ba,idan kuma kana ganin ba zan iya ba gaba ta nan ka kuma taɓa ta"ta faɗa cikin tsananin zafin rai,dan wannan samun wurin na Baba ya yi yawa.
Tabbas abinda ya hango a idon ta ya tabbatar zata iya aikata wa,haka kawai kuma sai ya tsince kansa da shakkun yarinyar,
Sauke hannu yayi cikin borin kunya yace"tunda haka kuka zaba ku tattara ku bar min gida na,bana bukatar ku,har abada bana son sake ganin ku,na baku daga nan zuwa ƙarfe biyar"yana gama faɗar haka ya fita yabar gidan,
Zamewa tayi nan bakin kofa tana lumshe ido,ta kasa yin hawaye,bata son tayi kuka ta ƙara ƙarya ya'yanta guiwa,bata son ta nuna masu gazawar ta,
Yarda sandan gefe tayi da sauri ta karaso inda take ta tsungunna a gabanta,ita ma Amina da dingishi ta karaso in da suke,rungume Mama suka yi gaba dayan su,yayin da Aunty Amina ta fashe da kuka"Mama ki gafarceni na ja maki,gashi ta sanadiyata Baba ta kore mu yace bai buƙatar ganin mu,ni na haƙura zan koma,zan je na faɗa ma Baba yayi haƙuri zan koma amma ya bar Mama tare dashi,ni na haƙura da rayuwar,kula a can Ajali na yake "
Dago su tayi daga jikin ta "babu inda zaki koma,ba zan yarda ina ji ina gani rayuwar ki ta salwanta ba,Bani da farin ciki daya wuce naku,na ganku cikin farin ciki da kwanciyar hankali shine buri na,ina ga lokaci yayi daya kamata ni ma nayi tawa rayuwar cikin yanci tare da ya'ya na,"
Sallamar wani yaro ne ya katse su,karasowa yayi in da suke ya mika mata wata takarda "Maman Sumaiya gashi in ji Baban Aisha wai na baki"
Karɓar takardar tayi gabanta na faduwa,amma bata nuna komai ba sai amsa da tayi ta rike a hannun ta,
Juyawa yaron yayi ya wuce,
"Mama yanzun ina zamu tafi,? Cewar Amina,
Murmushin dole ta kakaro domin ta san inda zasu je can din Asalin matsalar take,sai dai ya ta iya,ba tada in da yafi nan," Gida,gidan mu dole can zamu koma "
Jikinsu ne ya kuma yin sanyi,koda yini suka je yi a gidan da yaya suke yi su dawo saboda tsangwama,iyayen Mama duk sun rasu hannun kanin babanta ta tashi gida mai cike da yara,kowa kanshi da nashi kawai yake so,ko abinci in sunje sai ace ya kare alhalin suna kallo,gaskiya da sauran matsala a kasa kenan,amma ba yanda zasu yi,ƙaddara ce da Allah ya riga ya kawo masu,kuma dole su amsheta hannu bibbiyu,
Mike wa tsaye tayi"ina ga yanzun ya kamata naje na faɗa ma Baba abinda ke faruwa,ku kuji rani a gida zan je na dawo in ya so in ya bamu daki sai akwashi kayan akai can sai mu kyara,kafin mijinki ya dawo "ta karasa faɗa tana kallon Sumaiya.
Addu'ar a dawo lafiya su kai mata,suna masu fatan dacewa da sa'a.
Gabaki daya duk zama sukayi suja zuba tagumi kowa da irin abinda ke ci masa rai,
Yayin data bangaren Mama Allah kadai yasan halin zullumin da zuciyar ke ciki,dan ta san halin Baban ta,da kuma matanshi,sai dai wannan karon kome za'ayi sai dai ayi amma ba zata kara bari a cutar mata da ya'ya ba,sai dai shima in koran nata zai yi.......
*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*52*