← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 49

Sashe 48

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gigice ta juyo"yauwa,yauwa,Kazo,to sannu da zuwa,dama kamar kasan ina nimanka "ta faɗa cikin fitar hankali,wanda kai kanka daka ganta kasan ba'a cikin haiyacinta take ba,
" Kasan wani abu kuwa,lokacin daka nuna kana so na a wancan lokacin naji daɗi sosai,domin nasan idan na aureka duk wani yangan da Maman Sumaiya ke mana ya kare,domin duk abinda ka bata dole zaka bani,sai kuma naji dadi daka nuna baka son matarka ta sani saboda kawata ce,tare muka tashi,ni kuma na yarda,in faɗa maka lokacin da auren mu ya rage saura sati ɗaya har gida naje na same tana zage ta sosai,nace mata zan aure mijin da take takama dashi,naci mata mutunci saboda ta tayarda hankalin ta,sai dai ita ko a jikinta,duk da na tabbatar da hankalin ta ya tashi,tayi kuka sosai,sai dai taki nuna maka ta sani har sanda ka aure ni,bata taba nuna ta san kana da wata mata ba,har gida na sha binta in mata cin mutunci,amma bata kula ni,
Gabaɗaya haushi take bani,na tsani in ga farin ciki a fuskarta,ganin ta samu cikin Sumaiya har ya kai wata bakwai ni kuma ban samu ba,yasa na koma ma tsohon saurayina muna mu'amala tare,har ba samu ciki,
Saboda kana da son zuciya shi yasa naje muka maka Asiri ni da Mama ta,akan na mallake ka,kuma boka ya tabbatar min abu ne sauki ne dan kai ma bawai sonta kake sosai ba,kafi sona,kuma kanada son zuciya,shiyasa cikin sauki komai ya kamaka,
Naso ace namiji na haifa,amma sai gashi na haifi mace,
Na saka ka maida ni sabon gida ita kuma ka barta a tsoho,Alhalin gidan harda kudin ta aka cika aka siya fili aka kuma yi gini,amma bata taba kula kaba,
Dana yaye Momy sai na canja saurayi wanda bamu daɗe dashi ba,to dashi ne na samu cikin junior,na kuma haifeshi,"fashewa tayi da dariyar mugunta "kai kuma sai wani murna kake yi akan an haifa maka Namiji,Wawa kawai,harda wulakanta matar ka,ni kuma ina ta jin daɗi,
Na saka yan uwankan sun tsaneta,sannan na saka ka zaba ma yarta Amina miji mara mutunci mai dukanta,wanda duk lokacin data gudo gida gan niman taimako sai na saka kaci mata mutunci ita da uwarta ka kuma korata,wannan yasa ta tsaneka,ita kuma mara kunyar Sumaiya na haɗa ta da ɗan ƙauye wanda matsalar dangin su kaɗai ya ishe ta,itama na saka ta sane ka,bayan na je gidan boka na masu Asiri ta yanda idan mijin ta ya taɓa ta zai dinga jin zafi kamar ya ƙone,irin dai yanda nake ji,ita kuma na saka mata sha'awa ta yanda zata bi maza,
Dama boka ya faɗa min idan Asiri ya karye zai dawo kai na,
Ni na zuga Uwar mijin Amina ta tsane ta,sannan nake saka tabin bayan ɗan ta,shi yasa taimata duka ita da ɗanta,
Kai kuma daga karshe na saka ka karubutawa matarka saki day_daya har uku da hannun ka,ni kam ko yanzun na mutu na cika buri na,naji daɗi na raba ka da ita har abada"ta faɗa tana kyalkyacewa da dariya,sai kuma ta saka ihu tana fisge_fisge,kafin ta arta da gudu har ta bangaje shi ta fita gidan da gudu,
Gabaɗaya gidan yayi shiru baka jin komai sai kukan Momy dake faɗin "Mama Allah ya isa tsakanin mu dake,kin cutar da rayuwar mu" Tana faɗa tana kunjin kuka,yayin da ita kuma Aunty Abigirl tayi shiru kamar ruwa ya cita,dan duk mugun halinta bata taba tsakanin Maman Momy ta fita ba,sai gashi yau taji abinda yafi ƙarfinta,

Zamewa yayi anan bakin kofa in da ta tureshi ya faɗi,zaman yan Bori yayi yayinda gudun zuciyar shi ke ƙaruwa,
Tun daga farkon Al'amarin ya fara tariyowa a ƙwaƙwalwar shi, tabbas ya nuna zalamarshi da son zuciyar shi,shi mutum ne mai son zuciya wanda hakan ne ya jawo mai komai,gashi sanadin haka ya rabu da matar shi da yayanshi,da su ka tsane shi,
Macen kirki,wacce duk abinda zai mata bata kula shi,idan har bai dawo da ita rayuwar shi ba yayi Asara,ga ya'yan daya nuna mason duniya ashe ba nashi bane,nashi ya wulakanta rayuwar su,
Mikewa yayi da sauri zai wuce,
Cikin gigita Momy ta taso ta rike ƙafar shi "Baba! Baba! Ina zaka tafi ka barni,dan Allah ka tafi dani karka barni! Ni ba ni da wani uba daya wuce kai,kai ne Baba na,dan Allah karka tafi ka barni,bansan yanda zan yi da rayuwata ba ka taimaka min Baba"

Ji yake tamkar ya hambaran da ita ya wuce,saboda duk ta sanadiyar su da uwar su komai ya ruguje,ya tarwatsa rayuwar yayanshi,duk da yasan ba laifinta bane ita ma yanzun take sani,amma a wurin shi amsar ta ba abu mai sauƙi bane,idan kuma ya wuce tamkar ya zama mai son kai ɗin ne,dan haka ya danne zuciyar shi ya tsugunna ya dago ta"karki damu har a bada ke yata ce,ba zan taba gudu na barki ba,ki zauna tare da Aunty Abigirl,ko kuma ki bita gida zange na dawo ne,zan zo na ɗauke ki"

"Ka tabbata zaka dawo"
"Na maki Alkawari,sannan ki kira gidan Kaka ki faɗa masu halin da Maman ki ke ciki"
Tana kuka ta tashi ta koma cikin dakin ta rungume Aunty Abigirl.

Fita yayi ya hau saman mashin dinshi ya tayar,yasan wuri ɗaya zai same ta,shine a Unguwar Limawa gidan Babanta,
Dan haka kai tsaye can ya nufa,
Ko da ya isa a ƙofar gida ya samu Baba zaune,da sauran abokan shi suna hira,
Da kyar ya iya sai saita kanshi ya gaida su,
Baba ne yace"Baban Aisha ya na ganka haka kamar a rikice"kasancewar sunan babban danshi gare shi shiyasa baya kiran sunan shi,
Dukar da kai yayi cikin jin nauyi yace"Baba nazo ne wurin Maman Sumaiya,ko tana ciki? Ya karasa faɗa da tambaya,

"Ai bata gidan nan,yau kusan sati ɗaya kenan,domin kuwa tazo ta same ni akan ta kama haya a can wani unguwa zata koma ita da yara,shine fa ta tafi"

Gaban shine ya rinka faɗuwa,ba dai ta bar garin ba,to ina zata tafi,ji yake zufa na keto mai,

"Amma lafiya kake niman ta,ina ce ka rubuta mata saki sannan ka ce ka bar mata ya'yan,?

" Baba wani babban Al'amari ne ya faru,dani a yau ɗin nan,"nan ya shiga basu labarin duk abinda ya faru,yana yi yana sharan hawaye,,

Gabaɗaya wurin yayi shiru,kowa tsoron Allah na ƙaruwa a cikin zuciyar shi,wannan wani irin rashin imani ne,
Daya daga cikin tsofaffin dake zaune ne yace"tabbas idan ɓera da sata to daddawa da wuri,kai ne babban me laifi,domin tun farko idan da Ace ka tsaya ma gaskiyar ka akan wannan Al'amarin da hakan bai kasancewa,kamar yanda kowa ya sani matarka ba mai matsala bace,macen kirki mai haƙuri,na tabbatar koda ka faɗa mata niyarka akan kawar ta ba zata ki ba,idan da ka girmama matarka da waccen Arniyar bata isa ta wulakanta taba,amma gaba ɗaya ka dauki hanyar rashin gaskiya,ka ci amanar ta,ta sani amma bata nuna maka komai ba ta barka da halinka,ka ƙuntata mata ita da ya'yan ta,yanzun wa gari ya waya,sai kai,wake nadama,sai kai,idan da ace ka rike gaskiya duk abinda ita waccen zata maka dan ta shiga tsakanin ka da matar ka da yazo da sauƙi,ba ace Asiri karya bane,Asiri gaskiya ne tunda yaci Annabi,amma idan ka kiyaye Allah da dokokin sa,shima sai ya kiyaye ka,idan ya tashi saukar maka da fitina sai ya zo maka da sauƙi,shi yasa yake da kyau duk rintsi duk wuya bawa ya kasance mai tsayawa akan gaskiyar shi,ka rike gaskiya,sai ka zama abin girmamawa,idan kuma ka rike karya sai ka zama abin kwatance,Allah ya rabamu da aikin dana sani "

Dukkanin su da Amin suka amsa,

Cikin zubar da hawaye yace"Baba yanzun babu yanda za'ayi a mai da mana da auren mu?

Murmushi tsohon yayi"sai dai ka yi haƙuri Allah ya ƙadarta iya wa'adin zaman da za ku yi tare da ita kenan,amma babu wata hanyar,shi yasa babu kyau ko kaɗan irin wannan sakin a Musulunci,ka saki mace saki uku ras,to wallahi sai Allah ya jarabceku,idan kai ne ka yi da sanin ka,idan kuma ita ce ta saka kayi,Ubangiji ba zai kyale ku ba,dan awanan lokacin zaka ji wani irin sonta na taso maka na matsifa,haka idan itace,ka sani Allah shi ya halarta mana yin saki,amma kuma a duk lokacin da akayi ta,sai sama da kasa sun girgiza,mu yan Adam bamu San komai ba,har balle mu da muka kasance masu matukar sakaci ta ko wani fanni,dan haka sai dai ka yi hakuri,sai kuma in Allah yayi da rabon zaku sake zama shi ne bamu sani ba,"

Ya fahimci me yake nufi sosai tunda shi ba jahili bane amma kuma son zuciya yasa yayi aiki irin na jahilai,gashi kuma yanzun ji yake tamkar ya jawota su koma gidan su,
Share hawayen da suka ki daina tsayawa yayi"Baba ina son in je in nime tafiyarta,sannan kudin hayar da suke ciki,zan dinga biya ko dan yara na,"

Jinjina kai yayi"ba kai kaɗai ba,ni kai na zan so naje na nime yafiyarta akan abubuwan dana ta yi mata saboda ba ta da shi,ɗan uwana ya rasu ya barmin amanarta amma haka nata wulakanta ta,na gode ma Allah daya buɗe min ido tun yanzun ba sai da ƙasa ta rufe min ido na haɗu da dan uwana,na kasa bashi amsa ba,"

Duk na'am suka yi da maganar su,"Baba yanzun wani unguwa take"

Dan shiru yayi yana nazari kafin yace"kaga kuma sunan unguwar ya ɓace min,yama sunan unguwar nan na bayan Kasuwa"

"Wani kasu kenan?

" Kure market,ina nufin sabon kasuwa"

"Kodai Padukwai"daya daga cikin tsofaffin wurin ya faɗa.

" Yauwa can,anan ta faɗa min,wai gidan bai da nisa da bakin titi"

Sawa yayi aka kira mai babban ɗan shi,sai kuma shi Baba ya zama su uku suka tafi.

Da kyar da tambaya suka gane gidan,da fari sun yi tunanin ba gidan bane saboda ganin irin girman shi,sai dai suka ce bari su tambaya,
Suna sallamah kuwa sai gashi Aisha ce ta buɗe masu Get,
Ganin fuskokin waɗanda ke tsaye ne yasa ta tsaya cikin mamaki tana kallon su,kafin ta kira sunan Baban ta"Baba me kazo yi nan,ba mun bar maka gidan ka ba,ai nan gidan muna yanzun"
Chapter 48 · 0% Book details