← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 49

Sashe 4

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhajin ne ya kira sunan yaron daya tsayar da ita"Salisu"

Amsawa yayi,

"Ko jiya a unguwar ku anyi sanyi?

Gabaɗaya kwashewa da dariya sukayi,har da wasu mutanen dake zaune wurin," Ai sai dai in a unguwar su Jauro ne aka yi sanyi dan mu yanzun kan lokacin zafi muke"

"Kyale shege ya dai san Me ya ciyo har yake jin sanyi,ai ni yarinyar ma ta burge ni,gara data maka haka"

"Ai bani na gaiyace ta ba,kai kuma Salisu kar kayi abinda ke gaban ka,wallahi in ba kayi hankali ba har kai sai ƴan matan garin nan sun maka tunbur sun sace kayan jikin ka,dan haka gara ka caje ta da kyau"

Nan ma dariya suka kuma sakawa,in da Alhajin yace"a kwanannan mata na mana sata shi yasa muka kara saka CCTV a ko ina na cikin shagon nan"

Wani ne daya fito daga cikin shagon yace"Salisu ina yarinyar da nace ka tare?

"Gata nan,yanzun ma nake duba kayan ta"

Tsaki mutumin ya ja"wai ne yasa kai a rayuwarka baka yin komai cikin nasuwa ne,ni da ba ita na nuna maka ba,wata farin hijabi,shine zaka tare wannan ka bari Barauniya ta gudu,?

Da sauri ya shiga mai da mata kayanta cikin leda "ɗan Allah Madam kiyi haƙuri kuskure ne"

Fisge ledan dake hannun shi tayi "ba ni da lokacin mahaukaci irin ka"

Taku biyu tayi ta tsaya a gabansu,idon ta yayi ja,wanda har ya tara ruwan hawaye,wannan wani irin tozarci ne,a gaban mutane,ai ko bata ɗauka ba sun bata mata suna,
"In Allah ya yarda sai ƴan mata sun sace ka sannan suyi gunduwa gunduwa da kai su sai da naman ka"tana gama faɗar haka ta fita shagon tare da Addu'ar kar Allah ya ƙara haɗa ta da wannan mutumin domin ko yaushe hadurwata dashi baya tamo mata Alkhairi,.

Kallon shi sukayi yanda ya sake baki yana kallon ta,sai kuma suka kwashe da dariya,wanda Alhajin tsabar dariya har yana dukawa tare da rike ciki,

Kallon su yayi"To me na mata"

"Me yasa baka tambaye ta"

Ƙara kallon hanyar da rabi yayi "naga dai wannan karon ba da ita nayi magana ba,kodan nace yan mata take jin haushi na"

"Kama santa kenan ko Jauro"

"Eh to na dai taɓa mata tayin ko zata siya Condon a cikin Adaidaita wancan satin"

Duk zaro ido sukayi suna haɗa baki"tallan Condon,wannan budurwar?

Salisu ne ya ce"lallai Jauro baka dibo da sanyi ba,yanzun ka taba ganin in da aka ma budurwa tallan Condon ko da kuwa ƴar iska ce"

Bata fuska yayi "yo ni ba taimaka mata nace zan yi ba,kuma ai sa'a ce kuma su nake taimako"

"To wai in banda hauka ma irin naka me na sai da Condon?

" Nifa Dila ne,tunda bama da kamfanin nan Nigeria nake aiki ba,daga ƙasar Moroko ake kawomin Condon wanda da amincewar manyan kasarnar,da hukumar Lafiya na WHO,
Kuma an yi hakan ne saboda taimakon jama'a"

"Ta ya hakan ya zama taimakon jama'a"

Gyara zama yayi yana fasa ledan ruwa dake gabanshi ya zuke,"yanzun zamani ne na Family Planning da mata ke yi domin tsayar da haihuwa,wasu su saka na hannu,wasu kwayoyi na haɗiya,wasu Allurai,wanda dukkan su babu wanda bai da matsala,kaga kamar na kwaya,shi taruwa yake a mahaifa baya narkewa,karshe ya bata masu mahaifa a kai ga cirewa,Allah ya tsare,
Shi kuma Allura ko dai yasa mace ta shanza kamanni ta hanyar hurata,ko kuma ya sakar mata da jini,ko jinin yata wasa,gadai shinan,kaga wannan duk cutarwa ne,
Sai kuma wata hanya wanda ba ko wasu ma'aurata ne suke iya yin shiba,kuma shine hanya mafi sauƙi,wanda baya cutarwa,kuma Addini ya yarda dashi,malamai kuma sun tabbatar da babu matsala idan mutum yabi wannan hanyar,wanda ita ce Withdrawal Method (Pulling out) ba zaka zuba komai ba a jikin matarka,sai dai ka juye a waje,wasu kuma basu sanin sanda suke juyewa,to saboda haka aka yake da kyau amfani da Condom,ko ga ma'aurata wannan ba laifi bane,
Kaga wasu da yawa da auren su amma sai su haifi Unwanted child,ya'yan da ba'a so,wanda iyayensu basu shirya haihuwar su ba,kaji uwa na cewa ai wlh banma shirya haihuwa ba na haife shi,ko kuma iyaye su dinga jin haushin ya'ya saboda sun haifesu alokacin da basu shirya haihuwa ba,ko kuma ɗawainiya sun masu yawa,hakan sai ya ja su dinga hantaran ya'yan kamar basu suka haife su ba,
Su kuma yan mata,saboda gudun Sexual Transmitted Infection,kuma ni dila ne ba wa kananan abu ba,shi yasa na mata tallah,ashe taji haushi na"

"To wallahi kayi a hankali in ba haka ba wata rana sai mata sun maka duka,ko kuma su daddatsaka kamar yanda waccen Budurwar taka ta faɗa" Alhajin ya karasa fada yana kwashewa da dariya.

Tsaki yaja "ni kam na wuce dan yau Ruga nake son na kwana"

Ajiyar zuciya ta sake tana zamewa ta kwanta,wanda daganan barci ya kwashe ta,
Koda ta farka har ƙarfe goma sha ɗaya na safe tayi,dan haka kuskure baki tayi tare wanke fuska,ta fito ɗan daura girkin rana,
Kallon tsakar gidan nasu tayi yanda yayi shiru,"Aisha ina Mama"ta tambaye yarinyar dake zaune kofar daki tana wasa da kwankwalati,

"Mama ta fita,tace idan kin tashi nace ki daura girki sannan ta tafi gidan Matar Kansila"

Shiru tayi tana tunani,kenan Mama ta tafi,Allah dai yasa naji kyakkyawar labari...

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*6*

Yana barin ƙofar din su bakin titi ya nufa,dama ranar a cikin gari ya kwana shi yasa yace bari yazo ya dubata,
Yana tare abin hawa yace ya kaishi Cancaga,suna zuwa ya sauka,daga bayan shi yaji ance"Jauro ina zuwa?

Juyowa yayi,ganin wanda yayi magana ne yasa yayi murmushi,cikin harshen Fulatanci yace mashi"gida zani"

"Oh bamu gaisa ba,barka da safiya ka tashi lafiya"

Yana hawa mashin dinshi yace "lafiya klau ya iyalan naka"

A lokacin ya tada mashin din yana amsawa,a haka suke tafiya suna dan taɓa hira kasancewar Musa kanin abokin shi ne,da Cancaga da rugarsu bai da nisa sosai dan ana iya shigar da kai a naira Dari da ishiri,a yanzun ma kenan da mai yayi tsada,
Sun yi tafi wanda aƙalla bai wuce tafiyar mintina goma ba su karasa cikin rigar ya kalle Musa yana dafashi a kafaɗa "Musa" Ya kira sunan shi.

"Na'am Jauro"

"Ina ga ka maida ni kawai Cancaga ko kuma ka sauke ni na koma da ƙafa"

Ɗan juyowa yayi "lafiya kuwa bayan mun kusa karasawa"

"Lafiya glau,kawai dai nayi mantuwa ne,a kwai maganin dana siyo ma dabbobi kuma na manta dashi"

"To ka bari kaje ka huta mana ko zuwa anjima sai ka koma ka ɗauko"

"Na Baffa Bube ne"

Da sauri yace"A'a to bari na mai da kai kuwa"nan take ya juya akalar mashin ɗin,ya mai da shi in da ya dauko shi,sallamah suka yi ya kuma hawa wani Adaidaita ya dawo dashi cikin gari inda yake zaune yake haya,
Harya ɗauki ledan maganin shanayen sai ga kira ya shigo mashi a kan ana niman shi a wurin aiki da sauri,
Ba yanda ya iya dole ya mai da maganin ya ajiye ya tafi wurin aiki da zummar in ya dawo komai dare a ruga zai kwana saboda ya kai ma Baffa Bube maganin shanayen shi kamin ya tsine mashi.

A ranar bashi ya dawo ba sai ƙarfe takwas na dare,yana shigowa wanka yayi,yana fitowa ya dauki wayarshi dake ƙara tun yana bayi,ganin me kira ne yasa ya ɗauka da sauri,kafin yayi sallamah yaji yace"Jauro kana ina"

"Ina gida,lafiya na jika haka?

" Wani gida?

"Cikin gari"

"Kana jina"

"Eh,amma lafiya Adamu?

" Ba lafiya ba,duk inda kake karka kuskura ka shigo Ruga,domin dazu da ko Sallar Isha'i ba'a idar ba,aka shiga gidansu Baffa Sanda shida matarshi aka dauke su,sun kuma harbi Yaya Audu yanzun haka ana shirin kawoshi Asibiti dan haka kar kazo"

Gabaɗaya duk ya ruɗe "me kake nufi da an ɗauke su,su waye suka ɗauke su?

" Kidnapping dinsu aka yi,dan haka sai ka kiyaye Allah ma ya taimaka baka kusa"

Shiru yayi yayin da zuciyar shi ke zafi,sai kuma yace"suwa suka aita wannan aikin"

"Baka buƙatar amsa domin ka sani,kuma kasan abinda ya faru da Jabbi kwanaki uku da suka wuce,tayu tasu hanyar daukar fansan kenan"

Dafe kai yayi "ya Allahu,shi kenan na gode Audu,insha Allah zan kiyaye"

"Yauwa sai kaji ni kuma"nan suka sauke wayar,

Komawa yayi kan gado ragaf ya faɗi,yana lumshe ido,
A gaskiya ƙaddarar shi mai ƙarfi ce tunda Allah ya ƙaddara haihuwar shi a cikin Ahalin JAURO waɗanda suka kasance wasu irin hallittu da Ubangiji ne kawai yasan manufarsa na Halittar,
Su ba dabbobi ba ne amma kuma zuciyar su bana mutane ba ne,
Idan aka ce Ahalin JAURO indai ana maganar Dukiya na Dabbobi to Allah ya basu wannan Arzikin,
Baƙin ciki,harsada,da kyashi,wanda har yakai matakin da zasu iya hallaka junansu,
Ya taso acikin wata iri yar rayuwa mai cike da kalubale,tsana,tsangwama,rashin madafa,da kuma rugujewar buri,ya zamo ɗan marayan Dawisu a cikin mugun dawa,wanda yake ɗauke da mugayen namomin daji masu matukar hatsari da yunwa,wanda a ko wani lokaci suna iya kawo ma wannan Marayar Dawisu farmaki,ko nace sun sha kawo mashi Farkami inda Ubangiji ne kawai yake kareshi da kariyar sa,ya kuma saka shi acikin mutane masu tsayin rai acikin wannan dawar,yasa ya kasance a cikin zababbu bayan doguwar gwogarmaya.
Chapter 4 · 0% Book details