← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 49

Sashe 11

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai yayi duk da a lokacin ya fahimce wasu daga cikin abinda Malam liman ke faɗa wasu kuma bai fahintaba a wannan lokacin amma ya tabbatar yasa kudirinsa akan karatu.

Tun daga wannan lokacin ya cire komai a ran shi yasa ma ran shi lallai cewa shi maraya ne wanda bashi da uwa bashi da uba,ba kuma shida dangi,shi kaɗai ke son kanshi,sai dai kamar yanda Malam Liman yace mai Babu maraya sai rago,to lallai ba zai zama raggo ba,zai yi ilimi ta yanda mutane zasu so shi zasu kuma girmama shi,zai zama abinda yake son ya zama da taimakon Allah,wannan shine ƙudirin Yaro mai shekaru bakwai a wannan lokacin,

Tun daga sannan ya mai da rayuwar shi tashi shi daya,idan gari ya waye shi zai fito yayi wanke-wanken kwanukan da aka bata ya share tsakar gida duk sanyi duk iska,domin in bai tashi ba ma da bulala Inna Binta ke tada shi,idan kuma lokacin sanyi ne da ruwan randa zata tada shi,shi yasa tunkafin ma ta tashi barci yake kammala mata aikin da zai yi,baya tsayawa ya jira sai an bashi abin karin safe sannan ya tafe makaranta domin yasan ko ya tsaya ba lallai ya samu ba,ko ya samu sai kusan goma na safe,shi yasa ya gwammace ya wuce,in ya dawo ya samu to,in bai samu ba sai tafi gidan su Moha ko Malam Liman a can kam baya rasa abinda zai ci.

A hankali rayuwa ke tafiya abubuwa na sauyawa da dama, amma banda gidan su Jauro domin kamar dai yanda yake tun 1999,haka yake babu abinda ya canja a wannan gidan sai ma abinda ya karu,
Domin kuwa Inna Binta ta ƙara haihuwa,har ya'ya uku,kamar yanda ita ma Inna Kande ta ƙara har yara biyu,kuma ita ma idan lokacin kwanan Jauro yayi a shiyan ta,to da ita ma ta samu dan aiki,domin ita ba karamar kazama bace,shara wanke-wanke,har ta da wanki shi ke masu,ko da jika jika ne ita be dame ta ba,kuma a haka yake daurewa yake yin duk abinda aka saka shi,domin shi ba yaro bane mai son jiki,to ina ma yaga ta son jiki,wa zai ma son jiki.

Batun makaranta kuwa cikin ikon Allah shi ke daukar na ɗaya,domin Jauro irin yaran nan ne da ake kira gifted,in da magana ne akan Mathematic to ba'a magana domin ko malaman su suna mamakin yaron,domin yaron ga shi dai dan ƙauye amma Allah ya bashi,
Moha ya riga shi kammala primary har ma ya shiga wata government school anan wanda baida nisa da nan ɗin,yana primary five suka tafi gasa irin wanda ake kai yara,cikin ikon Allah shi yazo na daya,wanda jin daɗin hakan ne yasa wani mutum wanda ya ji an kira da suna Alhaji Abubakar Imam,shi ya ɗauki nauyin makarantar Jauro tun daga Jis one har S.S three kuma a makarantar kuɗi,domin shima ya nada nashi makarantar kuma babba ce ta masu kudi a wannan lokacin,

Wannan labarin ba karamin daɗi abin yama Malam Liman ba,Allah sarki har da hawayen shi,

Ta ɓangaren Islamiya kuma babu laifi domin har yakai izifi goma sha biyar,.
A haka rayuwa ta mike kuma tana tafiya da daɗi da kuma babu daɗi,
Shigar Jauro babban makaranta ya saka rayuwar shi sauyawa ta bangarori da dama,ya samu daukaka a cikin ɗalibai da kuma malamai,ba dan komai ba sai dan ilimin shi,sai dai.......

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*15*

*Bayan shekara goma*
A cikin waɗannan shekarun da suka wuce abubuwa da dama sun faru ko ince suna kan faruwa,domin gida ya ƙara cika da yaya,da kuma samari,

Ta bangaren halin mutanen gidan kuwa babu abinda ya canja,domin kuwa suna nan a yanda suke,sai ma abin da yaci gaba,
Domin kuwa yanzun yan gidan su Baffa Sanda basu isa suyi magana da koda yaro ƙarami bane in dai dan Baffa Bube ne,babu mutunci a tsakanin nin su kamar yanda babu ragi,

Baffa Bube dai shikam Allah yayi ya kara Aure,hmmm,sai dai ranar anga hauka tuburan a cikin gidan,
Sai dai shi mai gidan yace bata isa ta hana shi abinda yake so ba,kuma Amarya dole ta zauna,
Ganin da gaske yake ne yasa ta tattara kayanta ta bar gidan ta goma rugar su,wai tayi yaji,
Wannan yajin da taji ba ta san ba karamin dadi yama mutanen wannan gidan ba,
Ita a nata tunanin shine za'a biyo ta a bata haƙuri a kuma neme ta koma,ita kuma a lokacin zata wulakanta su,
Abinda bata sani ba shine mutane da yawa a gidan ba su fatan ta dawo,dan haka kowa yayi banza da lamarin ta,aka cigaba da shagalin biki,

Wasa_wasa sai da Amarya tayi shekara daya lokacin ta haihu tana da danyen goyo,sai gashi da rana tsaka Inna Binta ta tattaro kayanta ta dawo da kanta ba tare a anje biko ba,

Wanda har yau Inna Mari na mata gori a kan haka,ta dawo gidan miji ba tare da yaje biko ba,

Wannan dawowar da tayi,ta dawo ne da kwandunan bala'i a wannan lokacin,domin tsakar gidan Baffa Bube sai da ya kusan gagaran mutane shiga saboda kullun cikin yaƙi suke ita da Amaryar shi mai sune Hauwa,

Yanda kasan ƴan daba haka suke,domin kuwa da zaran Inna Binta ta dauko Icce,Hauwa zata dauki katon muciya,ko ita ma ta dauki Faskare,
Duk sun lalace sun zama kamar zararru,
Su kenan kullum cikin zuwa asibiti dinkin goshi,
Gaba ɗaya ta hana Hauwa zaman lafiya a gidan,

Wani faɗa da suka yi wanda shine na karshe wanda ƴan uwan Hauwa suka dauke tare da kwashe kayan ta,wai ba zasu bari haka kurin a kashe masu yar uwa ba,ai kuma suka tafi da ita har da danta,dan cewa suka yi ba zasu bar matarsa Binta ta kashe shi ba,duk bala'in Baffa Bube dole ya bari suka tafi dashi,domin gaba da gabanta ne,

Abinda ya faru kuwa shine,
Akan abinci ne faɗa ya haɗa su,wanda dama ita Binta tana jiraye da ita,dan haka kuwa ta shammaceta ta saka muciya ta shemeta da shi,ai kuwa ta suma,domin ta bugu,kamar wasa ansa ruwa amma taki farkawa,wanda sai da aka haɗa da Asibiti,kwananta biyu sannan ta farfaɗo,
Ganin ta farfado ne yasa yan uwanta suka yi hamdala,
Daga nan suka dauki zuga su shida,uku yanninta mata uku matan yanninta maza,suka tafi har Rugansu Jauro,

Kaman abin arziki suka ce sun zo daukar kayan Hauwa ne,babu wanda ya hana su tunda dama ita Inna Mari ba amfani gareta va,kuma Baffa Bube bai nan,dan shi kam yana son matar shi,

Ita kuma Binta tana ganin haka ta hau shewa da cika bakin ta kori kishiya,har da kiɗa kwarya a tsakar gida,

Hmmm,bata san dama da biyu suka zo ba,dan kuwa a ranar Binta ta yaba wa aya zakin sa,
Domin babu zato babu tsammani suka rufe ta da duka ta ko ina,yanda ta nuna ma yar uwar su rashin imani haka suka mata,
Domin sai da suka mata shegen duka sannan suka karya mata hannu daya da ƙafa ɗaya, suka bar ta nan kwance a sume,domin bata san in da kanta yake ba,
Dukan mutum shida ba wasa ba,
Makota naji ba wanda yayi ma tunanin ceton ta,
Suna gama mata wannan ɗanyen aikin suka kwashe kayan Hauwa tas suka bar gidan,
Ai kuwa wannan ciyon sai da ta shekara tana jinya kariya,domin abin bai zo mata da sauƙi ba,
Wannan kenan.
A lokacin Jauro yana shekaru goma sha bakwai a duniya,ya zama sauri sosai,domin yanzun duk abinda za'a mai dole a rage domin dai ƙarfin shi ya kawo,ta ɓangaren karatu kuwa ya sauke Kur'ani da jimawa wanda hakan ne yasa Malam liman ya saka shi hardar Kur'ani,kuma cikin nasara ya hardace,
A Boko kuwa sai dai san barka,domin kuwa a wani gasa da makarantar su da suka je a Abuja ne ya ciyo masu na daya,wanda har a gidan TV an haska gasar,
Anan Gamnati ta bashi scholarship na wani babban University a China in da zai yi karatun shekara huɗu,
Wannan ci-gaban da ya samu a cikin gidan ba wanda ya damu dashi domin gani suke kamar aikin banza kawai zai tafi yi,

Alhaji Abubakar Imam shi ne wanda ya tsaya mashi,yake kuma taimaka mashi akan batun tafiyar,domin kuwa shima babban danshi na can,a can yake karatu,tun last year,
Dama kuma dashi yake son ya haɗa su,

Acan Ruga kuwa,zaune suke a ƙofar gidan su Moha,su uku,
Yana rike da wani dan littafi ƙarami na Turanci a hannun shi,suna hira yana dubawa lokaci lokaci,
Sai su kuma da suke kallo a wayar Moha din shida yaron Malam Liman mai suna Musa,

"Wai kai yaushe zaka siya waya ne Jauro,gashi tafiyarka bai wuce saura sati ɗaya ba" Cewar Moha.

"Kyale ɗan iska ko da me yake son ya dinga kiranmu dashi oho,ba dai nufinka inka tafi shikenan sai ka dawo ba kuma,kar ka manta shekara huɗu suke ce,shekara huɗu ba kwana huɗu ba" Musa ya faɗa.

Rufe littafin dake hannun shi yayi"ni ba zan iya riƙe abin ƴan iska ba,domin duk masu riƙe waya yan iska ne,kuma basu san amfanin kuɗi ba da zasu ɓata wurin sayan wannan abun"

Zaro ido Moha yayi"ba dai mune ƴan iska ba Jauro?

"Ka rantse babu abubuwan banza a cikin wannan wayar,karka manta Malam abinda na kamaka kana kallo a cikinta shekaran jiya,in ma aure kake so ai Gara ka yi magana kawai ayi maka"

Ɗan dariya yayi yana shafa keya dan yasan bai da gaskiya,"to amma duk da haka ya kamata ka siya waya ko dan ƴan uwa"

Kallon mamaki yake mai"ƴan uwa?ƴan uwa fa kace?ni ina da wasu ƴan uwan da zan kira ne ko su kira ni,?ai in dai ma zan siya waya sai dan mutum uku,dan in ji muryar Malam liman,sai kai sai kuma Alhaji,yana nufin Alhaji Abubakar Imam,
Dan ku kawai zan iya siyan waya,to ku din ma ba zan siya ba dan ban iya amfani da ita ba,amma na dinga aron na ɗan Alhaji ina kira in ji muryar ku"
Chapter 11 · 0% Book details