Sashe 28
Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri ta girgiza kai in dai wannan ne ba abinda zai iya yi"
Mikewa tsaye tayi tana ninke darduma "to Allah na gode maka,bari na fara haɗa kayana kar nazo na manta wani"tana kammala haɗa kayan sai gashi ya ƙara shigowa fuskarshi dauke da fara'a," Fito muci abinci "
Dan bata fuska tayi"Allah yasa ba irin wannan jagwalgwalo bane?
"Ke dai fito ki gani"
Tashi tayi ta biyo bayanshi,wanda tunda ta saka ƙafarta a falon hancin ta ya shiga shako mata wani daddadan ƙanshin abinci wanda tuni ya cika falon,
Da sauri ta karasa in da yake zaune ya tankwashe kafa,ita ma ta zauna tana haɗiye miyau,gani irin kayan daɗin dake gaban shi,
Gasasshen kifi ne kato wanda yaji kayan yaji dana kanshi a jikinshi,
Sai kuma ɗayan shi kuma romon kaza ne wanda daga gani guda daya ne kai da kafa kawai aka cire,
Ta ɗayan gefen kuma lafiyayyen tuwan semolina da miyan ganye ne yaji zuku_zukun nama a ciki,sai kuma kwalayen lemu har kala biyu masu matukar sanyi,
Ba abin da take sai hadiyar miyau tana jin wani irin yunwa na taso mata,
Duk abinda take yi yana kallon ta,
"Yauwa Sumi Baby zuba yanda zai ishe kici mana,ni ma a zuba min"
Babu wani dogon nazari ko tunani ta shiga zubawa jikin ta har wani dan rawa yake ɗan Allah ya gani yunwa take ji,
Bata damu da ta tsaya zuba mashi ba ta shiga cin abincin ta hankali kwance,wanda hakan ya danso ya bashi mamaki,dan a tunanin shi yanda jikinta ke rawa zai ga tana cine hannu baka hannu ƙwarya,ma'ana kafin ta haɗiye na bakinta ta tura wani,
Sai dai ba haka ba dan a hankali take ci tana sake murmushi tana lumshe ido,
Tabe baki yayi ya dauki kofi ya tsiyaya mata lemu ya ajiye a gaban ta,
Sannan shima ya zuba nashi,
Har ya kammala ya koma ita yake jira kafin ta gama,dan yanda take ci a hankali zaka ɗauka ba zata ci sosai ba,amma sai gashi tana ninan tada abincin nan tas,dan kifin kam sai da ta cinye shi,kazar ne dai baci rabi,
Mike ƙafa tayi tana sauke numfashi "kai Allah na gode maka,Jauro ɗan Allah ka dunga siyo irin waɗannan nan,kaga kudin da ba'a ci baya Albarka,in kai ba zaka iya ci ba ni ka dinga siya min ina ci maka Allah zai baka lada,kuma dukiyar ka zai karu"
Jinjina mata kai yayi"kar ki damu ai babu damuwa,yauwa tunda kin gama tashi mu tafi"
Murmushi tayi"to bari kyara in da muka ɓata "
"A'a ki barshi kawai zasu kyara"
"To shikenan,bari na shiga na dauko kaya na"
Tana shiga ta dauko karamin ledar data saka kayanta ta fito,dan haka tare suka fito ya mika ma ma'aikata makulli sannan suka fito farfajiyar wurin in da anan suka kuma samun wata mota sabuwa a parke tana jiran su,sai dai motar in ba ta manta ba kamar ta rannan ce,
Dan haka kamar ko wani lokaci shi ya buɗe mata kofa ta shiga sannan ya kulle shima ya shiga kafin Direba ya ja motar.............
*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*36*
*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*
Kafin Direba yaja motar su bar harabar Hotel ɗin,
Kallon shi tayi ya maida hankali yana ta faman danna waya "Jauro gida zamu tafi"
Bai Dago ba ya bata amsa da "umm"
Murmushi ta sake tana mai da kanta ta jinginar jikin kujerar motar tare da sake hamma tana lumshe ido,
Tun tana buɗe ido tana kallon hanya kasancewar ta san aƙwai tazara zuwa gidan nasu har ta koma dai ta mai da tanka tana kallon hanya,ji take gabaɗaya jikinta kamar ba nata ba,ita dai gata nan,ita ba'a sandare ba ita ba'a sume ba,kamar dai wacce take cikin yana yi na semi unconsciousnes,haka take jinta,ganin komai take yi tamkar a marki.
*BAYAN AWA UKU*
A hankali take buɗe idanun ta tana lumshewa,ganin yanda hasken dakin ke kashe mata ido,kafin ta samu ta tsayar da kwayar idanun ta a kan silin ɗin dakin wanda yaji dizai da wasu irin kyal_kyali masu daukar ido,
Ta jima tana kallon silin ɗin kafin ta maida idanunta ta lumshe,tunani take yi a ina take,nan ina ne,ko dai mafarki take yi,
A hankali ta juya tana sauke ajiyar zuciya tare da ƙoƙarin mikewa tsaye,
Sai dai sam bata jin ƙarfin jikinta,hakan yasa ta koma ta zauna,dan sai lokacin ma take kare ma babban ɗakin da take ciki kallo,
Tunda take a rayuwar ta bata taba ganin haɗaɗɗen daki ba irin wannan,komai na dakin fari da Golden color ne na dakin,
Dafe kirjinta tayi domin lokaci ɗaya gabanta ya yanke ya faɗi,dan nan take zuciyar ta ya raya mata cewa ai hatsari suka yi shine ta mutu,yanzun haka ƙila tana cikin Aljanna ne,
Salati ta fara jikinta na wani irin rawa na tsananin tsoro,ƙara tashi tayi ta nufe in da labule ke kadawa a hankali,
Duk da irin faduwa da gabanta ke yi da irin gargaɗin da zuciyar ta ke bata akan karta leka ta je ta leko ma kanta gidan wuta,amma haka dai ta daure ta rakube tana dan leken windon,
Bata masan santa ta sake baki da hanci ba tana kallon yanda ƙanƙara ke saukowa daga sama,ga kuma kankara nan daskare ta ko'ina,haka kuma tana hangan wasu irin haddaun gidan sama ta ko ina ga haske ya haska garin wanda ita bata masan Safiya bane yanzun ko rana,duk bata iya banbancewa,sai kuma motoci dake wucewa wanda ko wanne ya kunna robar gaban mota irin mai share datti ne ko ruwa,to wannan ƙanƙaran dake sauka yake sharewa,
Jin wani dan kara ne yasa ta leka ta wurin,nan ma wani babban mota ta gani irin wanda ko a duniya bata taba ganin irin shi ba,motar yana kwasan kankara yana zubawa a wani wuri, irin ƙanƙaran dake kwanciya a gefen titi.
Jin karan buɗe ƙofa ne yasa da sauti ta juya,tana kallon wanda ya shigo,tare da fatan Allah yasa ba Mala'ika bane,
Ajiyar zuciya ta sauke tana nufar in da yake tsaye shima yana kallon ta,
Rike mai hannu tayi cikin tashin hankali tace "Jauro,mutuwa muka yi ne? Nan Aljanna ne?" Kuka ta fashe dashi tana fadawa jikin shi tare da zagaya hannun ta bayan shi ta rungume shi tana kwantar da kanta a kinjin shi,"I don't wanna die young,!ban sallami Mama ba,da su yaya Amina,!"kara shigewa jikinshi tayi tana cigaba da kuka,"yanzun shi kenan mun mutu kenan,? Waiyo Allah na wallahi bana son na mutu"ta faɗa tana ƙara sautin kukanta,
Shiru yayi yana sauraran ta,kenan ita a tunaninta ta mutu ne yanzun,
Murmushi ya sake yana jinjina kai kafin ya haɗe fuska kuma,
Shafa bayanta ya shiga yi"ai wannan shi ake kira mutuwa ta riga fata Sumi Baby,dan yau kwanan mu uku kenan a kabari,"
"Waiyo Mama" Ta ƙara faɗa a tsorace,
Ganin kukan nata na niman zarcewa ne yasa ya dago kanta ya haɗe bakin su wuri ɗaya,yana mata kyakkyawar sumba,
Bakinta na cikin nashi ya dauke ta ya maida ta kan gado yana hawa saman ta,
Cire bakinta tayi cikin nashi tana kauda kai,
Numfashi take saukewa da sauri da sauri, hawaye na bin idonta ita ba abinda yake mata ne a gabanta ba,abu ɗaya kawai zuciyar ta ke raya mata shi ne"I don't wanna die young?I want to go back to my family "
Juyo da kanta yayi"duk abinda na maki ki min,domin anan ba ama miji cin musu,in ba haka ba wuta kai tsaye za'a wurga ki"rungume ta yayi "bana son a gefa ki wuta"
Jinjina kai tayi tana ƙara shigewa jikin shi tana fashewa da kuka,yayin da shi kuma yake sake murmushi ta gefe cikin tsananin jin daɗin..........
Jauro ina ka kawo ƴar mutane😳

*37*

Hannun shi ya kai bayan rigarta yana ƙoƙarin jan zip din rigar kasa wayar shi ta shiga ƙara babu kakkautawa,
Ji yayi kamar ya share wayar kar ya ɗauka,sai dai ba dama saboda ringen din wayar ya shaida mashi mai kira,
Dan haka cikin jin haushi ya sauka daga kan gadon yana ɗaukar wayar shi da ya ajiye a gefen durowa ya kara a kunne,
Ta ɗayan ɓangaren aka ce"yallabai saura mintuna goma sha biyar girginmu ya tashi,dan haka ana buƙatar ku kara so kusa"
A daƙile yace"ok"yana kashe wayar tare da maida shi aljihu,
Iska ya busar ta baki yana kallon yanda take kwance tana matsar hayawen tunanin ta mutu ne,
Girgiza kai yayi yana cije leɓe,ya rasa wannan damar,amma ba komai,hakan ba wai yana nufin ya haƙura sai tayi kukan kayan shi data sadakar,
Karasa yayi inda take kwance ya dago ta"tashi mu tafi"
"Ina" Ta tambaya tana wani langabewa a jikin shi,
"England zamu,domin nan muna Santiago ne"
Baki ta buɗe"ina ne kuma haka"
Mikewa yayi da ita"mu je ki gani dan jirgin mu ya kusa tashi"
Daukar wani katon rigar sanyi yayi ya taimaka mata ta saka,sannan ta maida karamin hijabi a sama,
Kallon shi tayi"ya aka yi na zo nan?
Yana saka nashi kayan sanyin kai tsaye yace"abu na zuba maki a lemun kwalin da kika sha na saka ki karamin suma"
Cikin mamakin shi ta zaro ido"me ka saka min? Yanzun kai Jauro ko kunya baka ji ba kake faɗa min"