← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 49

Sashe 33

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ya matso inda take kwance,"ɗan Allah ki daina ta da min hankali da wannan kukan naki"

"Mugu ba zan daina ba,kuma sai Allah ya saka min"

Gabaɗaya hankalin shi a tashe yake,ya rasa yanda zai yi da ita,domin Allah ya gani bai san me yasa ba,in dai har zai taɓa ta ko ita zata taɓa shi to ji yake tamkar wuta ya taba,dan wani irin zafi ne zai ji yana ratsa jikin shi,ko inda hannun shi ya taɓa ajikin ta,
Kuma abin ya fara ne bayan barowar su Centiago,
A da ya dauka wasa ne,amma lamarin ƙara ta'azara yake,dan yaya ta taba shi ji yake kamar an daura mashi dutsen wuta a wurin,ko cika tsayawa yayi daf da ita sai ya dinga jin wani huci na zafi na buso mashi.

Ita kuma gashi cikin lokaci kankani sha'awar ta ya karu,babu abinda take so sama da ya taɓa ta,
A gaskiya besan me ya kamata yayi ba..........

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*42*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

Kamar wacce aka tsikara haka ta mike da sauri ta bar dakin,
Bin bayanta yayi da sauri sai dai kafin ya isa har ta saka ma kofar key,
Tun yana kwankwasa kofar yana Kiran sunan ta,saboda kukan ta da yake ji abakin kofa,har ya koma bubbuga kofa"Dan Allah Sumaiya ki bude min kofa, please"

Cikin shakewar murya tace"go away,I don't wanna see you"

Dafe goshin shi yayi yana jin yanda zuciyar shi ke zafi,"please Sumaiya ki taimaka ki bude min I am sorry i can help you with something"

"I don't want your help,go away"tana fada tana buga kafarta da kofar da karfi,

"Inna'lillahi wa'inna'ilaihi rajiun"ranar yanda ya ga safe haka yaga dare,domin kuka take sosai akan ciyon cikin,abinda ke bashi tsoro yana tsoron rasata,domin Allah ya gani ba karamin so yake ma Sumaiya ba,
Tashin hankalin ta tamkar nashi ne,ranar anan bakin kofar dakin ta ya kwana idanun shi biyu,
Kiran sallah Asuba ne yasa ya tashi dole sai da yayi wanka sannan ya tafi masallaci saboda yanda yake jin jikin shi babu dadi,ga stress daya kwaso a kauye ga kuma na rashin barci,duk da shi wanna ba damuwar shi bane tunda ai shi namiji ne akan ka,
Ya tsayar da zuciyar shi in dai har ya dawo masallaci bata bude kofar nan ba to wallahi sai ya karya kofar,
Dan haka koda zai tafi ma saida ya kwankwasa mata kofar kafin ya tafi,

Ya dan jima a masallaci kafin ya shigo dan sai gari ya dan fara haske saboda Azkar din da ya tsaya yi,

Ko dakin shi bai shiga ba kai tsaye kofar dakin ta yayi,sai dai yana taba kofar yaga ya bude,da sauri ya karasa tura kofar ya shiga dakin wanda yake da duhu,
Wayarshi ya ciro acikin Aljihu ya kunna wutar dakin,nan take dakin ya dau haske,

Hangota da yayi dunkule saman gado ne yasa cikin hanzari ya karasa in da take kwance,
Hawa yayi kan godon yayi yana yaye bargon data rufa dashi,yana kallon kyakkyawar fuskarta fari tas wanda a yanzun ya koma jawur ya kumbura,tamkar yanda idanun nunta yafi ko in kumburi,ta gefe guda Kuma sai zufa take amma kamar sanyi take ji,
Hannun shi har rawa yake kafin da kyar ya samu ya taba goshinta,duk da hannun shi na sauka akan fatar ta ya dauke da sauri,
Ba zan iya tantance yanayin temperature din ta ba, saboda yanayin da jikinshi ke kasancewa,dan haka ya yanke shawaran gara ya mata physical examination,ya duba lafiyar matarshi tunda duk maganar da yake mata taki kulashi,yama gode Allah data bude kofar,
Ya na gama duba Respiration ya sauka kan gadon don ba damar ya dau puse,yana shiga daki ya dauko digital thermometer ya dawo dakin,dashi yayi amfani yadau temperature din ta wanda anan ne ya fahimce irin zafin da jikinta yayi,

Bazai iya taba taba,ta yaya zai taimaka mata,ta wata hanya,

"Sumaiya, Sumaiya"shiru bata bashi amsa ba,

"I know you can hear me, please tashi muje Asibiti,"

Jan bargon ta karayi"ka kyale ni babu in da zanje,Kuma ni lafiya ta kalau"

"I know lafiyar ki kalau,Amma ni ba nida lafiya tashi ki raka ni Asibiti"

"Bazanje ba"

"Baki son in samu lafiya ne,na dinga biya maki bukatar ki"

"Bana so,bukatar ma taka bana yi, live me alone"

Kara marairaicewa yayi"nifa mijinki ne,dan Allah nace"

Kuka ta saka domin ita kadai tasan yanda take ji,gabadaya jikinta ciyo yake mata,ga maranta kamar zai fashe dan ji take tamkar an ajiye mata dutse a mara,

Ga kanta dake mata ciyo ta gefe daya,
"Ni ka kyale ni,babu in da zanje"ta fada da irin muryar dazai tabbatar maka mutum bai da lafiya"

Ajiyar zuciya ya sauke yana sauka kan gadon ya fita dakin,can babu jimawa kuma sai gashi ya dawo dauke da kofi a hannun shi,
"Tashi kisha wannan"

Kin kulashi tayi,shi gabadaya ma he is confused,ya rasa me zaiyi,

Lumshe ido yayi ya bude,dan haka dagota yayi gabadaya jikinshi ya rungume ta,yana daure fuska tare da kafa mata kofin shayin abaki,

Dago kai tayi tayi domin tayi musu,sai dai ganin yanda ya hade fuska da yanda idanun shi suka yi ja ne yasa bashi ta shiga kurban shayin a hankali tana hadiyewa da kyar,
Sai da ya tabbatar da ta sha yakai rabin kofin kafin ya jingina mata filo,yana kyara mata zama,
Yana fita kicin ya koma ya ajiye kofin kafin ya koma dakin shi ya shige bayi,
Zame jallabiyan jikinshi yayi,yana kallon yanda Hannun shi daya rungumeta dashi ya tashi,wurin yanda kasan wanda ruwan zafi ya zubar ma haka fatan wurin yayi,ga radadin azaba da yake ji,harma a kirjin shi,
Fitowa yayi ya bude jakkan aikinshi ya dauko wani oiltiment ya shafa a wurin, sannan ya maida rigarshi,
Jin wayarshi na kara ne yasa ya dauka,sai kuma ya har kofar gida ya bude,
Wata mata ce ta fito a cikin mota tare da wani matashin yaro,wanda daga dukkan alamu direba ne,
Sai da ya gaida jauro sannan ya koma cikin mota yana jiran matar,ita Kuma tabi bayan shi....
*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*43*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

Har ɗakin da take kwance ya kai ta,cikin tsananin damuwa yace"sister Hadiza dan Allah ki taimaka min ki yi mata treatment,taki yarda da ni"

Murmushi matar tayi"kar ka damu Abdul Aziz,insha Allah zata samu lafiya "ta fada tana ƙarasa shiga ɗakin,

" Na gode,"ya faɗa yana juyawa ya bar masu ɗakin, dan ya yarda da sis Hadiza in dai wurin iya creating interpersonal relationship ne da patient,yanzun zata saka ya saki mutum ya saki jikin shi da ita.

Komawa falo yayi ya zauna yana fuskantar kofar ɗakin.

Da sallamah ta shiga karasawa bakin gadon duk da tana da tabbacin a irin yanda ta kwanta ba lallai bane ta amsa mata,koda ta amsa ba lallai bane ta ji,
A hankali ta yaye bargon dake jikinta wanda ta rufa dashi,tana kiran sunan ta,
Amsawa tayi jin muryan mace tana buɗe idanu a hankali,
Ganin matar ta mata murmushi ne ta kara buɗe idanun ta,

Shafa fuskarta tayi "sannu kin ji,Allah ya baki lafiya,gashi kuma jikin naki da zafi sosai which is so bad,amma karki damu bara na taimaka maki," Ta faɗa tana taimaka mata ta jinginar da ita jikin gado,cikin sakin fuska ta nuna gadon"zan iya zama?

Da ido ta amsa mata dan ji take har ta kanta Sara mata yake,

"Yauwa na gode yar Albarka,
Ni suna na Dr Hadiza Umar,ni likitan mata ne,wurin aiki na daya da Mijinki Abdul Aziz,ya min bayanin duk abinda ke damun ki,da taimakon Allah zaki samu sauki,dan wannan ba komai bane ni ma na taɓa shiga irin wannan yanayin da kike ciki shekara uku da suka wuce "nan ta shiga yi mata hira tana haɗa Allurai,tare da kwantar mata da hankali har ta samu tai mata,sannan tace ta kwanta ta huta idan ta tashi zuwa yamma zata dawo ta duba ta,
Tun tana kallon matar sama_sama har barci ya dauke ta,
Ganin tayi barci ne yasa ta fito falon in da ta same shi zaune,

Da sauri ya taso yana tambayar ta ya jikin nata,

" Ka kwanta da hankalin ka na mata duk abinda da ya dace,sannan akwai magunguna zan aiko Sani dashi ya kawo maka,zuwa yamma zan dawo"

Godiya ya shiga mata har ta rakata bakin mota suka wuce sannan ya dawo,ya shiga dakin da take,
Tsugunnawa yayi a gabanta yana kallon yanda ta faɗa lokaci guda,
Yana son ya taɓa ta sai dai shi kan shi ya san bazai iya ba,dole idan ta tashi tana buƙatar wanda zai taimaka mata,

Tashi yayi ko canja kaya bai yi ba naga ya fito falon,wata kofa yabi a cikin falon wanda ya fitar dashi ta bayan gida in da anan naga jerin motoci guda uku masu matukar kyau,
Buɗe daya yayi ya shiga ya ta da ita,sannan yana zuwa bakin get ya fita ya buɗe get din sannan ya fita da motar,nan ma sai da ya ƙara tsayawa ta kulle,

Sai da ya fito daga cikin unguwar sannan ya fara tunanin tsayawa ta siya mata abu,
A Blue Mart ya tsaya ya siya mata ice cream dasu cake,harda shawarma,sannan ya karasa Dutsen kuran Hausa,inda anan gidan su Aunty Amina yake,
Yaro ya aika akan yamai sallamah da mijin ta,
Chapter 33 · 0% Book details