← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 49

Sashe 35

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ko da baki jin son shi,ki dage da addu'a Allah ya saka maki soyayyar mijinki,shi kuma Allah ya ƙara mashi soyayyar ki a zuciyar shi,in sha Allah komai zai yi daidai,koda ace komai ba nashi bane,idan har kin mallaki soyayyar shi duk abinda ya mallaka ko mai ƙanƙantar shi zai zama naki,na ki ƙara godewa Allah shi ba mugun mutum bane kamar Baban Samir,shi yasa Hausawa ke cewa saka auri me dukiya gara ka auri mai zuciyar yi,
An aura maki shine da manufar mai da je karamar bazawara ta yanda za'a ƙuntata zuciyar mahaifiyar mu,
Tunda baki son shi ai dole zaki kaso auren a tunanin su,dan Allah Sumayya ki basu kunya,ki zauna da mijinki lafiya,kar ki yi abinda zuciyar mahaifiyar mu zai gaza ɗauka "

Rungume Aunty Amina tayi hawaye na bin idanun ta"na maki alƙawarin zan zubar da komai,insha Allah,zan saka ku Alfahari da ni kada mama,zan kuma bi muku hakkin ku a wurin mazajen ku "

Murmushi tayi itama tana share nata hawayen "Allah ya maki Albarka ta kuma jagoranci rayuwar ki"

"Amin"

Ji suka yi ance"Mama yunwa nake ji"

Duk kallon Samir suka yi dake tsaye a bakin ƙofa "to kaje gamu nan zuwa"
Girgiza kai tayi"yaro baya jimirin yunwa"

"Kai kalli Agogo Aunty Amina har sha biyu tayi,ashe mun daɗe zaune"

"Ai lokaci ba wuya yake gudu yanzun"

"Bara to nake na daura mana ko da Cos_cos ne"

"Muje dai ki nuna min yanda zaki ake amfanin da Gas,sai na girka mana tunda ba lafiya ne dake ba"

Tare suka shiga kicin suka yi girkin wanda yaji zuku_zukun nama,
Zuba ma Jauro na shi suka yi a kula nasu kuma suka hada a babban pleta da yara,suka baje a falo suna ci suna hira,

Aunty Amina ce tace"ke tashi ki kaiwa mijinki na shi,"

Turo baki tayi "bari na gama cin nawa tukunna"

"A'a wallahi baki isa ba,tashi maza"

Tana turo baki ta mike zata nufi kicin sai gashi ya fito cikin wannan dai shigar tashi data tsana,daga dukkan Alamu sauri yake"

"Sannun ku Aunty na"

"Yauwa sannan kanina"

"Sumy Baby zan fita,ko akwai abinda kike buƙata,?

" A'a,sai dai ga abinci an gama"

"Yauwa to saka min a kwando sai ba tafi dashi,dan nayi baki ne kuma suna jira na"

Kicin ta shiga ta saka mashi a kwando har da cokula,da lemun kwali guda biyu da plate, ta kawo mashi"

"Na gode ya faɗa yana ansa"

"To sai ka dawo"

Cikin jin daɗin maganar ta yace "Thank you"

"Aunty zuwa yamma zan dawo na maida ku gida"

"To ƙanina sai ka dawo,Allah ya tsare"

Da Amin ya amsa yana barin gidan.

Can gidan gonan shi dake maikunkele ya nufa inda anan suke jiran shi,

Ba ƙaramin farin ciki ganin su yayi ba,dan rabon shi da su shakara biyu kenan tun dawowar shi karatu,
Wato masu su Haruna,waɗanda yanzun kan manyanta,shekara ishirin ba wasa ba,tun kafin rasuwar mahaifinsa Baffa Dottiya da ya basu Amanar Dabbobi shi,basu kara dawowa ba sai sheka biyu ba suka wuce da suka zo suka kawo mashi dukiyar shi da mahaifinshi ya basu amana wanda tayi Albarka sosai,fiye da tunanin shi,
Sunyi kukan mutuwar uban gidan nasu sosai suna tuno Alkhairin shi shida Uwar dakin su,mutuniyar kirki.
Da zasu tafi kuma ya masu abinda Arzikin da basu zata ba,kuma ya biya ma su biyun kujeran makka,

Nan suka mai bayanin komai,wanda shine dalilin buɗe wannan gidan gonan da yayi,ko lokacin da suka je da Sumaiya bai dai kai ta Asalin inda ake noma da kiyo bane,domin da kashin shanun shi suke amfani wurin yin takin su,
Iya karta wurin kiyon kaji,

To sai wannan lokacin da suka kawo mai ziyara,

A cikin wani kayataccen wurin hutawa dake cikin wurin wanda aka kayatashi da lambu suke zaune tare dashi suna hira bayan sun kammala cin abinci,

Haruna ne yace"nikan Jauro meke damun ka ne "

Murmushi ya kakalo"babu komai "

Kallon shi yake sosai "faɗa min gaskiya,domin ga jikinka nan naga yana hayaƙi"

Kallon kan shi yayi cikin mamaki yace"haya ki kuma"

Dafa kafadarsa yayi"muna da wankin ido,saboda dajijjikan da muke shiga,baka San me zaka haɗu dashi ba,tunda ka shigo naga jikinta na haya ki,ka faɗa mana komai zamu taimaka maka"

Ajiyar zuciya ya sauke,sannan ya shiga sanar dasu lamarin dake faruwa tsakanin shi Sumayya "sam bana iya taɓa ta duk yanda naso,dan ji nake kamar zan kome"

Shiru suja yi suna sauraran bayanin shi har ya kammala,

Sannan,Isma'il yace..........

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*44*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

"Wannan aikin sihiri ne,wanda akayi domin a raba ku,ta yanda ita aka saka mata matsananci sha'awa kai kuma aka saka maka jin zafin jikinta,ta yanda ba zaka iya taimaka mata ba,daga karshe ita kuma dole ta shiga bin maza domin sabon abinda bata samu ba daga gareka,a takaice dole zaka sake ta daga karshe,wannan shine ma'anar wannan Asirin da aka muku"

Gabaɗaya hankalin shi tashi yayi tunda yaji an sako sumaiya ta bi wasu maza,shi kuma zai sake ta,
Ji yayi wani abu mai ɗaci ya makale masa a makoshi,
Cikin tsananin kishin da shi kanshi bai san yana da shiba a kanta yace"wallahi Baffa Haruna da kuwa na kashi duk wanda yayi ƙoƙarin rabar matata,koda kuwa waye shi,na rantse maka da wanda raina da numfashina ke gare shi idan hr hakan zai faru to ba zan iya jurewa ba"

Dafa kafadarshi Baffa Isma'il yayi"ka daina ma fadar haka,domin da yarda Allah hakan ma ba zai faru ba,tunda har mun san komai ka sa a ranar komai ya zo ƙarshe,ina nufin matsalar ka,
Yanzun fada min,idan anyi aikin so kake amai da ma wanda yayi ko kuma a kyale shi? Sai dai ina mai tabbatar maka idan har aka kyale shi ko ita,to tabbatar gaba ba'asan abinda zasu yi ba,me ka gani?

Ba tare da wani dogon nazari ko tunani ba yace"a maida ma wanda yayi aikin shi"domin shi tunda yaji an ambaci Baby shi taba wasu mazan ya rasa hankalin shi,

Juyo da kanshi Baffa Isma'il yayi gare shi,dan ya lura kamar duk baya cikin natsuwar shi,"ka yarda dani? Ya tambaye shi yana kure shi da ido,

Ajiyar zuciya ya sauke,yana ƙoƙarin sai saita kan shi,"kun dauke ni tun daga randa na fado duniya,duk da banyi tsayin rayuwa da kuba,kun rike alkawarin mahaifinna baku ci amana kun manta dani ba,ko da ace ɗan da kuka haifa ne ni iya abinda zaku mai kenan,shi yasa nake nake maku kallon amintattun iyaye,na yarda daku fiye da yanda na yarda da kaina,"

Dukkanin su murmushi suke yi saboda jin daɗin kalaman shi,

Gefen Darduman da suke zaune ya damko kasar wurin a hannun shi ya mika mashi "karɓi wannan kasar ka je ka zuba a banɗaki inda ake bahaya, aciki zaka saka,idan ka yi wannan Baffan ka Haruna zai kara sa maka sauran aikin nan da kwana uku,"

Amsar kasar yayi yana kallon shi a hannun shi,sai kuma ya mike da sauri ya bar wurin,dan wallahi bayin da katan masu kiyo ke kashi nan zai je ya zuba,
Mintuna biyar ya dawo ya zauna "na kammala"

"To yanzun akwai wasu addu'o'in da za'a baka wanda zaka lazimce yin su safe da marece,mu kuma zamu din ga tayaka da namu addu'ar,domin da ita muka dogara,"

"Insha Allah"

"Nan Baffa Isma'il ya faɗa mashi yanda zai yi da kuma irin addu'o'in,wanda yace idan ya manta ya duba cikin Husnil Muslim"

"Godiya ya masu sosai kafin su cigaba da hira.

*A gida kuwa*

Zuwa ƙarfe biyar har sun kammala girkin dare,dan Sakwara da miyar taushe suka yi,Aunty Amina ce ta daka sakwaran,

Ɗaki taja Aunty Amina ta fito da katon jakkan da suka dawo dashi tafiya wanda anan ta saka nasu tsara ban,
Fito da kayan dake cikin jakkan tayi tana warewa wasu gefe,kafin ta dauko wasu dogayen riguna guda uku ta mika mata"Aunty na wannan tsarabar ki ce ta England "
Karɓar kayan tayi cikin tsananin farin ciki ta shiga buda kayan tana saka mata Albarka,
Kafin ta miko mata na yaran ta harda na Mama,wanda nata a aciki harda turare,

Kallon kayan maza dake gefen ta tayi"to ina na Baba"ta tambaya ganin tana ƙoƙarin mai da su cikin haƙƙin.

Nan take ta bata fuska "ban siyo ba"

Waro ido tayi tana kallon tsarabar data jido masu amma tace banda Baba,cikin mamaki tace"to me yasa"

"Kawai dai,kinga mu bar maganar kema in baki so bani kaya na"

Da sauri ta ƙara jawo kayan ta rungume dan ta san Sumaiya wani lokaci ba mutum ci ne da ita ba,"ba ki ji na ce haka ba,to amma maganar gaskiya kema kinsan ya kamata ki bashi wani abun"

Cikin takaici ta kalle ta"wai Aunty Amina me kika dauke ni ne? Me kika mai da ni ne?to bara na sanar dake koda kuɗi na na jan ƙasa ba zan taba ɗauka na ba Baba a matsayin kyauta ba,ke har kin manta me ya mana,kin manta halin da kike ciki,wanda Uwar mu ke ciki,ni kaina nake ciki,Allah yamin tsari,in dai har na bashi to bansan darajan mahaifiyata ba kenan "

Riƙo hannun ta tayi da sauri cikin kariyar zuciya,da kuma tsoron irin tsanar mahaifin su data hango a idanun Sumaiya,"ke kike faɗa haka ne Sumaiya,shi din fa mahaifinmu ne,y kama ki manta duk abinda ya faru a baya...
Chapter 35 · 0% Book details