← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 49

Sashe 14

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai kuma aikin safaran Condom wanda wannan contract ne daga World Health Organization (WHO) ya samu,
Sannan daga baya kuma ya fara aiki a nan general Hospital Minna,
In takai ce maku masu karatu,a shakara ɗayan da dawowar Jauro,ya nada manyan gidan kifi wanda kifi kawai ake kiyo da kaji masu zaman kansu har guda biyu anan cikin garin Minna,sai ɗaya a Abuja,
Jauro nada Babban Pharmacy wanda babu abin da ake siyarwa a ciki banda magunguna,ma'aikatan da ke aiki a wurin sunkai mutun goma da yan safe daban yan yamma daban,
Yana da daya a Kaduna.
Sai kuma mashina da yake rabawa matasa haya wanda wannan aikin ya bar ma ɗan Alhaji ne,shi dai nashi sai dai yayi order,gashi ko wani wata yana karbar Albashi mai matukar tsoka daga gwamnati,
A taikaice masu karatu jauro yana da kudin da shi kan shi bai san yanda zai yi dasu ba,
Abinda zai baka mamaki shine zaman da yake yi a nan cikin gari ba zaman aiki bane kawai domin Jauro harda noma yake yi,idan damuna ta sauka,ta can cikin unguwar ya siya wani tafkeken fili anan yake noma shida ma'aikatan da ya dauki haya,

Shi bai yarda da wani abuba wai shi rayuwar karya,inaaa ba dashi ba,ya sha wahala ya tara kuɗi sannan ya ta kashewa,gani yake asara ne,

Jauro yayi Dating ƴan mata da yawa dawowar shi,sai dai makonshi ke sa su rabu dashi,
Yana iya ɗaukar budurwa yanzun ya kai ta Restaurant cin abinci,da sun isa zai jawo mata kujera yace ta zauna bari yaje ya masu order,
Yana zuwa farko abinda zai tambaye su shine menene ya kare a wurin,ma'ana shine wani kalan abinci ne suka san ba su da shi,
Idan sun faɗa mai sai ya koma wurin budurwar yana yamutse fuska,sai yace mata ai da naso mu ci bu kaza ne amma sunce basu da shi,tashi kawai muje wani wurin,
Idan me hankali ce sai tace to ya siya masu drinks susha,idan kuma mai wayau ce sai ta bishi suje wani wuri,wanda nan ma suna zuwa ko dai ya ƙara mata haka,ko kuma yace ai sun ce Nama ya kare,ko kuma babu Kifi,dole dai karshi a bige da shan drink,
Kuma duk bala'in ki bai bari ki ga Menu balle ki zaɓa.

Shi yasa yawancin mutane suke masa kallon wanda bai san abinda yake yi ba,kuma matalauci,
Wannan shine asalin Jauro,

To masu karatu,ko yaya zata kaya tsakanin Jauro da Sumayya,
Ko zata iya cin kuɗin shi,
Ta yaya ya haɗu da mahaifinta har ya amince mashi,
Zata aure shi kuwa,
Yaya Ahalinshi,ya zasu ƙare,
Ya labarin dukiyar shi na shanaye da aka tafi dasu,shin zasu cika Alkawari su dawo mashi dasu.

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*19*

*Wannan littafin na kuɗi ne 300,ga mai buƙata ya turo ta wannan asusun Hauwa Umar, Zenith Bank, 2284905309.*

Abinda ya faru kuwa da su shine,yaran Baffa Sanda ne zasu tafi kiyo wato kannen su Yabbale,da Dotti da Nura, sai suka biyo ta gonar Baffa Bube,anan suka sami yaran shi da nasu dabbobin suna hutawa,ita kuma Binta tana ɗiban kara wanda zata je tayi girki dashi,
Kokarin biyowa ta cikin gonar suke su wuce saboda hanyan zai fi masu sauƙi akan suyi zagaye,
Ganin sun shigo masu ta cikin gona ne yasa da sauri kanin Ɗan Fodiyo wanda bai wuce shekaru goma sha ɗaya ba ya taso ya tsaya a gaban su,cikin rashin mutumci yace basu isa subi ta cikin gonarsu su wuce ba,bancin kuma ko a girma Dottiya ma ya girma yayanshi na biyu wato Ɗan Fodiyo,
Kallon yaron yayi yace masa ya matsa masu mana bai da kunya ne ai wucewa kawai zasu yi,

Cikin rashin da'a yace ko da ace Baffa Sanda ne zai zo da kanshi yace zai wuce ta cikin gonar nan ba zasu bari ya wuce ba balle su,
Wannan maganar da yaron yayi ne ya tunzura Dottiya har ya daga hannun ya mashi mari mai lafiya,
Shi kuwa jin zafin marin ne yasa ya faɗi ƙasa yana ihu,

Jin ihun ɗanta ne yasa Binta bata jira komai ba kuma bata nime bayanin komai ba ita dai kawai taga su Dottiya tsaye kan ɗan ta,dan haka sanda ta dauka lafiyayye ta zagayo ta bayan Dotti wanda ba zato ba sammani yaji saukar sanda a kanshi,
Shi kuma jin zafin hakan ne yasa cikin zafin rai ya kawo sara ta bayan shi ba tare daya san wanda ya mai wannan aikin ba,
Ita kuma da yake Allah ya kiyaye sai ta tare saran da hannun ta,wanda saran ba karamin shiga yayi ba dan har ana ganin kashin hannu,

Wannan shine musabbabin komai domin kuwa yaranta manya tasowa suka yi suka ce basu yarda ba,dole kuma sai sun daukar ma uwar su fansa,

Bayan kwana biyu da faruwan haka ne ranar Jauro ya shigo ƙauye,shine Bakari ɗan Binta na farko ya tare shi,wai yaga Alama yanzun wani tashen rashin kunya yake ma mutane tunda yaga wasu yan kuɗi suna shigo mai,dan haka yayi hankali da su,
To shi bai ma san wani rashin kunyar yake masu ba,
To kwana uku da wannan maganar ne shine ya shirya dan ya tafi ƙauye,Allah ya kiyaye shi bai isa ba ya dawo,to shine yake samun labarin kidnappen din Baffa Sanda da akayi tare da matarsa Kande,
Wanda dama kuma an daɗe da fara zargin su Ɗan Fodiyo da irin wannan harkar,

*CIGABAN LABARI*

A jiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi yana gyara kwanciyar shi,gara ya bari washegari da rana kawai ya shiga ƙauye,

______ɓangaren Sumayya kuwa,tunda ta kammala girkin rana take jiran dawowar Mama,sai dai shiru har kusan ƙarfe uku na rana sai gashi ta dawo,
Buta ta dauka ta zaga bayi,tana fitowa ta daura Alwallah ta shige daki,

Ita kuma ganin ta dawo ne yasa ta bi ta ɗaki ta samu wuri ta zauna tana jira ta idar.

Jira kawai tayi ta sallame sallah ko tasbihi bata yi ba,ta matso gabanta ta zauna tana zuba mata ido"Mama kin je?me ya ce ? Za'a fa...

Hannu ta daga mata,tana tasbihi da hannu,sai da tayi goma sannan tace"ai dai kya bari na numfasa ko"

Bata fuska tayi"dan Allah Mama ki faɗa min,wallahi hankali na ya kasa kwanciya "

Cire hijabi tayi tana mike ƙafa "banje ba"

Zaro ido tayi "Mama!

" Eh banje ba,ina fita na haɗu da malama Sadiya,Babban malamar islamiyarmu,ita na bi gida,tun dazu ina gidan ta,kuma na faɗa mata duk abinda ke faruwa,dan haka tace na faɗa maki ki zo gida ki same ta,kuma karna kuskura naje gidan wani malami,dan zan bata imani na ne,dan haka anjima sai ki shirya ki je gidan ta"

Cikin jin haushi tace"Uwar me zan mata a gida,ni ba inda zan je "

Buge mata baki Mama tayi"kina da hankali kuwa?

Kuka ta fashe da shi,"ni wallahi ba inda zan je,muguwar mata kawai,"

Ganin Mama na niman abun bugu ne yasa da sauri ta tashi ta fita dakin tana kuka,
Shi kenan ta shiga uku yanzun ina zata samu mafita,
Tunda ta shige daki take kwance tana kuka,har aka idar da sallar la'asar,sai da Mama ta shigo ta ci mata mutunci sannan ta fito tayi Alwallah tayi sallar,
Tana zaune kan Darduma tana jan carbiw wani tunani ya fado mata,dakatawa tayi da jan carbin tana nazari abinda ya fado mata a zuciya,
Dan haka cikin sauri ta Mike tsaye tare da kwabe hijabinta ta canja wani,ko kwalliya bata tsaya yi ba ta fito,
Dakin Mama ta leka wacce ke zaune tana cin abinci "Mama na tafi gidan Maman Momy"

Dagowa tayi ta kalle ta"me zaki je yi a can?

"Kawai dai zan je gaishe ta ne"

Kallon sama da ƙasa tai mata"ke ɗin ce a yau zaki je gaishe ta?

Turo baki tayi"eh"

"To ba zaki ba,dan bana son fitina,baki je bama ance kin je kinyi balle kuma kin je,ko ma ki zauna"

Bubbuga kafa ta fara kamar karamar yarinya,domin Sumayya irin yaran nan ne da Allah yayi su da fitina da kafiya "ni Mama zuwa kawai zan yi in dawo,kuma ba fitina zanje yi ba,"

Kauda kai tayi tana ci gaba da cin abincinta kamar bata san da ita ba,

Ganin Mama ta ƙyale ta ne yasa ta sadada ta fita gidan da sauri, tana tare mai mashin ta hau tace ya sauke ta ƙarshen layin su,duk da ba tafiya bane mai nisa ko da kafa zata taka,amma gudun Mama ta aika a dubata yasa ta hau mashin,

A bakin kofar wani gida mai bakin Get lafiyayyen ta sauka ta mika ma mai mashin Naira hamsin.

Maimakon ta shiga gidan sai tsayawa tayi tana karewa Get din kallo cikin mamaki kuma lokaci guda tana hararan Get ɗin gidan kamar shi ya mata laifi,
Kafin ta isa bakin kofa ta tura ta shiga,

A tsakar gida ta samu matar gidan tana wanki wacce jin an buɗe Get an shigo ne yasa ta ɗaga kai tana kallon ta cikin mamakin wacce ta gani,

Ita kuma ganin wacce ke tsakar gidan ne yasa kuma taji kamar ta koma,ta fasa yin abinda ya kawo ta,sai tsaki take ja a zuciyar ta,

Kallon yanda take wani har haɗe fuska matar tayi,lokaci guda kuma ta saki wankin da take tana murmushi wanda kai da gani kasan ba da zuciya daya take ba,ta kama hanci ta sake wani irin guda mai sauti tare da saka dariya tana riƙe haba "ah yau amarya ce a gidan nawa,lallai aure mai saka hankali"

Bata ce mata komai ba ta jawo kujeran dake gefe ta zauna,
Kamar ba zata mata magana ba tana turo baki tace"ina wuni"

Tsakar kanta ta tsaya ta ƙara rangada wani budar "Lallai yau Allah na gode maka daka nuna min ranar dani Sumayya zata gaida ni,Allah kasa ba mutuwa na kusa ba"
Chapter 14 · 0% Book details