← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 49

Sashe 18

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana daki tana jin duk abinda suke faɗa,rufe bakin ta tayi da tafin hannun ta tana ta faman kuka,wannan wani irin rayuwa ne haka,tunda Maman Momy ta shigo rayuwar su shikenan komai ya sauya masu,ba zata manta ba,haka lokacin auren Aunty Amina ya faru,ba karamin wahala tasha ba,dan ita a nata lokacin tana da saurayin da take so,amma maman Momy ta kawo mata wannan mutumin wai sai dai shi zata aura,gashi da mata har biyu ita ce ma ta uku,data ki yarda Baba har daure ta yake a ƙarfen Dish ta kwana a wurin,
Duk wahala baisa ta amince ba sai da shi saurayin ganin wahalar da take sha yayi yawa ne yasa yace ya haƙuri kawai ta aure wanda iyayenta suka zaba mata,a ranar sai da ta kwanta asibiti tasha karin ruwa yakai leda takwas,yayin da shi kuma karshe ya bar garin,
Daga karshe dai ba dan taso ba haka ta hakura ta aure shi,
Indai wurin ciyarwa ne mutumin yana da ƙoƙari,haka tufafi dan gaskiya ba laifi,sai dai kuma yana da zuciya abu kaɗan duka,shi yasa har zuwa yau Aunty Amina bata kaunar shi,duk da sunada yara biyu,gani yake kamar siyan ta yayi,ba tada inci,haka in maganar zuwa gida ne gasu a gari daya jaha daya amma sai tayi wata biyar, shida bai bari ta leka gida ba, dan ba karamin kudin shi Maman Momy da Baba suka ci ba,kuma har yanzun a haka take kullun da kalan shaidar dukan da zaka ganta dashi a jiki ko a fuska,
Wannan lamarin na damun Mama sosai,sai dai babu yanda ta iya tunda anfi ƙarfinta,Maman Momy kamar ta asirce kowa ba mai ganin laifin ta,da tayi magana sai ace zata kashe ma yarinya aure,shi yasa ta hakura kawai take binta da addu'a,
Yanzun gashi abin ya zo kanta,sam bata son ta saka ma maman su damuwa dan idan abin ya mata yawa hawan jini na iya kamata,kwanaki ba jimawa da Aunty Amina tayi yaji mijin ya mata ɗan banzan duka,shine ta gudo gida,
Shi kuma ya kira Baba ya faɗa mashi karya da gaskiya,ba tare da Baba yayi bincike ba ya hau kan maganar mutumin nan ya zauna,
Har gida yazo ya same ta da cin mutuncin akan maza ta shirya tabi mijinta ta koma,ita kuma tace ko zai kashe ta ba zata koma ba,yayi bala'i har ya gaji ya wuce ba wanda ya kula shi,
Da ya tashi sai zagaye ƴan uwan mama tare da nashi yayi yana fadin ai mama ta zugo Amina akan ta kashe aurenta ta hanata zaman gidan miji,haka yasa a wannan lokacin ƴan uwa suka juya mata baya,daga nata har na miji,babu inda take jin daɗi,
Shi yasa akan Amina ta fauwala ma Allah komai.

Zama tayi kusa da ita"Kuka kike yi Sumayya?

Share hawayen ta tayi"A'a"
Rungume ta tayi a jikin ta,nasan kin amince ne saboda kina gudun tozarcin da zai biyo baya daga gare ni,duk da kasancewar ki yarinya mai taurin kai,amma kina da tausayi na,kin damu da damuwa ta,ban so auren ki ya kasance haka ba,bana son rayuwarki ya kasance tamkar irin nawa dana ƴar uwar ki,naso koda ke din ce ki samu kwanciyar hankali,amma babu yanda na iya,kin gama min komai,ina maki fatan nasara a rayuwar ki,kamar yanda kike da ƙudurin taimaka min a rayuwar ki,Ubangiji ya taimaka maki,kar ya taɓa barin ki tabewa,Allah ya zama gatanki,kamar yanda kika so ki zama gatan mu,
Na san idan ace a yau ina da iyayen da zasu tsaya min ne da hakan ba zai faru dani ba balle ku,sai dai na taso ne ni ma a gidan da ba'asan daraja taba,
Nasan ba ni da abinda zan iya baki daga yanzun har a kaiki dakin mijin ki,haka kuma ba zan taba roƙon ƴan uwa na ba domin su taikama min,sai dai ina iya baki dama akan kiyi kuka a kafaɗa ta iya yanda kike jin zuciyar ki zata yi sanyi,"ta fada tana ƙara rungume ta,

Kuka ta fashe dashi tana kara rungume Mama,yayin da ita kuma take shafa bayanta a hankali.

___________*Gidan Maman Momy*

Baka jin tashin komai a tsakar gidan sai tashin dariya,
Zaune suke sun baje a tsakar dakin ko wacce da kwalbar kok a gabanta,su uku ne.

Daya daga cikin su ne ta sheke da dariya "shegiya Asma'u ba kida dama,wato dai ba zaki mata da sauƙi ba"

Maman Momy ce naga ta kai ma matar data yi magana duka a cinya"waya faɗa maki ana sanya a zamanin nan Blessing,ai idan kace zaka zauna sai kaga ta zama,shi yasa kika ga tunda na shigo gidan nan a tsaye nake na hanata rawar gaban hantsi,bata isa ta motsa ba,ya'yanta ma ba tada ikon da zata aurad dasu sai mijin dana zaɓar masu,dan nasan idan suka aure masu kuɗi ko gidan hutu to Uwar su ta huta,ni kuma abinda ban so kenan "

"Amma fa Asma'u zance ko Julia ba kiɗa mutunci,kamar ba tare kuka tashi da Maman Sumayya ba,yanzun da kike mata haka wa zai ce kawarki ce,ita ta musuluntar dake,ta baki kaya,kar ki manta kawarki ce sosai a wancan lokacin,amma kika mata cin amana kika aure mata miji kika hanata kwanciyar hankali,lallai kin cika butulu,na jinjinama makircin ki,dole na zo daukar darasi na musamman "

Hararanta tayi"bana son iskanci Abigil,ni har mantawa nake na ta fitowa daga jinsin kiristen,batun wancan matar kuma tamin komai ai bai taso ba tun da ban taba rukonta ba"

Ihu Blessing ta saka"Jesus,Julia kar ki manta nan har rokon Maman Sumayya pant kike da Bireziya,batun rokon abinci kuwa ba'a magana, shine yanzun tsabar samun wuri zaki faɗi haka,Jesus karya babu wuya yanzun"

Tsaki taja tana murguda baki"ay koma dai menene a da ne,yanzun kuma fa,ai dai nafi ƙarfinta,kuma sai yanda nayi da ita da ya'yanta har ma da mijinta,"

Duk kallon juna suka yi suna tabe baki,dama haka ɗan adam yake bai iya samun wuri ba,domin duk a unguwa daya suka tashi dukkan su,wanda ya ke haɗe da Arna da Musulmai,kuma a wannan lokacin suna zaman lafiya sosai,
Amma shine taci amanar kawar ta,koma dai yaya ne su babu ruwansu tunda dai in sun zo ana ɗan siya masu kok...

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*25*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

Kiran Baffa Bube ne ya ta da shi barcin da ya koma bayan sallar Asuba,dan ranar bashi aiki yana hutu,

Faɗa mashi yayi akan yana nimanshi a gida yanzun,

Dole ya tashi ya kintsa sannan ya dauki hanya,
Kwata_kwata tafiyar awa daya ne ya kaishi ƙauye,

Koda ya isa a ƙofar gidansu ya same su zazzaune harda yaran Baffa Sanda,su Yabbale,

Sallamah ya masu sannan ya samu wuri ya zauna,bayan ya ƙara jajanta masu abinda ya faru,

Baffa Bube yace Audu dan gidan Goggo Badejo ya je cikin gida ya kira Dan Fodio,tun dazu zaman jiranshi suke yi da tuni sun fara,amma ya tsaya yana ja masu rai kamar wasu ƙananun yara.

Yana fitowa zama yayi ba tare daya ce ma kowa komai ba,
Suma kuma basu kula shiba,

Baffa Bube ne ya fara magana "kai tsaye na tara ku ne domin na sanar daku mutanen da suka dauke Sanda sun kira,sun kira mun yi magana dasu sunce suna buƙatar Miliyan goma ko wanni mutum daya,wato dai shida kande,wanda kuɗi ya tashi miliyan Ishirin,
Na dai roƙe su akan su rage mana akan mu bada miliyan goma,basu yarda ba wai sai dai a basu sha-biyar ko kuma su kashe su,
To ku me kuka gani?

Gabaɗayan su shiru su kayi,kowa na jinjina yawan kuɗin,

"Ba shiru ya kamata ku yi ba,kamata yayi a san abun yi"

"Abun yi ɗaya ne,shine kawai ƴa'ƴan shi su fitar da kudi su amsoshi,in basu dashi su fitar da dabbobinsu a sai da"

"Wannan wani irin maganar banza ne haka kake faɗa Ɗan Fodiyo" Cewar Audu.

"Ai ba maganar banza na faɗa ba,idan ku kunada kudun da zaku bada to ni dai banida shi,"

"Kai wai m...

" Ya isa haka Audu,kyale shi,mu da yake uban mu ai dole duk yanda zamu yi muyi domin mu amsoshi,"cewar Yabbale

"Ban taraku dan kumin rashin hankali ba,dan haka ko wannen ku ya saurare abinda zan yanke mashi wanda zai bayar"

"Dukkan ku manya zaku bada budu dari biyar_biyar, ko wannen ku,bana son jayayya"

Mikewa tsaye yayi"haba Baffa,wani irin dubu dari biyar,ina na ganshi,ita kake son mu samu,ni dai gaskiya banida halin shi"

"Dottiya ne ya ce Baffa gaskiya sai dai ya'yan shi su sai da dabbobin su a biya,dan ni dai Bani da shi,"

"Ai dama ba nimam taimakonku muke yi ba,ko da zamu sai da rabin dabbobinmu mu zamu amso mahaifin mu" Yabbale ya faɗa cikin jin zafin abinda suke faɗi.

"Ya isa haka duk ku zauna" Baffa ya faɗa
Sai dai ko kallon shi babu wanda yayi,sai ma wucewa dasu Yabbale sukayi,

Kallon Jauro yayi wanda tunda aka fara magana bai ce komai ba,sai dai ya kalli wannan ya kalli wancan "kai ba kada abinda zaka ce ne?

" Eh ina da abin faɗa Baffa "

Maida hankalin shi yayi kanshi daga kallon su Ɗan Fodio da suka wuce suna faɗa,"ina jinka"

"Baffa yarinyar da zan aura iyayenta sun ce na turo magabatana,kuma nan da sati biyu suke son ayi bikin,to ni kuma gaskiya bansan yanda zan yi ba saboda ga batun kama su Baffa da batun amsosu da ake yi,sai dai wallahi Baffa bana son na rasa yarinyar dan ina son ta"

Ɗan karamin tsaki ya ja"ni ba wannan maganar nake ji daga bakinka ba,maganar kuɗin da muka yi yanzun nake son naji yaushe taka ba da naka,idan har ka bada naka bani da damuwa a kan batun auren ka,kaga ko Malam liman yana iya zuwa yayi komai "
Chapter 18 · 0% Book details