← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 49

Sashe 39

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A takaice ce ta amsa tana jin haka kawai wani abu na tsaya mata a makoshi,yanzun duk wannan cikakkiyar kuma hadaddiya matar Jauro ne,to a ina ya samo ta,kalle ta jajir da ita,amma idan ta tuna kalan matar su Dottiya da Yabbale sai ta ji abu ya soke ta a zuciya,gasu kazamai,ga shi haihuwa biyu kawai yanda kasan tsofaffin,
"Bikin da aka kasa jira mu dawo ayi damu,kila tunani yake ba zamu dawo ba"

"Ki yi haƙuri innan Yabbale,Allah ne ya kawo lokacin a gaggauce wanda ba wanda ya isa ya dakatar shi yasa"

"Ke kuwa abunda an ka riga an ka yi,yanzun dai Albarka kawai ya rage ki saka masu sai ki bi su addu'a" Cewar Goggo Halira.

Kamar ba zata ce komai ba sai kuma tace"Allah ya bada zaman lafiya "

Da Amin suka amsa,sannan ya ajiye mata Basket din da suka zo dashi,

Goggo Halira ce ta fara yin gaba,sai shi dake bayan ta,
Ji tayi matar tace "Allah yasa ma ka kasa rike ta tunda kaje ka dauko abunda yafi ƙarfi ka"

Duk juyowa sukayi suna kallon ta,
"Me yasa zaki ce haka Kande bayan yanzun kika gama saka Albarka" Cewar Halira da harshen fullanci wanda ita ma dashi ta yi maganar,

Shiru yayi kawai yana kallon ta ya rasa me ya tsare ma waɗannan mutanen har abada basu taba bin shi da Alkhairi,

"Ai ba karya na faɗa ba,in banda rigima ba sai ya ɗauka a kauye kamar yanda sauran yan uwan shi suka yi ba,in Allah ya yarda ya ɗaukar ma kanshi bala'in da zai halaka shi tunda karya ya saka a gaba"

"Kamar yanda kika ambaci Allah,to insha Allah ba zai taɓa ganin bala'i ba,aure na dashi kuma sai ya kasance mai Alkhairi da abin Alfahari,ƴan bakin ciki sai dai su mutu" Ta faɗa cikin harshen Fullanci wanda gabaɗayan su sai da suka jijjiga jin abinda ta faɗa,
Daga ita wacce ta faɗa har goggo Halira mamaki da kunya ce ta kamasu,har balle Kande wacce bata taɓa tsammanin yarinyar najin yare ba,sannan bata taba tunanin zata maida mata da amsa ba,
Yayin da shi kuma yake tunanin dama tana jin Fullanci bai taɓa sani ba.

Cikin kwanciyar hankali take takawa har tabar dakin riƙe da hannu Aisha,

Kallon ta goggo Halira tayi "yau dai kam kin ji kunya Kande"

Juyawa tayi tabi bayan su,ganin bata gansu bane yasa ta zagaya ta baya in da sauran ƴan uwa ke zaune,

Yana tsaye ita kuma tana zaune saman tabarma ita da Aisha kusa da Goggo Badejo,dake mashi tsiya akan bai kaimata Amarya gidan ta ba,haƙuri yake bata akan sunanan zuwa su gaida ita.

Matar Dotti ce tace"ai kuwa Jauro ta fika kyau,a ina ka samo ta"
Duk dariya suka yi,

Bakari shida Shafi'u yaran Baffa Bube ne suka iso wurin,

"Wai me yasa ku har yanzun ba za ku yi hankali ba,kun zo kun same mutane amma babu sallamah balle gaisuwa kun zo kun ma mutane tsaye a kai kamar a kwai tsaranku anan,"cewar Goggo Halira wacce isowar ta wurin kenan.

Cikin rashin kunya Shafi'u yace" Saboda an tsane mu shi yasa ba aso mu zo,to wucewa zamu yi ma,"

Duka goggo badejo ta kai mashi a baki ai kuwa cikin sa'a ta same shi da kyau "shege me bakin hali,mu zaka ma rashin kunya,to ko Uwar taka ba ta isa muna wuri ta shigo mana haka ba, shegu sun tsotse nonon tsiya,in kun ga dama karku kara zuwa nan,su kuma wadancen yannin naku ba dai sun ƙi zuwa ba,ina nan zuwa har gida na same su,sai sun nuna min wanda yake ɗaure masu gindi"

Sun san halin goggo badejo da faɗan tsiya dan haka ba tare da sunce komai ba suka bar Asibitin,

"Goggo zamu tafi Ruga dan ina son mu je har gidan Malam liman"

"Gaskiya kam ya kamata ku je,ni ma da naso na shiga ƙauye amma sai dai zuwa gode"

Mikewa tayi suka masu sallamah sannan suka fito Asibitin,
A bakin Get ya kuma tare masu abin hawa sannan ya faɗa mashi inda zasu,
Cewa mai adaidaitan yayi "ku ba da dubu daya"

Bai masan sanda ya harari mutumin ba"in da ake zuwa dari uku shine zaka ce dubu daya?

"To ai faɗa nayi in bai maka ba sai ka faɗi iya yanda zaka iya biya"

"Na maka kama da wanda zai tsaya ciniki,ko kuma kaga Alama ba tafiya zanyi ba"

"To ku bada dari biyar"

"In baka zuwa......

Kafin ya karasa har sun shige cikin Adaidaitan" Muje Malam "
Ai kuwa jan mashin din mutumin yayi yana ƙoƙari wucewa,

"Kai kai ina zaka wuce min da mata" Ya faɗa da ƙarfi,

"Malam karka tsaya"

Ganin da gaske wucewa yake yasa da gudu ya bi su ya dale cikin Adaidaitan yana sauke numfashi,
"Kai mahaukacin ina ne,tsaya_tsaya mun fasa tafiyar,guduwa zaka min da mata?
Ji yayi tace" Malam cigaba da tafiya "

Kallon ta yayi"guduwa da zai yi dake fa?

"Ni nace ya tafi"

"To why?

" Saboda naga kamar baka shirya tafiya ba"

"To kin san wurin ne?

" Ai kai kasan wurin "

"Dafe kai yayi,Oh Sumy,ni dai to dari uku zan ba shi"

"Dari biyar zaka bashi"
"A'a ba zan biya ɗari biyar ba"

Juyowa tayi tana fuskantar shi "dubu daya zaka bashi"

Zaro ido yayi"me yasa zan bashi har dubu daya?

"Saboda kanada shi"

Nuna mai Adaidaitan yayi wanda yake ta kwasan dariya,
"Sumy this is not fear"

Ajiyar zuciya ta sauke tana shafa kumatun shi"karka damu nasan kafi karfin haka"

"Amma....

" Shiiiiiii"ta faɗa tana daura ɗan yatsarta saman labban shi,

Shiru yayi ya kauda kai yana turo baki,wanda hakan ba karamin dariya ya basu ba,ai kuwa darawa suka shiga yi ita da Aisha,dan yanda kasan wani auta haka yayi.

Juyowa yayi kuma yana kallon ta kafin ya kira sunan ta"Sumy"

Juyowa tayi batare data amsa ba.

"Dama kina jin fullanci baki faɗa min ba"

"Baka tambaya ba ne"

Shiru yayi wato ramawa tayi,"ok bani labari"

"Akan me"
"Akan taya kike jin fullanci bayan nasan Baba Bahaushe ne how come"

"Wacce ta haifi Baba Fulani ne sosai,ƴar Katsina,mun zauna tare da ita har Allah ya mata rasuwa lokacin ina SIS 2 a secondary School,kuma fullanci take mana,dan haka duk muna ji"

"Wow,that is impressive,,to akwai kuma abinda ya kamata na sani ne"

"Kamar me?

" Kamar komai,dan bana son mata ta tana ɓoye min wani abu"
Gani yayi tayi shiru ta maida hankali kan labaran da ake yi a gidan rediyo,in da mai bayanin ke nasar da cigiyar masu ra'ayin koyarwa a makaranta Secondary,aka kuma fade in da Venue din yake da kuma lokacin da za'ayi gwaji dan tantancewa.

Gabaɗaya dawo da hankalin ta kanshi tayi ta riƙe hannun shi,"kace in akwai abinda ya kamata ka sani na sanar da kai saboda ni matar ka ce ko?
Jinjina kai yayi,
"Ka amince ciki harda buri na?
Nan ma jinjina mata kai yayi.

" A rayuwata bani da buri da ya wuce na samu aikin koyarwa domin na taimakama mahaifiyata,tasha wahala da ɗawainiya dani har sanda taga na samu abinda nake so,
Ni kuma gani nake ta hanyar yin aiki da kuma taimaka mata ne kaɗai zan iya saka mata da kuma nuna mata bata yi asaran kudin banza ba,
Dan Allah ka taimakamin na cika buri na "ta ƙarasa faɗa idanunta nayin raurau da hawaye,yayin da gabanda ke faduwa na tsoron abinda zai fito bakin shi.

Shiru yayi na dan wani lokaci,yayin da ke jin yanda take ƙara matse hannun shi a cikin nata,
" Ki bari in mun je gida sai muyi magana "

Lumshe ido tayi tana jin tamkar ta shiga zuciyar shi ta ji me zai ce.

Dan murmushi mai Adaidaitan yayi,domin ba karamin burge shi suka yi ba......

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*48*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

Tunda suka shiga Rugar take kalle_kalle yanda kowa ke gudanar da abinda ke gaban shi,
A da ta dauka ko ƙaramin ƙauye ne,amma ganin yanda gidaje ya cika ko'ina yasa ta gane ƙauyen na da yawa,

Abakin wani masallaci yasa suka sauka, sannan suka shiga gidan dake jikin Masallacin,
Abakin zaure ya haɗu da Moha wanda dama ya sanar dashi zuwan su,
Rungume juna suka yi suna dariya,kafin ya juyo in da take tsaye tana kallon su,

"Amaryar mu sannu da zuwa Ruga" Ya faɗa da Hausar shi wanda fullanci ya kwace,

Cikin sakin fuska ta gaida shi,
Shiya masu jagora har dakin bakin da Malam Liman ke zaune,
Ai kuwa ba karamin daɗi tsohon yaji ba,ya kuma saka masu Albarka sosai,sannan yace Jauro ya kai ta cikin gida ta gaida iyaye mata,
Saida suka gaida matan Malam Liman sannan suka shiga dakin Uwargidan Moha,wanda matan shi biyu,
Basu jima ba kuma shida Moha suka fita suka bar ta nan suna hira,dan matan ba su da matsala ga sakin fuska,
Abinci kuwa da nama duk ci irin na ta sai da tabarshi,dan ita in dai wurin ci ne ba ruwanta da baƙunta,

Daya daga cikin yaran gidan ne ya shigo wai ta fito in ji Jauro,
Matan gidan ne suka rakota har ƙofar gida sukai mata sallamah,

A ƙofar gida ta same shi tsaye shida Abokin shi,yana ganin ta ya taso,"me kika ci haka naga bakin ki da manja"

"Da gaske?

" Ummm"ya faɗa yana jinjina kai,

Hannu ta saka ta shiga goge baki,tana kallon shi "ya fita"

"Me kenan?
" Manjan "
"A ina? Ya tambaye ta,
" Amma yanzun kai kace akwai manja a baki na "
"Ni da yaushe na faɗa,ni banga komai ba a bakin ki"
Duka ta kai mai a kafaɗa,da sauri ya goce yana dariya,
Hararanshi tayi tana ƙara ma tafiyar ta sauri ta bar shi a baya yana dariya.
Chapter 39 · 0% Book details