Sashe 40
Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin tana ƙoƙarin bin hanyar da bashi bane yasa da sauri yace"malama ba nan zaki bi ba,"
Tsayawa tayi"to ni dai dan Allah kazo kai mana jagora,ni in da ma nasan gidan da ba zan ma jira ka ba"
Karasowa yayi inda take ya riƙe mata hannu,"tanan ne hanyar "ya faɗa yana bi da ita ta wata hanyar,
A hankali suke ta ratsa ta cikin gidajen Fulani da kuma gonaki,har suka iso ƙofar wani gida mai babban iccen Darbejiya,
Kallon ta yayi ya kalli zauren gidan dake gabansu,juyo da ita gaban shi tayi" Kin ga wannan gidan? Ya faɗa yana nuna mata,
"Anan nan iyaye na suka rayu,anan kuma suka mutu,anan na rayu kuma na tashi,ina girmama wannan gidan,sai dai mutanen dake rayuwa a cikin ba kamar yadda kike tunanin suke ba,ina fata duk tarbar da kika samu ba zaki yi korafi ba,kuma duk abinda kika ji zaki toshe kunnen ki"
Jikin ta ne yayi sanyi,domin tunda take dashi bata taba tambayar shi yaya iyayen shi suke ba,ko da kuwa tace ya gaida mahaifiyarsa,cikin sanyin murya tace"to ina mahaifinka?
Murmushi yayi mai ciyo,yana tuna irin mutuwar da mahifiyarsa tayi cikin jini da a zaban nakuda,da irin niman taimakon da ya rinka yi a wurin jama'ar gidan amma aka rasa wacce zata taso ta leka koda a wani hali take,har ta rasu jini ya sandare,wannan yana daya daga cikin bakin cikin da ya karasa mahaifinsa,"ya rasu bayan sati biyu da rasuwar Inna ta"
Bata masan sanda ta saki hannun Aisha ta rungume shi ba,"I am Sorry! I am sorry for not asking you about them"
Shafa bayanta yayi yana murmushi "kar wani ya fito ya ganmu"
Ƙara rungume shi tayi,"don't worry I will take care of you "
"Keda kike min rashin kunya ta yaya zaki kula da ni?
Kafin ta bashi amsa ne suka ji daga bayan su tana salati tare da tafa hannu" Hande min boni,yau me zan gani,yanzun Jauro Karuwancin naka har ya kai kazo da Mace ƙauye ka rungume ta a tsakiyar gari"
Duk juyowa suka yi suna kallon me managa,
Daga bayan shi kuma suka ji ance" meke faruwa nake jin salati"
Ƙara cewa yayi"Baffa Jauro ne yazo da ƙaruwa har gida suna rungume juya babu kunya"
Kafin tsohon yayi magana cikin bacin rai yace"Ɗan Fodio ka iya bakin ka,yanzun in banda rashin da'a da rashin sanin ciyon kai matar tawa zaka kira da ƙaruwa?
Duk sai lokacin suke kare ma yarinyar da ya kira da matar shi kallo,
Cikin kishi da bakin ciki yace"ko dai menene naka ita ai wannan karuwanci ne,ta yaya a ƙofar gidan mu,gamu da ƙananan yara zaku zo kuna wani rungume juna,in banda yan iska"
Idan ranshi yayi dubu ya baci akan kalmar daya jefe matar shi dashi,
Kallon Baffa yayi"kana jin abinda yake faɗa "
"Yo ni kan Jauro me zan ce mashi,tunda gaskiya ya faɗa,kai ma kasan abinda kuka aikata bai kamata ba" Ya fada yana shigewa cikin wani dakin.
"Kaima kasan mu anan ba haka muke ba"
"Sai ka faɗa min in da Allah ya haramta,sannan abu na karshe da zan faɗa maka shine,duk randa bakin ka ya ƙara kuskuren kiran matata da karuwa Ɗan Fodio,wallahi! Wallahi ranar sai nasa ƴan sanda sun tafi da kai,sai na saka an shigar min da ƙara Kotu ta yanda zaka faɗa min in da ta dace da wannan sunan,in ba haka ba sai ka yi gidan yari,ka daina tunanin kai ɗan uwa na ne ba zan iya aikata maka hakan ba,tsaf zan cika abinda na faɗa kuma ka kara maimaitawa ka gani"ya faɗa yana mai tabbatar mashi da maganar shi,
Tsoro ne ya kama shi,domin yasan duk abinda Jauro yace zai yi to sai ya aikata,dan haka cikin borin kunya yace "ku dai kuka sani" Ya faɗa yana rabawa ta gefen su ya wuce.
Juyowa kanta yayi yana ƙoƙarin sai_saita ɓacin ranshi "mu je ciki ki gaida Kaka ta"
Jinjina mashi kai kawai tayi,dan ita jikinta ba karamin sanyi yayi ba tun a ƙofa,kafin ma su shiga.
Taga dai shiyoyi da yawa a gidan kasancewar yanzun an samu kari harda na Surukai,
Daya daga ciki taga sun nufa,sai da yayi sallamah a ƙofar shiyan kusan sau biyar amma ba'a bashi amsa ba,dan haka suka shiga,
A zaune a tsakar gida suka iske wata mata tana wanke-wanke,kallo daya tai masu ta kauda kai tana bitar waƙar dake tashi a wayar ta mai kiran Shakidar ka baƙauye,
Suma basu ce mata komai ba ya nufe wata ƙofa,
Ɗaga labulen dakin yayi yana ƙara yin sallamah,
Wata tsohuwa ce sosai ta gani a zaune saman tabarma,sai dai duk da tsufan matar da Alama tana da dan sauran karfin ta,
Dago ido tayi ta kalle su"waye a tsaye a kofa? Ta fada da yaren Fullanci,
Ganin ya shiga ne yasa suka bishi a baya,wani tabarmar ya dauko ya shinfida suka zauna,"Jauro ne"
"Aiyo sai yau ka ga damar zuwa"
"Kin ga ni Amarya ta kawo maki ta gaida ke,"
Ita ma da harshen Fullanci ta gaida ita,tana amsawa cikin sakin fuska,
"Ya haƙuri da Ja_irin yaron nan"
Murmushi tayi kawai bata ce mata komai ba,
"Ɗauko mata fura gashi can ta sha"
Daukowa yayi ya kawo mata haɗin Kindirmo lafiyayye,
Duk da a koshe take ta san halin tsofaffi,dan haka kaɗan tasha ta mika ma Aisha,
Kwala kiran sunan Hajjo ta fara,sai da tayi kira uku wanda suka tabbatar da tana ji kafin ta shigo din babu sallamah,ta tsaya masu a kai"Gani Kaka"
"Amma ke kan anyi Tsinanniyar yarinya,bana hanaki shigomin daki babu sallamah ba,?
Cikin gungumi ta fita,sai da ta ƙara ɗaukar wani lokaci sannan ta shigo da sallamah,
Amsawa suka yi,
" Baki ga Jauro bane da matar shi"
Kallon su tayi"na gan shi,sai dai ni dama bawai na sanshi sosai bane"
Salati ta saka "amma dai kam Hajjo ba kida ɗabi'a,yanzun Jauro ne zaki ce baki sani ba,yaron da har kashi ya wanke maki,ki na matsayin ƴar goggon shi kice baki sanshi ba,ko da kika auri Ɗan Fodio shi ya maki kayan daki duk da bai gari"
Kauda kai tayi,domin dama bawai gane shi bane bata yi ba,kawai dai kishin shi take yi,dan ba Ɗan Fodio taso ba,shi taso ta aura amma ya nuna bai da ra'ayin ta,har roko tayi akan a ɗaura masu aure kafin ya dawo zata jira shi,amma kiri_kiri yace baya son ta,sannan yanzun ta ganshi da mata ƴar gayu sannan har ta nuna ta san shi ko kuma ta nuna ta ji daɗin ganin su,Allah ta mata tsari,
Katse mata tunani maganar Kaka yayi"to ina ita Uwar taku?
Tana nufin Surukarta.
"Ta fita suna bata dawo ba"
"To ki kawo masu Abinci da ruwa"
Da sauri yace"a'a mun koshi "
"Ai koda ma zasu ci ya kare dan na yara ne ya rage"ta faɗa tana barin dakin.
Baffa Bube ne ya dago labulen dakin," Inna kina ciki ne?
"Eh ina ciki,gasu Jauro ma sun zo"
"Au basu tafi ba"
"Ka gansu ne" Ta faɗa tana tambayar shi,
"Eh mun haɗu a zaure"
"Jauro naji ance ka dube gidan gona a cin birni"
"Eh,Baffa ai yakai shekara biyu,tun lokacin da na faɗa maka sai dai in ka manta ne?
" Au ina ce wani ne ka buɗe "
"A'a tun wannan ne"
"To me zai hana ka dawo dashi ƙauye ai ina ga zai fi,in akwai bisashe,kana iya haɗawa da nawa na maka kiyo tunda mu nan babu matsalar abinci"
"Haka ne Baffa"
Murmushin nasara yayi,yana zama a bakin ƙofa,maimakon tsaye da yake"yaushe za'a kawo su?
"Eh to,bari nayi lissafi,dabbobin gado na yanzun sun kai guda nawa?
Nan take ya bata fuska" Bana faɗa maka tsawa ya faɗa masu ba,wasu kuma su ake ta saidawa lokacin kana makaranta ana turama Alhaji Abubakar kudin ya tura maka"
Ajiyar zuciya ya sauke"ina ga dai kawai mu bar maganar kiyon nan,dan bana son wani tsawar ta kuma faɗa madu duk da basu wace biyar ba,"ya faɗa mashi haka dan baya son susan abinda ya mallaka.
Tsaki ya ja yana mikewa"Inna ni na tafi gona"
"To bazaka tsaya ku karasa magana ba?
" Kyale shi kawai,sai dai inna dawo"bai jira amsar ta ba ya wuce.
Murmurewa yayi"mu zamu tafi kaka sai dai wani lokaci kuma "ya faɗa yana ajiye mata dubu biyu,
" Ka dai dinga kawo ta tana shiga dangi "
"Insha Allah"
Godiya tayi mai tana saka mashi Albarka,sannan suka fito,a bakin ƙofar gidan suka iske Adaidaita wanda yake cike da Doya da kayan miya a bayan but harda kaji guda biyu,duk a gidan Malam Liman me aka basu.
Suna shiga mutumin ya ja suka kama hanyar barin Ƙauyen.
Lokaci-lokaci takan dan kalle shi,tamkar akwai abinda kecin ran shi.....
*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*49*
*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*
Koda suka isa gida har uku na yamma tayi,
Kowa dakin shi ya shige,dan haka wanka ta fara yi sannan tace Aisha ma ta shiga tayi,
Riga da siket ta saka,waɗanda suka dame mata jiki,
Fitowa tayi ta shiga dakin shi,
Zaune yake ya tasa takardu a gaba,sai dai kuma sam hankalin shi baya kan takardun,
Alamu ma ya nuna kamar tunda suka dawo ba abinda yayi,har tayi sallamah ta shigo bai sani ba,
Zama tayi a gefen shi,ta daura hannun ta saman nashi,
Juyowa yayi ya kalle ta yana sauke ajiyar zuciya,"yaushe kika shigo?
"Yanzun,nayi sallamah baka amsa ba,tunanin me kake yi? Ta faɗa tana langwabe wuya.
Girgiza kai yayi yana dan sakin murmushi," Babu komai,"ya tashi zai bar wurin,
Da sauri ta rike hannun shi cikin shagwaba tace"ina zaka muna magana,ba zaka faɗa min ba,"
"Babu komai da gaske"
Bai ankara ba kawai sai ji yayi ta fashe da kuka ta saki hannun shi tare da barin dakin,