← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 49

Sashe 2

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A baiyane tace "ya Allah ka raba ni da auren wannan bawan naka" Kara gyara zama tayi yayin da zuciyarta ya tafi tunanin farkon haɗuwar ta dashi,wanda ita tun a ganin farko wanda bata sanshi ba bai san ta ba,taji haka kurin mutumin bai mata ba,karamin tsaki taja,"kai Yawo ma dai bai yi ba a rayuwa,da ace ranar batayi Baba karyar zata taya Aunty Amina gyaran daki ba da haka bai faru da ita ba,da basu haɗu da juna ba,"a wannan ranar kuwa tana kwance ne a gida tana barcin asara,in ji ta,bata da in da zata yi,kawai sai ga kiran Rahina,cikin yana yi na mai barci ta ɗauka,wanda daga ɗayan bangaren tace"Sumayya kina ina ne?

"Gida mana"

"A'a baki samu zuwa bikin Rose bane,gashi har za'a tafi park "

Zabura tayi ta duro daga kan gado,tana missike ido"ke wallahi na manta yau ne,gani zaune a gida dama babu wurin zuwa"

"To ki dai yi sauri kam,dan ƴan makarantar mu ma duk gasu nan sun iso"

Ihu tayi"ke ki ce yau da ansha dani,bikin Rose tamu gaba ɗaya ai ganinan zuwa"da sauri ta ajiye wayar,
Fitowa tayi tsakar gida,tana niman ruwan wanka,sai dai duk durom din da suke ajiye ruwa ba komai a ciki,
Tsaki taja"wai yo Allah na,to yanzun ina zan samu ruwan wanka "

Ƙanwarta ƙarama ce ta shigo gidan da leda a hannun wanda daga dukkan alamu aikanta aka yi,
"Yauwa ke Aisha zo nan"

Zuwa yarinyar tayi ta tsaya "gani Sumayya"

Harara ta dalla mata"wai me yasa yaran nan bakuda kunya ne,ke nafa na baki aƙalla shekara goma sha uku,amma shine ba ki iya ce min Aunty,sai Sumayya gatsau,in da yaran masu kuɗi suka fiku kenan,sai da kaji ance Aunty Baby,ko Aunty wacce,amma ku ya'yan talaka sai rashin kunya tsiya "

Daga bayanta taji muryar Mama na faɗin "daɗin abin dai ubanki talaka ne,kin ga a rashin tarbiyar harda ke"

Juyawa tayi ta kalle Mama tana turo baki"ni fa Mama da Aisha nake magana,ba ki ji wai Sumayya take kira na bancin na girmeta "

"To sannan Uwar ta,ke zo nan oh,kyale ta"

Da gudu kuwa yarinyar ta wuce tana mata gwallo.

Nuna kanta tayi"ni ko,ni kike wa gwallo ko,dan kin ga Mama na ɗaure maki,zamu haɗu,ai zan kami ki "

"In kin gama faɗa sai ki zo ki dibo mana ruwa a gidan Malam Sa'adu,tunda kin ga ko tarfe ba mu da shi a gidan"

Zaro ido tayi tana kallon Mama kamar taga abin tsoro,domin a duniyar Allah idan akwai abinda ta tsana shine ace taje dibo ruwa,haba,haba,ai wannan ba ƙaramin zubar da Class bane,kamarta,yanzun ace kamar ta ce zata dibo ruwa kuma tun daga nan har bakin layin su gidan Malam Sa'adu,kawai sai a ganta da baho akai wai tana dibar ruwa,ai wallahi samarinta ma dariya zasu mata,
"Mama dibar ruwa kuma,ɗan Allah ki saka su Abdullahi mana kin ga ni yanzun ma fita zan yi,"

"Wasu Abdullahi,yaran da basu nan,duk basu dawo makaranta ba,dan haka wa kike son in aika,gashi lokacin daura girki yayi,ai kema dai kin gani ba nida ruwa, mdan haka bana son wata doguwar magana,ina jiran ki" ta faɗa tana jan hannun Aisha zasu shiga daki,juyowa tayi"kar in ji kin bar gidan nan da sunan zuwa unguwa,kin dai san halin Baban ku in ba so kike ki saka ni cikin matsala ba"

Hawaye ta fara,oh Allah me yasa ka yini a gidan iyaye talakawa,da yanzun ina Dubai ko London ina hutawa ta,ko kuma ina kan gado yana juyawa dani,sai kuma da sauri tace Astagafurullah,
Daki ta goma ta ɗaki jakkanta wanda kayan kwalliyarta ke ciki,madubi ta dauka ta dauki man baki ta shafa,ta dauki ɗankwalin ta dake gefe ta goge fuskarta dashi tas,
Jakkan kayanta ta buɗe ta dauki wani Les da Aunty Amina ta bata,ta saka ta yafa gyale,
Ta windon dakinta ta lelleka tsakar gida,sai da ta tabbatar ba kowa sannan ta fito da sauri_sauri ta nufe kofar gida tana fita da sauri ta shige gidan makotarsu,har tana ba matar dake tsakar gida tana shara tsoro,waigen bayanta take"Sumayya lafiya,waya biyo ki "

Itama juyawa tayi ta kalle bayan nata,"babu kowa,"

Dafe kirji tayi"wai har kin ban tsoro"

Bata ce mata mo kai ba,sai butar data gani a tsakar gidan ta ɗauka,wanke kafarta tayi dashi,sannan ta koma saman dakalin kicin ta zauna,jakkan hannunta ta buɗe ta ɗauko wani karamin robar mai ta shiga mutsukawa a kafa da hunnu,

Kallon ta matar tayi rike da baƙi "naga ta kaina,ƴan matan zamani sai da daka tsami,babu wanka"

Kallon ta tayi"ba zaki gane ba maman Aminu,wallahi ba muda ruwa ko dis,yauwa Mama tace wai ɗan Allah ki ranta mata roban fenti guda ta fara aiki dashi,idan su Abdullahi suka dawo makaranta zasu dibo maki "

"To ba damuwa gayacan ki ɗauka ki kai mata"

"A'a idan dai kin samu yaro ki daura masa ya kai mata dan ni dai sauri nake yi"

Kallon ta take"naga dai ta ƙofar gidan zaki bi ki fita ba sai ki mika mata ba"

"A'a ta bayan gidan nan zanbi dan bana son saka ido irin na mutanen unguwar nan"

Girgiza kai kawai tayi taci gaba da aikinta,dan in dai halin Sumayya ce sai dai taba wani labari,

Tana gamawa ta tashi ta saɓa jakkanta,a yanda ta fito wata shar da ita ka ɗauka yar gidan wasu masu kuɗi ne,gashi dai ko kwalli bata shafaba,man baki ne kawai sai kamshin da take yi,yanda kasan wacce tayi wanka,"Maman Aminu na wuce"

"Allah ya tsare" Tace tana mata fatan shiriya a zuciyar ta,mutane da dama suna mata kallon yar iska ce,saboda yawo da Shige shige irin nata,sai dai ba haka take ba,ita ta san halin yarinyar,sai dai rashin ji da taurin kai irin na ta,uwa uba rashin kunya,.

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su ɗaura min littafi a shafinsu ko a mai da min littafi Audio ba tare da izina ba*
*3*

Kamar yanda ta faɗa haka kuwa akayi,ɗan ta bayan gida tabi,bata yarda ta biyo ta cikin unguwar su ba,sai bayan gidajen mutane data tabi,tana kwana,da haka har ta fito bakin titi,
Bata wani jimaba a bakin titi ta samu abin hawa,"Malam Tunga zaka kaini,nawa"

"Dari biyu"

Waro ido tayi"dari biyu fa,sai ka ce zanbar gari,kaga ajiye ni a Mobile,tunda Saba'in ne"

Kallon ta yayi daga sama har kasa"haba Hajiya,ai ba girmanki bane,kawai ke da zaki ce muje kawai,"

Hararanshi tayi"kaga in bazaka Tunga a dari da ishirin ba,ka sauke ni Mobile,shima in ba zaka ba,ka ƙara gaba"

Girgiza kai yayi"shigo muje,amma dai dari da hamsin zaki bada "

"Kai dai ka sani" ta faɗa tana shiga,
Ita sai lokacin ma ta lura da ashe akwai mutum zaune a ciki,kallon shi tayi,wata kodaddiyar bulun riga ce a jikin shi mai dogon hannu,irin wanda yake da botiri a ƙarshen hannu, da wata baƙar wando irin wanda yawanci a gwanjo ake samun irin su,itama ta fara canja kala,sai talalmi cover shoe,wanda fatar takalmin ma ya fara tashi,
Bayan ta gama kare ma kayanshi kallon ne ta maida idanun ta kan fuskarshi,

Baƙi ne sosai,sai dai ba irin wuluk ɗin nan ba,gashin kanshi a cike yake mai laushi irin ma fulani,wanda shi kawai zai nuna maka cewa shi Fulani ne,ba shida wani dogon hanci,haka kuma bakin shi madaidaici ne,ba zaka kira shi ƙarami ba tunda yanada dan girma,kamar yanda idanun shi basuda wasu girma,kai a takaice dai yana cikin gerin mutanen da za'a saka cikin Babu Yabo Babu Fallasa,haka kuma ta bangare guda duk da a zaune yake ta tabbatar da baida tsawo,

Yana juyowa kuwa suka haɗa ido da ita,ai kuwa harara ta zuba mashi tana matsawa gefe,dan ita kama yake mata ma yan kidnapping,

Waya ce ta shiga kara babu kakkautawa,da sauri ya ciro wayar daga Aljihun shi,wanda ganin kalar wayar dake hannun shi ne yasa zarginta ya ƙara girma a zuciyarta wato ɗan Kidnapping ne,in ba haka ba ta ina kamar wannan bagidajen,ba ƙauyen za'a ganshi riƙe da waya IPhone kuma ba ƙarama ba,a ƙalla daga gani zatayi dubu dari biyu da wani abu,

Receiving call ɗin yayi,ya saka wayar a kunne,sai dai cikin rashin sani hannun shi ya danna amsa kuwa,
Kawai sai ji tayi daga ɗayan ɓangaren ance "Kai JAURO amma ka cika ɗan iska,shine zaka bani Condom marasa kyau"

"Kamarya marasa kyau?

" Eh mana ina sakawa ko gamawa banyi ba sai gashi abu ya yage,Allah saura kaɗan nayi ma Madam bari"

"To killa dai baka saka da kyau bane Malam"

"Wallahi sau uku kenan yana min haka,dan haka zan kawo maka sauran kwalen a canja min wasu,dama kwalli goma ne,to gashi ko daya bai kare ba"

"To ba damu ka kawo min gida zuwa anjima, sai na canja maka da wani"

"Yauwa na gode aboki na"

Tsaki yaja yana kashe wayar.

Ji yayi mai keken yace"Malam Condom kake sayarwa ne"

"Eh ko zaka siya ne"

Dariya mutumin yayi"ikon Allah,kowa da kalar tashi sana'ar,yanzun nawa kake samu riba a kwali daya"

"Dari da hamsin mana,"

"AH lallai ba laifi,to yanzun ina son kwali biyu zan samu"

"Me zai hana abu na kuɗi"

Dariya suka saka a tare,

Jin anja tsaki daga gefen shi ne yasa ya juya ya kalle ta,wannan karon ma hararan shi ta kuma yi,

"Malama kwali nawa kike so?

Ya tambaya babu alamu wani Dar a tare dashi,

Zaro ido tayi har tana dafe kirji," Me kenan ?

"Condom mana,kinsan yana da kyau ƴan mata su dinga amfani dashi saboda tsaro"

Tunda take a rayuwarta ba'a taɓa faɗa mata magana mafi muni ba irin wannan,wani irin bacin rai ne ya sauko mata,wanda har sai da ta kasa magana,
Kallon me Adaidaitan tayi cikin bacin rai"Malam sauke ni anan"

Juyowa yayi "Amma kince Tunga zaki sauka ai,kuma gashi ko Mobile bamu kai ba"

Cikin masifa tace"nace ka sauke ni,na fasa zuwa,ka sauke ni"

Tsayar da Adaidaitan mutumin yayi,

Cikin fishi ta fito"wato fatan iskanci kuke min ko,kai kuma harda cewa in siya Condom,to ta Allah ba taka ba,har in yi aure bazan taba yawon karuwanci ba sai dai kanwarka tayi"
Chapter 2 · 0% Book details