Sashe 49
Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Duk kallon mamaki suke ma Aisha yarinya karama shekara takwas ta san ta faɗi haka,ko da yake ba laifinta bane ga mai laifi nan tsaye tunda shine idan ya tashi ci ma uwarta mutunci baya duba idon yarinya,Alhalin su yara basa mantuwa,shi yasa bai da kyau idan faɗa ya haɗa ma'aurata suyi shi a gaban ya'yansu,domin yaran zasu girma ne da abun acikin zuciyar su,kamar dai Aisha,gashi kiri_kiri take faɗa masa ba gidan shi bane.
Jawota yayi jikin shi ya rungume ta"ki yi hakuri Aisha,na sani,ba nazo koranku bane,nazo ne niman yafiyar ku,kai ni wurin maman ki"
Bata ce masa komai ba sai zame jikinta da tayi a na shi tayi gaba suna biye da ita a baya,har ta buɗe ƙofar ta shiga,
Ganin sun tsaya ne tace "ku shigo sai na kira Mama"
Bin bayan ta suka yi,sai dai suna shiga suka sake baki wurin kallon hadadden falo,
Manya kujerun zama tima_tima waɗanda suka kusa cika falon,kai ko TV su ma na bango abin kallo ne,idan ka yi wasa ko silin da wutar da aka kawata falon dashi zai iya dauke hankalin ka,
To ko dai nan gidan da take aiki ne,
Su dai sunyi shahada sun zauna amma kansu ya kasa tsayuwa wuri daya,
Suna zaune sai ga Amina ta fito daga wata kofa sanye da doguwar riga,ta yi kyau ta ciko kamar ba ita ba,ciyon fuskarta kaɗan ya rage ya gama ɓacewa,
Babu wani sakin fuska ta gaida su ta shiga kicin ta dauko limun kwali a tire da kofuna ta ajiye a gabansu,ganin da gaske ƙoƙarin tafiya take kamar wacce bata sansuba yasa yace"Amina baki ganni ba"
Kafin ta basu amsa ne suka ji wani ni'imtaccen kamshi turare kafin taku ya biyo baya,sanye take da hijabi iya guiwa,sai Atamfa riga da zani wanda zanin ne kawai kake iya gani,dai kuma takalmin ta da yake zubin silifas amma mai kyau,
Yanda kasan ba ita ba,ta kara ƙiba da cikowa har wani haske ta ƙara,na kwanciyar hankali,
Da kallo suke binta har ta iso ta zauna kan daya daga cikin kushin,
Kallon su take cikin kwanciyar hankali,babu wani firgita ko mamaki,"Baba ina wuni,"
Da kyar ya iya amsawa har bakin shi na rawa,
Kafin suma ta hada cikin jam'i ta gaida su,wato da yayanta da shi uban gaiyar,
A sulake suka amsa,
"Baba da fatan lafiya na ganku da rana tsaka?
Sun ma rasa ta ina zasu fara bayayi,dan kowa jikinshi yayi sanyi,domin a yanayin da sukayi sammanin zasu same ta,sai abin ya juya,
Shine dai ya ɗaure ya fara magana" Dan Allah ina niman Alfarma ko zaki kira mijin Sumaiya kice ya kawo ta ina son ganin ta,dan nafi son na fara magana a gaban kowa"
"Kai me zai hana ka kira shi da kanka"
Dukar da kai yayi,cikin jin kunya domin ko number Jauro bai da shi,
A hankali yace"dan Allah "
Mamaki ne ya kamata,yau shine da ce mata dan Allah cikin kwantar da murya,to Allah ya mata tsari dashi da abinda suke tafe dashi,
Kallon Amina tayi",kiramin yayanki kice yazo shida Sumaiya'"
Da to ta amsa,
Tashi tayi tace"zan koma ciki idan sun iso zan fito"
Ba wanda ya iya ce mata komai da kallo kawai suka bita,
Bayan mintuna ishirin da uku,sai gasu sun iso,ita kanta Sumaiya kallon gidan take,domin be faɗa mata inda zasu ba,
Ganin mutane dake zaune a falo da Aisha dake wasa yasa ta fara tsorata kardai ace Mama ce ta mutu,da sauri tayi wurin Amina a tsorace,"ina Mama"
Riƙo hannun ta tayi suka bar Jauro a falo shida su Baba,
"Ke ki natsu tana daki"
"Lafiyar ta kalau dai?
Tura ƙofar tayi suka shiga,da gudu ta fisge hannun ta cikin na Amina ta rungume Mama tana sauke ajiyar zuciya" Mama har naji tsoro,meke faruwa,nan kuma ina ne"
Zaunar da ita tayi"ki natsu,nan gidan mu ne"
Ƙara kallon dakin take"gidan ku kuma?
Ajiyar zuciya Mama ta sauke,sannan ta shiga ba ta labarin duk abinda ya faru tsakanin ta da Jauro har yau da zuwan Baban su,"Sumaiya mijin ki ɗan Albarka ne,dan Allah ki rike shi da zuciya daya,ki kyautata mai kamar yanda ya ke kyautata min,babu ranar da bai zuwa dan duba lafiya ta,"
Cikin tsananin mamaki tace"amma Mama bai taba fada min ba,wani lokaci har kuka nake masa akan ya kawoni na duba lafiyar ku amma sai yaki"
"Shi yace kar a faɗa maki,kinga harda takardun gidan duk ya mallaka ma Mama" Cewar Amina,
Kukan farin ciki ta fashe dashi tana rungume Aunty Amina "na gode_na gode"
Ture ta tayi suna mata dariya ita da Mama "mijinki zaki je ki rungume ki masa godiya ba ni ba"
Aisha ce ta shigo tace"Mama ana magana a falo"
Tare suka fita dukansu,
Kallon Mama Baba yayi kafin ya fara bata labarin duk abinda ya faru,yana yi yana kuka tare da nuna tsantsan ladamarshi,gashi babu damar maida ita ya riga tayi barna,ya cuce rayuwar shi,
Baba ma ya Daura ya bada nashi haƙurin har da cewa ta bar aikin da take yi,ta zo ta koma gida zai bata babban daki kuma za'a dunga zuba mata abinci ita da yaranta,
Baban Aisha ne yace"in kuma baƙi son komawa ni zan dinga biyan kudin haya dana karatun Aisha har da na Abincin ku duk wata"
Murmushi tayi tana godewa Allah daya nuna mata wannan ranar a rayuwar ta,
"Ni Bani da abin da zan faɗa sai dai in ce Alhamdulillah,domin yanzun bana cikin kunci da tashin hankali,ina cikin farin ciki ni da yara na,wannan gidan da kuke gani ba aiki nake yiba,gidanane mallakina,wanda ɗan da Allah bai Bani ba a baya ya Bani yanzun,wato Jauro,a lokacin da nike tsaka da niman taimakon wadanda nake tunanin zan iya jingina da su,suka juya min baya,sai gashi Allah ya kawo mun shi,ya gama min komai,ya saka ni farin ciki,ya siyamin gida,ya Bani abinci,yana kula da ya'ya na,yanzun haka yasa mijin Amina ya bada takardar ta makaranta zata koma,dan haka idan nace na kullace ku kamar ban gode ma Allah bane,ni na yafe maku duniya da lahira,komai ya wuce,suma kuma yayana sun yafe maka domin kullun cikin yi masu nasiha nake,Amina ku faɗa ma babanku"
Duk jikinsu sanyi ya kara yi,
"Baba mun yafe maka" Suka haɗa baki wurin fada,domin yafe mashi babu abinda rai kara masu koya rage masu,haka kuma rashin yafe mashi,sai dai ma yasa suta rike abu a zuciyar su,
Kuka ya fashe dashi,yana fadin"na cuce kaina son zuciya ya kai ni ga aikin dana sani"haka dai suka ta kwantar mai da hankali kafin su wuce,
Tana ganin sun bar falon ta tashi da sauri ta rungume shi tana fashewa da kuka tare da dukanshi a kirji,dariya ya fara to me kuma na kuka"
"Shine baka faɗa min ba"
"Ba komai bane dan ɗa yama mahaifiyarshi sai ya faɗa"
Ranar a gida ta yini sai dare yazo suka sha hira tare kafin su koma gida,
_____a bangaren ƙauye kuwa,ƴan sanda sun samu nasaran kama yaran Baffa Bube,Bakari da Ɗan Fodio,waɗanda ake ma zargin yin Kidnapped,
Ranar Uwar su kamar tayi hauka,
Dama ita rayuwa haka take,wani idan ya canja wani ba zai taba canjawa ba sai dai ya mutu da halin shi,ko mai kyau ko mara kyau,Allah dai yasa mu cika da imani,
Amma kam su Ahalin Jauro halin su na nan yanda take,kwana biyu idan abin yayi sauki,idan kuma ta juyo sai hamdala,haka suke tasu rayuwar,
Sumaiya kuma ba ko yaushe suke zuwa ƙauye ba,sai lokaci-lokaci yake kaita,sun san halinta,duk girmanka idan kai mata abinda hankali bai ɗauka ba yanzun zata gwada maka nata kalar haukan,
Kamar kuma yanda Jauro ya faɗa ya samar mata aikin koyarwa a makarantar secondary School,a nan unguwar su,
Rayuwar su suke cikin tsananin soyayya da kwanciyar hankali,
Sai da tayi wata biyar a gidan shi kafin Allah ya bata ciki,ranar murna a wurin Jauro ba'a magana,duk wani masoyin shi sai da ya faɗa mashi,
Cikin ta naɗa wata takwas aka nada shi a matsayin Ministar of Health,na Niger State gaba ɗaya,Al'amarin daya faranta zuciyar masoyan shi,
Mama kuwa yanzun a danginta har wani girma na musamman ake bata,duk in da ta shiga,wanda ita kallon kowa take yi kar da kar,
Su Momy kuma idan sun samu hutu Baba yakan kawo su wurin Mama su mata hutu dan bata zubar dasu ba,
Yayin data bangaren Mama Momy ta shiga duniya ba'a masan in da take ba,
Cikin hukuncin Ubangiji Allah ya sauke Sumaiya lafiya inda ta haifi ƴan tagwage duka maza,
Daya yaci sunan Baban shi Jauro,wato Abdul-Aziz,daya kuma Abdul Hakim,
Sai dai muce Allah ya raya,ya kuma shiryar damu akan hanya madaidaiciya.
*Alhamdulillah*
To masu karatu anan na kawo karshen wannan littafin nawa mai suna Jauro,
*Sai kuma idan Allah ya nufa FITILAR DARE,zata haska mana hanya domin yin WATA TAFIYAR,tare da SARDAUNA,sai mu haɗe da JAURO domin dauko maku ƳAR TSANAR ZINARI,bayan Sallah idan Allah ya kaimu rai da lafiya*