← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 49

Sashe 44

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

Tana shiga gidan da sallamah ta gaida matan gidan,Uwar gidan shi da suke kira da Goggo ta tambaya"ko Baba na nan?

"Ki shiga yana ciki"
Godiya ta mata sannan ta shiga dakin bayan ya bata damar shiga.

Ko zama bata yi ba yace"kinji daɗi kin kashe ma yar ki aure sai ki yi yanda kika so dasu,tunda kin nuna ba wanda ya isa dake "

Wato har yazo ya riga ta faɗa kenan,
Tsugunnawa tayi guiwa biyu a gaban shi,"Baba ka bani dama na maka bayani akan komai"

"Babu wani bayani da zaki min,domin na riga nasan komai,ba dai zaman gidan kike son ba,ai gaki gashi sai kiyi,akwai dakin dake kusa da dakin yara babu komai a ciki sai ki kyara ki zauna,ni ba nida karfin da zan ciyar dake da iyalan ki,sannan zan ƙara tuna maki ba kida gado a nan gidan domin babanki ya riga iyayen mu rasuwa,zaman ki anan na ɗan wani lokaci ne sai kiyi ƙoƙarin shawo kan mijinki ki koma,"

Kokarin danne zuciyarta kawai take yi,tana haɗiye abinda ke taso mata,"na gode Baba,"ta mike tana fita,tsaki yaja yana kyara kwanciyar shi,

Tana fitowa ta sami Goggo in da take kyara wuta"Goggo wai in ji Baba ki nuna min dakin kusa dana yara "

Da hannu ta nuna mata"gashi can"

Dakin ta nufa tana kallo,karamin daki ne wanda ko rabin kayansu ba zai dauke ba,gashi babu windo babu ƙofa,innalillahiwa'inna'ilaihi rajiun,abinda take ta maimaitawa kenan,
Sallamah taimata ta wuce,
A wani lungun dake unguwar su wanda ba'a cika bi ba,ta tsugunna ta shiga rusa kuka, dan ji take kamar zuciyar ta zai fashe dan irin raɗaɗin da yake mata,kuka take sosai wanda sai da tayi kusan minti talatin kafin ta iya sai_sai ta kanta,bawai danta gaji da kukan ba,
Tashi tayi ta goge fuskarta sannan ta kama hanyar gida,zuwa lokacin biyar saura,ta san kudin dake hannun ta kwata_kwata bai wuce dubu uku ba,sai kayan miyar da bai wuce na dari uku ba,dama shi take siyarwa,kuma a yau tayi niyar zuwa kasuwa ta siyo,sai ga zuwan Sumaiya,
Tana shiga a lulluɓe ta same Amina tana rawar sanyi,Sumaiya kuma sai sannu take mata,
Bata jira komai ba tace ta tashi suje chemis,sai dai ita Amina taki yarda wai sai dai kawai a siyo mata magani ta sha na ciyon jiki,
Da yake basu da nisa da kemis shine Sumaiya ta amsa dubu daya taje ta hado magunguna,
Tana kallon idon Mama tasan cewa tayi kuka,bancin damuwar dake kwance a fuskarta,sai dai sam ba zata iya tambayar ta ba,dan bata son ta kuma tada mata da wani mikin,

Ganin Aunty Amina tasha maganin ne yasa suka fara haɗa kayan cikin manyan buhu ita da Mama,
Sai da suka kammala sannan ta fita ta kira mai Adaidaita suka zuba kayan a ciki,
Ita take binshi suna kai kayan tare,sai da sukayi mayawa biyu da kaya,ana uku kuma ta dauko Mama da Aunty Amina,
Ita kanta hankalin ta a tashe yake ganin irin dakin da su Mama zasu zauna,amma ba tada yanda zata yi,
Tabarma suka shimfida ma Aunty Amina ta gefen dakin sannan suka shiga ita da Mama suka share dakin suka kyara,sannan suka shimfida kafet,
Katifar Mama dayafi girma suka shinfida,sannan sauran kayan kuma suka hada wuri ɗaya suka loda shi,

Gabaɗaya dakin a cike yake ɗan wurin sallah kawai suka bari,
Lokacin ma har Ana shirin kiran sallah Magrib,
Aisha ce ta shigo dakin tana fadin"Mama zanci tuwo"wanda ba komai ya sa ta fadin haka ba face ganin yaran gidan dake cin tuwo,kuma babu wanda yace mata ta zo ta amsa,

Laluba Ajjihunta tayi kwata_kwata abinda ya rage mata bai wuce dari bakwai ba,sai garin masara da take dashi da bai wuce rabin mudu ba,

"Nasan yanzun mijinki zaizo yaa kamata ki kira ki faɗa masa inda kike karyaje can bai same ki ba,ni bari naje ya siyo kayan miya na dawo"

"To Mama ki kawo na siyo "

"A'a bari dai naje"

Gyaɗa kai ta yi,sannan da ɗauki wayar ta tana kiran number shi,ganin Aisha na kokarin fita ne yasa tace"ke Auta dauko ga leda can da Jauro ya kawo muga me aciki"

Da gudu ta dauko ledojin,
Buɗewa tayi,Manyan Gwangwanayen kayan shayi ne da suger Kwali,sai biredi manya sinki biyu,da kuma Chocolate,dasu cake,sai wata Envelop data gani tana buɗewa taga kudi wanda ta kirga taga dubu goma ne cip,
Ba ta san sanda ta saki murmushi ba wani irin daɗi na kama ta,karo na farko daya mata abinda ya birgeta kuma ta ji daɗin shi har a zuciyar ta.
"Aisha dauko roban kindirmon da muka kawo na zuba maki ki sha kafin a gama abinci"

Jin ya dauki kiran ne yana sallamah yasa ta amsa mashi,"idan zaka zo kazo Limawa family house din su Mama ka sauke ni"

"Me kuma ya kaiki Limawa?

" Is a long Story sai ka zo"
"Ok"ya faɗa yana katse wayar.

Tashi tayi ta hada wuta a Abaca tunda sunzo da gawayi,yana kamawa ta ɗaura ruwa a kofi,yana yin zafi ta juye a kofi ta Daura tukunya ta kuma saka wani ruwan,
Tea mai kauri ta hada a kofi ta ajiye a gefe,sannan ta taimaka ma Aunty Amina wacce Mama ta saka ta zauna tunda Magrib ya gabato ta sha Tea din,sai da ta tabbatar tashanye sannan ta kyaleta,
Sai da tayi sallah sannan ta juye ruwan zafin ta taimaka mata tayi wanka ta gasa jiki,

Mama ce tace"ina aka samu kayan shayi haka"ta faɗa tana shan kindirmon data diba a kofi,

"Kayan da Jauro ya kawo ne,gashi ma harda kuɗi a ciki" Ta faɗa tana mika mata,

Amsa tayi tana saka mashi Albarka,da Allah ya gani wannan kudin da kayan ba karamin taimakonta zaiyi ba,

"Mama wallahi hankali na ba'a kwance yake ba,kalli wannan dakin fa babu wundo babu ƙofa,"

"Ai ga labule nan mun saka,kuma wata rana sai labari"

Ajiyar zuciya ta sauke tana daukar wayar ta dake ƙara,
"Ina ƙofar gida" Abinda ya faɗa kenan,
Ji take tamkar tace masa ya wuce kawai ba zata ba,
"Gani nan fitowa"
Kallon Mama tayi tana marairaice fuska"Mama yazo"

Murmushi tayi tana gode ma Allah a zuciyar ta,ko ba komai ta samu sauki ta wurin Sumaiya tunda tana zaune lafiya da mijinta,"tashi ki tafi Allah ya maku Albarka,ki ƙara mai godiya"

"Amin Mama" Lekawa tayi in da Aunty Amina take,sai dai tayi barci ko,gashi sai zufa take haɗawa dan har anyi sallah Isha,
"Idan Aunty Amina ta tashi ki gaida ita,in sha Allah ina nan zuwa in kara dubata"

"Zata ji"

Aisha tarakata har kofar gida tashiga mota sannan ta koma gida,

Kallon ta yayi yana tada mota"yana ga fuskarki tamkar kinyi kuka"

"Ni ban yi kuka ba"

"Allah yasa,amma idanun ki sun nuna"

Bata bashi amsa ba,dan bata son magana,
Tsayawa taga yayi ya siya masu gasasshen kaza,
Suna zuwa gida wanka tayi ta saka wani rigar bacci fari tas,iya cinya ko bran bata saka ba tayi kwanciyarta,tana tunanin halin da su Mama ke ciki,
Kallon dakin da take kwance tayi,ga AC na tashi,haka kawai ta tsintan kanta da fashewa da kuka,ta ja bargo ta rufe kanta tana cigaba da kuka,

Bata ji shigowar shi ba sai jin tayi mutum ya zauna kusa da ita,yaye bargon yayi ya dagota jikin shi gabaɗaya ya zaunar da ita saman cinyarshi,"me ya samu Baby na?

Kwantar da kanta tayi saman wuyan shi tana ci gaba da kukan ta,ba komai ne yasa ta saki jiki dashi ba sai sanin da tayi babu abinda zai mata,tunda a tunanin ta bai da wani katabus ta wannan fannin,,
"Ni dama Dazu na faɗa amma kin ce ba haka bane,faɗa min me ke damun gimbiyata"

Girgiza kai tayi"um,um,is a family matter"

Dagota yayi suna fuskantar juna"ni bana cikin family ku Sumaiya,kin cire ni a cikin family ku ko,
A tunani na tunda na same ki zaki Bani dangin ki su zama nawa,iyayen ki su zama nawa,amma kin nuna min ba haka ba"

Komawa tayi ta kuma rungume shi ta na fashewa da kuka sosai wanda yafi nada ƙarfi,dan sai yanzun ne abun ke ƙara mata ciyo,
Jin yanda ta kankameshi tana kuka sosai ne yasa bai dagota ba sai dai hankalin shi ya tashi sosai jin irin yanda take kukan to gara dai ya bar ta tayi ko zata samu natsuwa,

Tayi kuka sosai dan sai dai tayi shiru dan kanta yana aikin shafa bayan ta,
Dago fuskarta yayi ya share mata hawayen ta da tafin hannun shi,"fada min me ya faru?

A hankali ta shiga sanar dashi abinda yake faruwa tun daga farko har komawar su gidan Baba"hankali na bai kwanta da wannan gidan ba,ga kofar dakin Mama abude babu wundo,ina tausayawa rayuwar da zasu yi,in da ace Iyayen Mama na nan da hakan ba zai faru da ita ba,in da ace mu maza ne da Baba ba zai wulakanta taba,inda ace ma...

Maida ita yayi ya rungume "shiiii ya isa haka,komai zai wuce,ba gani ba,ai nima ɗanta ne,ki kwantar da hankalin ki,yanzun tashi kuje mu ci abinci"

Girgiza kai tayi"a'a na koshi "
Bai bata amsa ba sai ɗaukarta yayi a kafada ya wuce da ita dakin shi,
Duk irin kauda kan da take tayi sai da yasa ta ci sosai badan ta so ba,sannan suka yi brush,
Tana kokarin fita ne ya riƙo hannun ta"yau anan zaki kwana"

Girgiza kai tayi "Jauro yau bana jin fitina kabarni naje na kwanta"

Jawo ta gaban shi yayi ya rike hannun ta suna nufar kan gado"shi yasa nace ki kwanta a nan saboda nasan baki jin yin magana,kar kiyi min musu pls"

Bata jin yin magana dan haka kan gadon kawai ta hau taja bargo ta rufe tana addu'ar barci.

Murmushi yayi yana tuna maganar karshe da suka yi da Baffa Haruna kafin su tafi...........
*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
Chapter 44 · 0% Book details