Sashe 32
Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ai in faɗa maki gaskiya tun randa aka kai ta washe gari da aka je budan kai babu kowa a gidan har yau ina faɗa ba a san in da yayi da ita ba,ko da yake na tabbatar da yanzun haka suna ƙauye"
Dafe kirji tayi tana salati "ba dai ƙauye Sumayya zata zauna ba"
"Kamata yayi goggon su ki ce,yanzun a ƙauye Sumayya ke zaune"
Cikin jin haushi tace"ke dai wai Maman Aisha wata irin mata ce,kai tir da uwa irin ki"ta faɗa tana mikewa"ace baka san in da danƙa ke aure ba,Allah dai ya basu zaman lafiya "ta faɗa tana wucewa.
Kallon Mama tayi"hmmm adaiyi zaman lafiya mu gani," Ta faɗa tana ƙara fashewa da dariya,
Bata bata amsa ba sai ma mikewa da tayi tana barin gidan bikin ganin hankalin mutane ya fara dawowa kan su,gara ta tafi ta bar mata gidan bikin kafin taja mutane su fara saka mata baki,
Wanda ta lura haka take so,
Maganar gaskiya hankalin ta ya tashi da maganar Maman momy,sai dai kawai idan ta tuna sunyi magana da Sumayya sai taji sanyi,amma bata San me yasa ba gabanta ya faɗi da maganar matar na yanzun,
A baiyane tace"ya Allah ka kare min ya'ya na a duk in da suke".
_____________washegari ƙarfe biyu na rana jirgin su ya sauka a Abuja,
Suna fitowa Airport ya kalle ta"kina jin yunwa?
Girgiza kai tayi,
"Ok to bari mu tafi Minna kawai "
Shatar mota ya daukar masu wanda basu suna shigo garin Mina ba sai kusan biyar da rabi saboda rashin kyaun hanya,
Tunda suka shigo Chanchaga ta buɗe idanun ta,Addu'a take a zuciyar ta,Allah yasa kar ya kai ta Hotel,
Ita dai taga yana ta ma direban kwatance har suka iso wani babban estate wanda taga a jin wani signboard an rubuta Talba Estate,
Unguwar ta bayan gari yake babu hayaniya sai manyan gidaje,
A ƙofar wani babban gida mai get taga yace mutumin ya tsaya,
Shi da kanshi ya buɗe mata mota ta fito sannan ya saka hannun shi a ta jikin kofar gidan sai gashi ya ciro makulli,
Budewa yayi ya mika mata key din"ki fara shiga bari na shigo da kaya "
Kallon shi take tana kallon gidan.........
*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*41*
*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*
Ganin ya juyo da katon jakka ne yasa da sauri ta tura kofar gidan ya buɗe tana matsa mai ya shiga,
Binshi tayi a baya har ƙofar falon shiga inda anan ma sai da ya ƙara buɗe ƙofar sannan suka shiga,
Tsayawa tayi ta sake baki a tsakiyar falon tana kallon Aljannan duniya,
Falon babba ne wanda yake dauke da saitin kujeru manya manya masu numfashi har saiti biyu,ta gefe ɗaya kuma harda Dinner table,gashi ko ina yaji manyan labulaiya,Dark Blue da fari,
Gaskiya falon ya haɗu iya haɗuwa domin duk da ba wasu tarkace ne a falon ba amma da ka ganshi kasan yaji kudi,
Titowa yayi daga ɗakin da ya kai mata kaya ya zo ya same ta inda ya bar ta tsaye"ga ɗakin ki can na kai maki kaya"ya faɗa yana fita domin kwaso sauran kayan,
Bin hanyar da ya nuna mata tayi domin ta Allah_Allah take taga dakin da yake fadin nata ne,
Babban ɗakin ne mai dauke da Royal bed mai dauke da durowar madubi,sif din saka kaya,abin rataye jakka wurin saka takalmi,harta inda aka daura TV na gadon ne,sai firij ƙarami da kushin guda buyu wadanda daga ganin saitin kasan duk na gadon ne,kai ko ban dakin abin kallo ne,dakin yanda kasan dakin yar wata babban mai kuɗi,
Zama tayi saman kushin din tana sauki nunfashin gajiya,da sauri kuma ta mike jin zuciyar ta ya raya mata to idan gidan ba nashi bane fa,kai yaga kudin gina irin wannan gidan,bari dai ta je ta tambaye shi,in ya so komai dare Gara ya maida ta inda zasu zauna ba zata kallon irin wannan kwalelen ba,
Tana saka kai shi kuma zai shigo,karo suka yi,da sauri ya koma baya yana ya mutse fuska,
"Ki dinga kallon gaban ki Sumy Baby"
Shafa goshinta tayi"ni dai kazo ka mai dani gida"
Kyara tsayuwar shi yayi"wani gida kuma kike magana wai bancin wannan "
"Gidan da aka fara kai ni ma"
Ƙaramin tsaki yaja"ba zan iya zama a can ba shi yasa na kama mana hayan nan gidan dan haka sai ki kwantar da hankalin ki"
Waro ido tayi"kana nufin harda komai na gidan "
Bai bata amsa ba sai ma cewa da yayi"ni zan fita akwai kayan abinci a kicin in kina buƙata sai ki Girka"
Bai jira amsar ta ba ya juya yana ƙoƙarin fita,
Ƙara dakatar dashi tayi"na ce ba"
Wannan karon kamar ranshi a ba ce ya juyo,sai dai bai ce komai ba.
"Ɗan Allah ina bukatar waya saboda ina son in yi waya da su Mama"
Gani tayi kawai ya juya ya wuce ba tare da ya ce mata komai ba,
Da kallo ta bishi,kome ke damun shi oho,
Zagayen gidan take tana farin ciki,koda ma na haya ne abin ba karamin daɗi ya mata ba,
Kicin ta shiga nan ma wata duniyar ce,kayan abinci babu irin wanda ba'a zuba ba,
Taliya da kifi ta dafa,dan shine abu mafi sauki da zata iya dafawa yanzun,
Tana kammalawa ana kiran sallah Magrib,dan haka wanka tayi da ruwa masu dumi,
Tana fitowa durawar kaya ta buɗe duk da tasan babu komai aciki amma dai tana son ta gani ta kuma jera waɗanda ta siyo ma kanta a can,
Sai dai ga mamakin ta sif din kaya ne a ciki na ban mamaki,duk da ba zata kira shi da acike yake ba,amma dai tasan ko atamfofi dinkakku manyan zannuwa bana roba ba sun kai kala goma,sai las uku shadda uku,sai jallabiyoyi sun kai kala biyar,
Abin mamaki harda ƙanana kaya haddu irin wanda bata taɓa tsammanin gani ba,
Rike baki tayi"eeye lallai ma Jauro ɗan duniya,kowa ye ya ajiye da zai saka mashi irin waɗannan kayan oho,"tsaki kuma taja"oh na manta ma ba amfani gare shi ba,waiyo Allah na Maman Momy kin cuce ni da kika haɗa ni da raggon namiji "jawo wani hijabi babba sabo tayi cikin kayan da ta gani,dashi tayi sallah sannan ta saka wani ƙaramin wando iya cinya,da riga mai dogon hannu ta robo,rigar ya matse ta sosai,
Kyara suman kanta tayi ya sauko mata har gadon bayan ta,
Masha Allah,yanda kasan wata Yar Tsanar Zinari,
Fitowa falo tayi ta zuba taliyar ta a plate yaji kifi,ga lemun kwali a gefe,tana ci tana kurban lemu,
Tunda ta aure Jauro bata taɓa cin abinci ta koshi ba irin na wannan lokacin,dan sai da taji babu wurin zubawa sannan ta hakura,
Kyara wurin tayi sannan ta wanke kayan da ta ɓata.
Ana kiran sallah Isha'i ta tashi tayi sannan ta dawo falo ta zauna tana kallo,har wuraren ƙarfe tara na dare,
Ganin bai dawo bane yasa ta shige daki ta canja kayan barci zuwa karamin riga iya cinya da pant,sai wata doguwa wacce ake daurawa a sama,
Tayi kwanciyar ta,babu jimawa barci yayi gaba da ita,cike da tunanin gida,
Bai samu ya dawo ba sai wuraren sha ɗaya na dare,ya shigo ranshi a bace,domin daga ƙauye ya fito ba karamin tsiya suka kwasa ba da su Ɗan Fodio,dan su ba da kuɗin da za'a hada sunce ba zasu ba da ba,tunda ba uban su bane,shi kuma Yabbaleyda zuciya ta kwashe shi ya kaima Ɗan Fodio sanda,nan take faɗa ya kaure a tsakanin su,
Ana cikin haka ne,sai ga ƴan sanda sun shigo cikin ƙauyen sun kama mutum biyu samari wai ana zargin su da yin garkuwa da mutane,kuma su din abokan Ɗan Fodio ne,hakan ne yaja kananun maganganu ya shiga tashi a karamin garin kafin kace me,
Tofa shine Baffa Sanda ke cewa ai Jauro shi ya kawo ƴan sandan tunda bai daɗe da zuwa ba suka zo,kuma dan sunji ya gaisa dashi cikin harshen Turanci shi kenan wai ai baki suka haɗa,
Inna Binta harda marin shi tayi tana tsine mashi albarka wai indai yasa aka kama mata ɗan ta wallahi ba zata bar shi ba,
Ko gidan Malam liman bai jeba ya baro Rugan ranshi a bace.
Kokafin yayi wanka ya kammala abinda zai yi ya kwanta har sha biyu da rabi tayi,dan haka addu'a yayi ya kwanta,
Yaso ya samu barci ko kaɗan ne sai dai abin ya faskara dan sai juye_juye yake,
Ji yayi an buɗe ƙofar anshigo babu sallamah hakan ne yasa ya tashi ya zauna yana ƙara hasken wutan ɗakin,
Kallon ta yake yanda take tafiya jikinta ko'ina yana motsawa cikin jan rigar barcin data saka mai tafiya da hankali,
Tana isowa faɗawa tayi a jikinshi ta rungume shi tana haɗa bakinsu wuri ɗaya tashiga tsotso,
Tare da rungumo wayar shi,
Ji tayi ya zareta daga jikinshi da karfi,yana mikewa tsaye da sauri yana shafa wuyan shi,
Tashi tayi zata ƙara nufar shi ya dakatar da ita"me gaka kike yi Sumy Baby "
Cikin wani irin azababben shauki dake taso mata wanda bata san na menene ba ta ce"ji nake tamkar in ban same ka ba zan mutu,marana da jikina duk wani iri yake min,zan mutu idan baka min wani abu ba"
"Me kika sha? Ya tambaya yana jin wani irin raɗaɗi yana ratsa in da ta taɓa shi,
" Ni babu abinda na sha,dan Allah Jauro ka taimaka min ji nake kamar zan yi hauka"
Girgiza kai yayi"ki koma ɗakinki ki kwanta dare yayi"
Kuka ta fashe da shi sosai "dama kasan ba kada lafiya shine kaje ka aure ni? Yanzun gashi ina cikin wani yanayi ka kasa yin komai," Mulmula ta hau yi a kasa tana kuka tare da riƙe ciki"waiyo Allah ciki na zan mutu "