← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 49

Sashe 12

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaki Musa ya ja "ɗan ƙauye dai duk yanda akayi dashi sai ya nuna halin shi,ɗan Allah Jauro kar ka bada mu,yanzun fa babban yaro zaka koma,ka zama ɗan gayu,amma ka tsaya kana magana kamar irin wanda bai taɓa shiga aji ba,kai ko dan irin sha'awan nan ba kaji,kalli yaran makarantar ku,kowa ka gani da babban wayar shi yana yanga,daga mata har maza amma kai kullun cikin riƙe takarda kake,"

"Ai duk yan iska ne,ni kaga kar ka ishe ni da batun waya,domin ni a nawa ganin duk masu rike waya basu da aikin yi,na biyu kuma iskanci suke kallo a waya kamar dai ku"

"Oh mun shiga uku da Jauro,wai kai an ce maka duka ne aka taru aka zama daya,yanzun fa zamani ya canja,kuma zaka ce na faɗa maka da kanka zaka zo ka siya waya,"

Mikewa yayi tsaye "Allah ya raba ni,ni dai ku shirya min tsaraba kunsan ran sati ne rafiyar mu"

"Ni dai me kake son in siya maka" Cewar Musa.

"Naga Innar ka tana shanya kanzon tuwo,shi zaka karba min,sai ka haɗa min Sugar da Kuli-kuli,kai kuma Moha Garin Rogo da suyayyen gyaɗa,sai kwalin Lipton,sauran siyayyan in naje can na karasa,"

Baki buɗe Moha ke kallon shi,yayin da ya juya ya wuce abin shi yana ce masu sai sun haɗu anjima a wurin Malam liman,

Juyo da kallon shi gun Musa yayi,tare da nuna Jauro da yatsa"anya yana da hankali kuwa?

"Me yayi? Domin shi Musa bai yi karatu ba.

"China ne zai je da kanzon tuwo,har da gari,kodai ya ɗauka boarding school za shi ne?

" Au ba'a zuwa da su?

Tsaki ya ja shima ya tashi tare da bar mashi wurin dan ba zai iya da wannan haukan nasu ba,tsakanin Jauro da Musa bai masan wanda yafi wani hauka ba.....

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*16*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

A ranar da zai bar Minna zuwa Abuja ne ya je ya same Baffa Bube ya tsugunna a gaban shi"Baffa zan tafi makaranta "

Kallon shi yayi daga sama har kasa,takalmi silifas ne a ƙafar shi,sai wasu kodaddun kaya riga da wando na yadi a jikin shi,duk yayi wani kura_kura dashi yanda kasan Almajirin ƙauye,ko ɗan mai bai shafaba,to ina ma ya ganshi balle ya shafa,
Bushewa yayi da dariya harda nuna shi"yanzun kai Jauro a haka kake faɗin zaka kasar turawa karatu,ni kan anya mutumin nan ba dan yankan kai ba ne?in ba haka ba ta yaya zai ce zai kai ka kasar turawa wanda sai an shiga jirgi,sannan ace bai amsa ko sisi ba daga wurin mu,?

Shiru yayi kawai yana kallon kanin mahaifin na shi,

"To ba damuwa tashi ka tafi,idan kana da rabon dawowa Allah ya sadamu da Alkhairi,idan kuma Allah bai yi zamu kara ganin ka ba,to ka gaida mahaifinka sai mun iso,ka ce ya ajiye mana wuri zama mai kyau kar ya bari a cike wuri"

Yama rasa mai zai ce mashi,dan haka tashi yayi kawai ya fito tare da shiga shiyan Baffa Sanda,in da yake zaune shi kuma yana wasa Addan shi,
Tsugunnawa yayi shi ma a gaban shi "Baffa zan tafi makarantaba sai dai Allah ya dawo da mu"

Bai bar abinda yake ba sai kallon shi da yayi"ina ne ma kace min zaka karatun duniya "

"Baffa China na"

"Ohh,to kai dai ka san su,kai da waye zaka tafi?

" Ni kaɗai ne,amma akwai yaron Alhaji a can tare dashi za mu yi karatun"

"To madallah,idan dai kaje ka ga zasu cuceka ka gudo ka dawo gida,kar ka yarda su sayar da kai,dan wani aboki na ya faɗa min idan sun ga ba kaɗa wayau,tsaf zasu siyeka su baka kuɗin ka cinye,daga baya su zo su tafi da kai su yanka bayan ka gama tara maiko,
Dan haka kayi hankali dasu,banda kallon mata masu tafiya tsirara jauro,dan kana iya makancewa"

Jikin shi ne yayi sanyi da huɗubar Baffan na shi,to yanzun idan yaje aka siye shi aka bashi kudin shi ya cinye fa,gaskiya da an samu matsala,dan aradu ba zai yarda yana ji yana gani ya tsaya a yanka shiba,gashi yaji ance harda Naman gwangwani suke yi,
Wani tsoro ne ya kama shi,tare da haɗiye yawon tsoro,shi tsoro ma ya kama shi,sai dai kuma ba halin yace ya fasa"insha Allah Baffa,"

Ajiye Addan yayi a gefe ya saka hannu a Aljihu ya ciro ƴan dubu dai_daya a Aljihun shi tare da wasu canji,
Jujjuya kuɗin yayi,ya buɗe su,sai da ya kirga su da kyau dubu Arba'in da huɗu ne da dari biyar,sai canjin Naira Saba'in a sama wanda suke Naira ishirin_ishirin guda uku naira goma guda ɗaya,
Canjin saman ya mika mashi wato Naira saba'in ɗin tare da maida sauran kuɗin Aljihun shi"karɓi wannan kasha ruwa a hanya"

Amsa yayi yana ɗan bata fuska,dan ya ɗauka zai bashi ko da dubu daya ne"na gode Baffa,"yana gama faɗar haka ya tashi ya wuce,
Babu wanda ya mai rakiya koda nan da kofar gida ne,
Sai dai Moha wanda shi ya kai shi har cikin gari gidan Alhaji Abubakar,in da yake jira sai yaga wucewar su Abuja kafin ya koma ruga

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*17*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

Suna isa gidan har cikin falon Alhaji Abubakar Imam suka shiga da jagoran ɗan shi,
Cikin girmamawa suka gaida shi suna zama a ƙasa,
Amsawa yayi yana ƙare masu kallo,
Yasan ko yace su zauna saman kushin ba zama zasu yi ba,wayar shi ya ɗauka yayi kira,wanda ko mintina biyar ba ayi ba sai ga ɗaya daga cikin yaran shi ya shigo,
Nuna mashi Jauro yayi"ka bashi wasu kayan ya canja,kafin mu wuce"

"Ok Dady" Ya bashi amsa,tare da juyowa wurin Jauro"taso mu je"

Tashi yayi ya bi bayan shi suka fita,
Dakin shi ya kai shi ya fito mashi da wasu riga da wando masu kyau,harma da takalmi,cikin farin ciki ya amsa kayan ya saka,irin wanda bai taba tunanin zai saka su nan kusa ba,

Ya saka kaya kam,sai dai maganar gaskiya shine kayan basu wani yi mashi kyau ba,saboda kai da ka ganshi ba sai an faɗa maka ba kasan wannan duk yanda aka yi daga Ruga ya fito,shi ko dan irin wayewar nan da mutum zai nuna irin yayi karatu,to babu shi a tare da Jauro,

Yana fitowa kallon shi ɗan Alhajin yayi tare da tabe baki,ba laifi kam,ba kamar dazu ba,kyara mashi kwalan riga yayi,sannan ya ja ahi suka koma falon inda su Moha suke,

Koda suka shiga Alhajin baya falon sai Moha da aka kawo ma lafiyayyen abinci,ya ji nama manya-manya bai ciba yana jira Jauro ya zo suci,

Suna shigowa kallon Jauron yayi yana sakin murmushi,"kai Jauro kayi kyau sosai,ka zama ɗan gaye,"

Shafa rigar yayi yana washe baki "baka ga ma takalmin ba,wani irin dashi,kalan na ƴan ƙwallo"

"Gaskiya kaji daɗi sosai,matso mu ci abinci,gashi da zafin shi,zo ka gani"

Matsowa yayi ya zauna yana kallon plate din dake gabansu,
Nan suka zauna suka kwashi lafiyayyen abinci,
Suna kammalawa yaron daya bashi kaya ne yazo ya kira shi wai ya fito zasu tafi in ji Alhaji,

Sai da yaga zasu rabu da Moha ne ya fara hawaye,wanda sai da ya saka Moha din shima kuka,sai yake ganin kamar ba zai dowo ba,
Sai da Alhaji yayi aikin lallashi kafin su hakura sannan ya shiga mota suka kama hanya,

Har suka isa Abuja ko gyangyaɗa bai yi ba,yana kalle_kallen hanya,
Sai da suka fara tsayawa a Hotel kafin zuwa ƙarfe huɗu su nufi Airport,
Tashin hankali,domin kuwa sai da aka zo shiga jirgi yace bai san wannan ba,dan shi kam bai ga wurin shiga ba,balle ya shiga ya jeho shi kasa ya mutu,ba da shiba.

Da kyar da lallashi da nasiha sannan Alhaji Abubakar tare da ma'aikatan jirgi suka samu suka shawo kanshi sannan ya amince,ba dan san ranshi ba,sai dan kawai yayi imani idan har ya mutu yau to lokacin shi ne yayi,kuma karin firgicin nashi ashe shi kaɗai zai je ba tare da Alhaji Abubakar ba,wai shi sai daga baya zai zo,idan ya je zai haɗu da Ɗan Alhaji da ke can,

Masu aikin cikin jirgin wanda aka ba Alhakin kula dashi ne su suka sanya mashi belt din jirgi,su kuma suke ta ɗan kula dashi tare da kwantar mashi da hankali har zuwa sanda jirgin su ya sauka a China wuraren ƙarfe takwas na dare ne a garen.

Daya daga cikin ma'aikatan jirgin da aka ba number Sadik ɗan Alhaji shi ya kira shi ya shaida masu sun sauka ya zo ya dauki ɗan uwansa,nan ya sanar dashi ai yana ma a cikin Airport ɗin,
Tare da su ka fito in da anan suka hadu da wani matashin saurayi tsaye yana jiran su a wurin tarbon baki,dan haka yana ganin su da sauri ya zo ya rungume Jauro dan Dady ya turo mashi hoton shi,
Godiya yama mutumin kafin ya fara dariya yana amsar jakkan dake hannun shi"barka da zuwa kasar China Abokina"

Dan sanyi yaji jin ya mashi magana da yaren Hausa,"kai a gaskiya har naji daɗi da na samu mai jin yare na,"
Chapter 12 · 0% Book details