← Book details Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 58

Sashe 8

Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aslam kuwa yanacan jiki duk y murde dama shi mai siffar karfafa balle kuma y samu training yauma kamar kullum sundawo daga training shida safwan,Aslam yace wlh inaso inje gda dannayi missing dinsu da yawa,dariya safwan yayi yace kayi missing din yan gda ko kayi missing din islam saboda ai naga yan gda suna xuwa maka visiting kawai ka futo kace kayi missing din jerry dinka y karasa maganar yana kyakyata dariya,tsaki Aslam yayi yace Allah y sawake min narasa wanda xanyi missing sai wannan fitinanniyar yarinyar kai bakasan halinta bafa ita ko yaya muka xauna saita batamin rai ko kadan batason farin cikina safwan y kyalkyale da dariya yace shiyasa ai kuka xama tom & jerry kai tom ita jerry wlh abokina da xakuyi rayuwar aure da islam dakuwa na koma gidanku da xama saboda nadinga kallon drammer y karashe xancen da dariyar shakiyanci,darararsa Aslam yayi yace ko kadan ko a mafarki baxan taba aurar yarinyar nanba nasha fada maka cewa ni babbar mace nakeso wadda xata dauki lalura ta ba wannan tatsitsiyar yarinyar ba,safwan yayi karaf yace ai itama xata girma tsaki Aslam yayi yace naga kai xancen dadi yakeyi maka y dauki towel y shige bathroom wata dariyar safwan yayi yace woo Aslam na islam bada kanka a sare kaje gda kace y fadi.

Lokaci ya tafi abubuwa da yawa sun faru aciki harda gama primary skul dinsu islam rayuwa tanawa islam dadi saboda rashin ganin Aslam dan ita harmantawa takeyi dashi.

??????
*daga* *mrs* *hamisu* *taura*
[11/12, 8:58 PM] ?+234 703 443 5155?: (16/10/2016 2:00pm)na umma yahya musa

????????????
????????
????
??
*GOYON* *KAKA*
*26*
*3* *year* *letter*
Mislan 4:00pm islam ce xaune tana tsantsara kwalliya kaika rantse wata shahararriyar yan mata ce a lokacin tana da 11 year Amira ma tana gefenta tana shiryawa sunyi bala'in yin kyau englishi wears suka saka wandone pencil black da body hug ta islam purple ta Amira pink Islam tanada veil purple Amira kuma pink sunyi kyau sosai wani arnen takalmi suka saka black mai tsini da igiya ma ake daureshi.

Futa sukayi suna islam ce tayi juyi ta kashewa yaya haidar ido tace my bros yaka ganmu munyi kyau ko yace sosaima ai fadar irin kyawun da kukayi bata bakine,tace toh yanxu ka dauko mukullin mota ka kaimu gidansu khausar wanta sagir y hada mana party yace tab kuje isya ya kaiku niyau banajin xan iya futa,kallan kaka tayi ta shagwabe fuska tace kinji shiko kaka wai baxai kaimu ba kaka tadan sassauta murya tace haba angona daure ka kaisu dan Allah tashi yayi yace toh kunci albarkacin kaka kuxo na kaiku amma ku sani wlh baxan daukoku ba islam tace eh munji futa sukayi da aunty amarya suka hadu xata shiga part din kaka tace toh sarakan yawo ina kuma xakuje carab Amira tace gidansu kausar,aunty amarya tace towa kuka tambaya kuma me xakuyi,islam ta xumbura baki tace kaka muka tambaya kuma ai party yayansu kausar y hada mana kuma kaka tace muje girgixa kai aunty amarya tayi tace Allah y shirya.

Mota suka shiga islam a gaba Amira a baya y kaisu gidansu kausar y juyo dayake ba nisa neman magana ne irinna islam tace sai a mota wai itama yanxu ta xama yan mata.

Shiga sukayi har part din mamarsu khausar suka gaisheta,acikin gdan yaya sagir yasaka akayi decorating aka kawata gurin itama khausar irin dressing din su islam tayi amma ita body hug da veil dinta red kawayensu maxa da mata sunxo gurin dan harda yan islamiyyarsu sunxo.

Sagir y kalli islam yace pretty kinga kyawun da kikayi kuwa ai kin haska gurinnan tamkar xara acikin taurari,wani farr tayi da ido ta kyalkyale da dariya tace kai yaya sagir karka bani kunya mana yace au baki yadda ba kenan ko pretty murmushi tayi wanda har saida dimfil dinta y loba ta rufe idanunta da hannunta kama hannunta yayi yace taho muje muyi rawa,suka shiga d.j y saki kida su kausar suka mara musu baya suka fara cashewa.

A daidai gate din gidansu y sauka a taxi sanye yake da white t shirt da wandon kaki na sojoji kanshi da hula y daura ainahin rigar unifoam din a kugunsa yana rataye da wata katuwar jaka a kafadarsa yana da tsayi dan irin gient dinnanne jikinshi ne xai tabbatar maka da cewa kakkarfa ne dan irinsu ake kira da lion shape,hular y cire y karewa area din kallo subhanallah shine abinda na fada saboda haduwar saurayin chocolate colour ne yana da wani irin sexy eyes wanda eye lashes suka kawata shi xara2 yana da cikar gira baka kirin kwantacciya dogon hancine dashi har baka yayinda yake da dan madaidaicin baki lebenshi pink colour ne wanda ta ido xaka gane xaiyi laushi,yanada kwantaccen saje yayinda wani gashi y xagaye bakinshi wani irin sihirtaccen kyawune dashi murmushi y saki lokacin daya karewa layin kallo ai susucewa nayi saura kiris birona y fadi saboda bayyanar jerarrun hakwaranshi farare tass yayinda siririyar wushirya ta kawata tsakiyarsu daga kumatunshi na dama kuma y lotsa daidaita xaman jakar yayi a kafadarsa y fara tafiya irinta xaratan maxa yana wani taku da karfinsa nidai a tunanina xai kai 25 year amma a yadda yake saikayi tsammanin dan 30 year ne.

??????
*daga* *mrs* *hamisu* *taura*
??????
[11/12, 8:58 PM] ?+234 703 443 5155?: (17/10/2016 2:00pm)na umma yahya musa

????????????
????????
????
??
*GOYON* *KAKA*
*27*
Saida naga gdan daya shiga mutsitstsike ido nayi nace kai badai Aslam bane yaxama wannan karkarfan namijin ba da gudu nabishi ganin harya shige gdan.

Aunty amarya ce ta fara ganinshi a lokacin ta futo daga part din kaka fara'ar fuskarta ce ta fadada da sarsarfa y karasa gurinta jakarshi y ajiye y rungumeta wani sassanyan numfashi y saki yace i miss u my aunty,dariya tayi ta xareshi daga jikinta ta saki dariya tace lallai my son ka sammacemu ko waya,wani murmushi yayi wanda y kara futo da ainahin kyawunsa yace ai surprising dinku nayi,tace lallai kam kuma kaci hannunsa ta kama da daya hannun kuma y dauko jakarshi suka karasa shiga part din mommy a palo suka tarar da mommy tana kallon arewa 24 da sauri y saki hannun aunty amarya yaje y rungume mommy dariya mommy tayi tace auntyn yara gaskiya yaronnan naki baya girma kiga yadda yaxo y turmusheni,shagwabe fuska yayi yace kai my mom yanxu bakiyi missing dina ba (ni dariya y banima yadda yake shagwabe fuska ??) aunty amarya tace a'ah mommy ai duk cikin kewarmu ne tashi Aslam yayi yace su daddy basu dawo ba mommy tace eh suna kasuwa yace OK banaje naga my granny da sassarfa y fice,mommy tace auntyn yara kiga yadda danki ya wani xama kato dariya aunty amarya tayi tace ai aikin soja ba wasa bane shiyasa nake alfahari da dana dariya mommy tayi tace gaskiya tashi aunty amarya tayi tace bari naje na hadawa my son abinda xaici tunda bai sanar damu ba girgixa kai mommy tayi itadai tana farin cikin irin yadda fateema takeson yayanta.

Da sallama y shiga part din kaka kaka ta tashi da hanxari tana wanake gani kamar mai gidana da sauri y karasa yahau juya kaka saida y wanata tamkar fanka sannan y rungumeta kaka kuwa sai maida numfashi takeyi ??,yace wlh matar nayi kewarki sosai da sauri kaka ta kwace jikinta ta koma ta sauna ragwab akan kujera tana maida numfashi 1 da 1 tace lallai Aslam yauna tabbatar da sojoji bakuda imani ko tausayina bakaji ba kake wanani tamkar fanka,su ihsan da suke xaune a palo sukuwa me xasuyi inba dariya ba,Aslam ma murmushi yayi yace Allah y baki hakuri uwargidana wai irin yadda nayi kewarki na nuna miki doke hannunsa tayi da yake kan cinyarta tace naji dai murmushi yayi y tashi yana sosa keya kallansu ihsan yayi yace baku iya gaisuwa ba,suka gaisheshi y amsa sannan y fuce yana kaka ki damamin fura.

Yana futa yayi kicibis da Amir da sauri suka rungume juna,amir yace dawowata kenan daga skul aunty amarya take cemin ka dawo,Aslam yace eh shigowata kenan,Amir yace amma babu sanarwa Aslam yace eh surprising dinku nayi Amir yace gaskiya kam karasawa part dinsu sukayi bedroom dinshi Aslam y bude y shiga Amir na binshi kayan jikinshi y rage y xama daga short nikker sai vest yadau towel y shige bathroom,Amir kuwa dakin y fara kadewa y cire bedsheet y canja wani danma dakin ba wani datti yayiba kusan duk sati ana share dakin a gyara.

??????
*daga* *mrs* *hamisu* *taura*
??????

(17/10/2016 2:30pm)na umma yahya musa

????????????
????????
????
??
*GOYON* *KAKA*
*28*
Kafin Aslam y futo y gyara dakin yayi morphing ya dauko burner a dakinshi yasa turaren wuta tuni dakin yadauki kanshi (nikuwa nace lallai Amir matarka ta huta irin wannan gyara haka).

Da Aslam y futo mamakine y kamashi y kalli Amir yace ah my bros waye y gyara dakinnan murmushi Amir yayi yace waka gani a dakin,Aslam ne mamaki y kasa boyuwa a fuskarsa yace kana nufin kaika gyara lumshe idanunsa yayi y kwanta a gadon yace eh nina gyara Aslam yace lallai dan samari ka huta kai wlh ko aure kayi matarka ta huta murmushi Amir yayi yace kaima dole ka koya ai Aslam yace tab karasawa yayi gaban dressing mirrow ya shafa mai y taje sumarsa ya fesa body spray jallabiya y dauko acikin jakarsa y saka sannan y feshe jikinsa da turare kiran sallar magruba aka farayi bathroom Amir y shiga y dauro alwala,masallaci suka futa dayake a layinnasu.

Ana idar da sallah suka dawo daddy da Abba suka je suka gaisar da suke part din mommy abincin da aunty amarya ta hada masa part din mommy ta kawo masa daukar warmers din yayi Amir y dauki jug din coconut drinks din da akayi masa suka wuce part din kaka.
Chapter 8 · 0% Book details