← Book details Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 58

Sashe 4

Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

????????????
????????
????
??
*GOYON* *KAKA*
*10*
Mummy da aunty amarya suka futo suna Allah y kiyaye y tsare hanya Allah y doraku akan hajiya ta yadda ta biyoku sukace ameen suka shiga mota Aslam ne yake driving inda daddy da Abba suke a seat din baya,Aslam driving yakeyi cikin nitsuwa har suka karasa gwarxo parking yayi a kofar gidan kaka suka futa y rufe motar suka shiga ciki.
Shiga sukayi bayan sun gaggaisa da kaka ta kawo musu ruwa da lemo kallon aslam tayi tace baka tafi koyon aikin sojan ba ai naxata wannan satin ka tafi yace a'ah sai wani watan xan tafi,Aslam yace kaka ina aljanar jijarki ne hararararsa tayi tace ban sani ba murmushi daddy yayi yace aslam islam dince aljana yace ai wlh daddy tafi aljana yanxu muna xaune ma kila a kawo kararta,kaka tace to makaranta ta tafi aslam yace Allah yasa.
Sallama sukaji anayi aslam ne y tashi yaje y gano dan aikene daga fadar mai gari ana neman kaka aslam yace toh gatanan xuwa y koma y fadawa kaka aiken da a kayo gurinta mayafi ta saba Abba yace haba hajiya ki tsaya mu muje mana kaka tace a'ah dole na amsa kiran mai gari ai kudaixo muje dayake ba nisa a kafa sukaje.
Su islam suka gani sunata kuka suna sun daina baxasu kara ba iyayen su hanne ma sunxo cikin tashin hankali kaka take tambayar meyake faruwa,su Abba kuwa guri suka samu suka xaxzauna suka gaishe da mai gari,suka tambayi dalilin kiran mahaifiyarsu anan mai gari y fadawa su Abba irin ta'asar da islam da abokananta sukeyi masa a gari sannan da karar da malam tanimu y kawo anan yaja hankalin iyayen sauran yaran daya xama dole su tsawatar da yayansu in ba haka ba kuwa xai dauki kwakwkwaran mataki,sannan yace kowa y tafi da yaranshi sukayi godiya kowa y kama danshi y tafi gda.
Tun a hanya kaka take sababin masifa akan an tsanar mata jika,anan su daddy suka dinga bata hakuri Abba yace yanxu kawai hajiya ki yadda ki biyomu mu tafi kinga acan ba ruwan wani da wani,islam tace eh kaka mu tafi birni dama wlh nagaji da yadda ake sakamin ido,kaka tace toh shikenan muje mu tattara kayanmu farin ciki sosai ne y kama aslam saboda yanaji y kusa gyara islam.
Nikuwa nace anya kuwa mudaije xuwa yanxu lbrn y fara ku biyoni danci gaban lbrn??.

??????
*daga* *sisin* *mama*
??????
[11/12, 8:54 PM] ?+234 703 443 5155?: (7/10/2016 2:30pm)na umma yahya musa

????????????
????????
????
??
*GOYON* *KAKA*
*11*
Harhada kayansu sukayi a jaka,da gudu islam ta fice a gda gidansu hanne taje tararwa tayi innar hanne tana mata fada akan y kamata ta gyara halinta inba so takeyi ta rasa mijin aure a kauyen ba.
Sallama islam tayi tace hanne naxo nayi miki salama yau xamu koma birni gidansu babana ko nasaka ta na wala da yadda kowa y sakamin ido,innar hanne ce ta girgixa kai tace Allah y shiryaki islam to ina kudan yake balle romonsa da har xakice an saka miki ido,murguda baki islam tayi tace yanxu ke inna baki gani ba umh hanne xo muje gidansu ilah da yusufa nayi musu sallama,da sauri hanne ta tashi innarta tana kiranta kota kanta batabi ba suka fice.
A hanya hanne tace yanxu shikenan islam in kin tafi binni xaki manta damu ko,wata dariya islam tayi tace mai xaisa na mantaku kunefa abokanai na na hakika kuma ba ai Abba yace xamu naxuwa hutu washe baki hanne tayi tace Ashe nima wataran xani birni islam tace sosai a kofar gidan su ilah suka tarar da ilah da yusufa anan islam ta sanar dasu tafiyarsu birni suma basuji dadi ba suka dunguma suka tafi raka islam.
Acan bayan sun gama saka kaya a mota daddy yace to ina kuma islam din,kaka ce ta kama baki tace la'ilah ha illallah in ka bibiya ta tafi gidansu hanne yi musu sallama amma mu jirata.
Xaman jiran islam sukayi harna tsahon 10 minute amma shiru ba ita ba dallinta tsaki Aslam yayi yace amma yarinyar nan yar raunin wayoce in ba rainin hankali ba tasan jiranta mukeyi xata tafi yawo kaka ce ta hararesa tace to sai taki yiwa abokananta sallam...,bata karasa ba suka hango islam itada su hanne,Aslam yaja dogon tsaki yace saboda yarinya an batata wai har abokanai ne da ita maxa kaka ta hayayyako masa tace saika fadi waya batata kai wlh da badan islam tanason komawa birni ba kuma baxan iya bari ta tafi ita kadai ba wlh da ba inda xani,daddy ne yace hajiya dan Allah kiyi hakuri y kalli Aslam yace be carefull in ba haka ba kuma y girgixa kansa.
Islam ta karaso ta shiga mota daddy y bawa su hanne kowa 100 ganin da gaske islam tafiya xatayi suka hau ihu da kuka suna bin mota,islam itama ihu takeyi kaka ma harda goge kwallah??.

??????
*daga* *sisin* *mama*
??????
[11/12, 8:54 PM] ?+234 703 443 5155?: (7/10/2016 3:00pm)na umma yahya musa

????????????
????????
????
??
*GOYON* *KAKA*
*12*
Aslam ne yaji kukan islam yayi yawa kuma su Abba sunata rarrashinta taki yin shiru,tsawa y daka mata yace da Allah kiyiwa mutane shiru kin cikawa mutane kunne ke gaki mai kawaye ko,dago fuskarta tayi shabe-shabe da gawaye ta murguda masa baki tace to ina ruwanka in baxaka jiba ka toshe kunnanka da wanda ya tilasta maka dole kaji kukana xaro ido yayi yakai mata rankwa shi ta goce,daddy yace Aslam y kake wasa da rayuwarmu ne Aslam yace I'm sorry dad,sannan yace mamana rabu dashi kinji ta washe baki kamar ba ita take kuka ba tace toh.
Tunda suka tafi take surutu komai ta gani sai tayi magana na tambaya kuma ta tambayi Aslam ko kallanta bayayi sai tayi tsaki tace daddy ko Abba menene wannan saisu fada mata.
Aslam kuwa duk haushinta yakejin ganin yarinya karama tana shirin rainashi yadda kowa yake girmama shi a gdan amma yanxu xataxo da nata salon na daban murmushi yayi daya tuno da irin axabar da xaiyi mata har saitayi biyayya tsinto ihunta yayi ta kwalla kara tana yeah kiiiii yaja birki saura kadan y bugawa motar gabanshi dan ma Allah y nufa babu mota a bayansa da hatsarin da xasuyi ba kadan bane.
Kaka firgigit ta farka daga gyangyadin daya dauketa tana salati,su Abba ne suka kalli islam sukace ihun me kikeyi ko kinaso muyi hatsari mu mutu daddy yace kai Aslam kai kuma tunanin me kakeyi,kaka tace so yakeyi y kashemu kawai dama bai damu da rayukan muba.
Islam tace nifa tsoron wannan nakeyi gani nake in mun hau xamu fado,dariya Abba yayi yace islam rigima wannan fa gadace da ana fadowa ai da bakiga wasu motocin suna biba(nikuwa na kyalkyale da dariya nace kai aradu kauyanci baiyi ba yanxu hawa gadar takewa ihu haka????).
Aslam kuwa wani bakin cikine y turnike shi a ranshi yana watako ita duk iskancin nata ma tsoron mutuwa takeyi aikuwa xakici ubanki y figi motar,islam kuwa idanunta ta runtse sai da suka sauka akan gadar ta bude idonta.

??????
*daga* *sisin* *mama*
??????
[11/12, 8:54 PM] ?+234 703 443 5155?: (8/10/2016 4:00pm)na umma yahya musa

????????????
????????
????
??
*13*
*GOYON* *KAKA*
Tafiya sukeyi har suka karasa gda horn Aslam yayi gate man y wangale katon gate din gidan suna shiga yaran gdan suka taho da gudu harda taslem duk suka futo a motar wata mika islam tayi taja doguwar hamma ko rufe baki batayi ba,da sauri Aslam yadan bige bakin yace ba'a fada miki in anyi hamma ana rufe baki ba ihu ta kwala a firgice y juyo yace dan Allah kiyi hakuri yakai hannu y rufe mata baki,da yake ba wanda yaga time din daya bige bakin nata.
Shiru tayi taja tsaki ta murguda masa baki,kaka ta kalleta tace ke kuma ihun mene wannan kamar wadda tayi gamo cuna bakinta gaba tayi bata bata amsaba.
Su mommy da aunty amarya ne suka futo sukayiwa kaka sannu da xuwa har part dinta aka shigar da dukkan kayansu dayake an riga an share part din.
Bayan sun gaida kaka,islam kuwa hankalinta yana kan taslem yar 3 year tanata mata wasa,aunty amarya tace islam baki gammu bane ba gaisuwa murmushi tayi tace aunty amarya ina xuwa wasa nakewa taslem duk maganar da takeyi ko dago kanta batayi ba.
Girgixa kai aunty amarya tayi a ranta tace Allah y shirya,futa su mommy sukayi suka kawowa kaka abinci kala kala bayan sunci,islam ta mike ta shiga toilet fanfo takeson kunnawa ta kasa,saboda ba irin na kauyensu bane garin kici kici ta kunna shower kawai sai jin ruwa tayi y xubo mata ihu ta saka tana wayyo Allah na shiga uku.
Da gudu suka tashi sukayi bathroom din ganinta sukayi a tsaye jikinta sai rawa yakeyi ta rufe idonta sai ihu takeyi ruwa duk y jikata,Aslam da Amir dariya suka farayi ganin dalilin kukannata sauran yaranma duk suka dau ihu suna villager girl aunty amarya kuwa tsaki tayi ta koma mommy ce ta shiga bathroom din ta kashe shower din kayanta ta taimaka mata ta cire,sannan tayi mata wanka ta bata towel suka futo,mai ta shafa mata da powder sai kwalli islam tace mommy bakiyi min dige-dige ba,mommy tayi murmushi tace nan birnine ba'ayi ko kinaso a dinga ce miki yar kauye xumbura baki tayi tace niba yar kauye bace mommy tace ai dama bance miki yar kauye ba,islam tace to daxu daga ina ruwa y xubo naga ba a bude saman bandakin yake ba balle nayi xaton ruwan samane jan hannuna mommy tayi suka koma bandakin tace wannan shower sunanta wanka akeyi da ita dariya ta kyalkyale tace yasin birni yayi ta dada kyalkyalewa da dariya a haka suka futo yaran suna ganinta suka fara villager girl kugu ta kama ta joge kafa tana girgixa tace wace bulleja gal din wlh ni ba sa'arku bace sainayi muku tsinannen duka(nikuwa nace kaji turancin manya????).

??????
*daga* *sisin* *mama*
??????
[11/12, 8:55 PM] ?+234 703 443 5155?: (8/10/2016 4:30pm)na umma yahya musa
Chapter 4 · 0% Book details