← Book details Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 58

Sashe 30

Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karasawa tayi taja kujera 1 ta xauna ta kalli Aslam tace ina plate dinnawa kuma,wani banxan kallo y jefeta dashi yace yaje koyan gaisuwa,murmushi tayi har dimple dinta y lotsa tadan sosa kai tace au ina kwana,tsaki yayi yace daban kwana ba xaki ganni itama tsakin tayi tace naji mutum yace na gaisheshi,na gaisheshi kuma yana min iyayi,kallan mamaki yake mata yama kasa magana saboda y fahinci rainin hankalin islam yayi yawa ko yaushe da kalar wanda take kirkiro dashi,katse masa tunaninsa tayi ta hanyar cewa yaya nifa yunwa nakeji,harararta yayi yadanyi tsaki yace wlh in baki daina min rainin hankalinnan ba yanxu jikin ki xai fada miki in banda kin rainani ma ni kikeso natashi na dauko miki plate da cup din,kuma da kike cemin yunwa kikeji gaba abinci ba koni kikeso naxama abincin ciki,bude bakinta tayi tana kallansa da mamaki sai kuma tayi yar dariya tace tab to ai kai yaya ko abinci kaxama wlh babu mai cinka saboda sam baxakayi armashi ba ta karashe maganar da kyalkyalewa da dariya,shikuwa Aslam ji yayi wani tukukin bakin ciki y turnike shi ga wani Abu dayaji y tokare masa xuciya tunani y tafi wai meyasa yarinyar nan ta iya fadar bakaken maganganu masu ciwo ne can wata xuciyar tace ai kai kadai take fadawa maganganu son ranta,dafe kanshi yayi yace to meyasa ta rainani ne a iya sanina ko matasa sa'anni na shakkata sukeyi kallan kansa yayi yaga irin kirar da Allah yayi masa ta karfafan maxa kwafa kawai yayi y mike lokacin islam ta dawo rikeda plate da cup ganin y tashi tace yaya harka koshi,yace bansani ba y wuce daga kafadarta tayi ta murguda baki tace kada Allah yasa ka Sani din.

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*
??????
1/8/2017 10:20:46 AM: ?+49?174?6076805?: (30/11/2016 3:00pm) *na umma yahya musa*

????????????
????????
????
??
*GOYON KAKA*
*84*

Palo y karasa y dauki key din mota da wayoyinsa y fuce su Amira sunayi masa a dawo lfy ko amsa musu baiyi ba shiga motar shi yayi y fice direct gda yayi.

Islam kuwa xama tayi ta cika cikinta daganan ta koma palo selection suka saka na india suka kure home theater har bakin gate anajin karar suka har dirkar rawa baji ba gani,islam kuwa sai wani karye2 takeyi tamkar karina kapoor lol ??,saboda islam ba baya bace dama wajen rawa.

Islam kuwa yana xuwa direct part din mommy yace suka gaisa ta tambaye shi y islam,kanshi y sosa yace tananan lfy jiya tanata kuka wai kun tafi kun barta dakyar na lallameta tayi shiru,murmushi mommy tayi tace islam rigima dan Allah son ka rike islam amana nasan sai kayi hakuri saboda yanxu kuruciya na dibanta amma a hankali komai xai dai2 ta domin irin abinda ka horar dashi to dashi xata tashi dan haka ka koya mata dabi'u masu kyau jikinsa ne duk yayi sanyi,sannan dan Allah karka dinga takura mata kasan dai yarinya ce batasan komai akan rayuwar aure ba,cikin jin kunya yace toh mommy tace Allah yayi muku albarka yace ameen,tambayarta yayi yace daddy fa tace sun tafi kasuwa yace Allah y dawo dasu lfy,mommy tace ameen y tashi yace bari nakarasa gurin aunty na murmushi mommy tayi shikuma y tashi y futa.

Da sallama y shiga part din aunty amarya ta amsa masa sallama cikin farin ciki fuskarta dauke da murmushi da sauri y karasa y xauna a kusa da aunty y daura kanshi a kafadarta yace aunty ne barka da safiya cikin jin dadi ta shafa kanshi tace barkan mudai y gda,y angwanci dariya yayi yace aunty angwanci kuma (saboda tun tashin Aslam baya taba iya boyewa aunty amarya damuwarsa saboda itace abokiyar shawararsa) tace eh mana ko xubawa islam din ido kayi dariya yayi yadan shafi kansa yace haba aunty nawa islam din take nikam saina raineta ma nifa ina tunanin islam bama tasan menene aure ba,dan xungurinsa tayi tace au haka kake tunani ashema auran bashi da wani amfani tunda baxai yi maganin cutar taka ba tashi yayi yana dariya yace nifa aunty na gaskiya kunya nakeji banaso ta rainani y mike dariya itama aunty amarya tayi tace kujini da ja'irin yaro to kasata a gaba kana kallo tamkar t.v ficewa yayi a part din yana dariya part din kaka y wuce.

Xaune y tarar da ita tana kallan t.v da Sauri y karasa yayi hugging dinta yace uwar gda ran gda uwar gda sarautar mata,dariya kaka tayi tace ni cikani ja'iri,hade rai yayi yace Allah xan sakeki kika kara kirana da wannan sunan kinsan yanxu inada mata kuma in kika bari nayi xuciya to saina shekara 1 baki kara ganina ba,harararsa tayi tace toda yanxu wane y kiraka inka tashi tafiya kafi ruwa gudu kuma ma ai da tsohuwar xuma ake magani,yanxu naxata kasan kana da amaryar amma ka taho gurina,dariya yayi yace yar tsohuwar nan da kishi kike to maida wukar kinsan dai amaryata special 1 ce tsaki kaka tayi tace kaikasan abinda kake nufi,tashi yayi yana naga yau xuciyar ki a kusa take bari natafi kafin fadannaki yakai ga duka y fice.

Part din samarin gdan y wuce direct tsohon dakinsa y nufa saboda yasan safwan yana can a kwance y tarar da safwan yana bacci tashinshi y farayi,a hankali safwan yake bude idanuwanshi tarr y tsaidasu kan Aslam mikewa yayi y shiga bathroom yayo brush y futo.

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*
??????
1/8/2017 10:20:47 AM: ?+49?174?6076805?: (1/12/2016 2:00pm) *na umma yahya musa*

????????????
????????
????
??
*GOYON KAKA*
*85*

Safwan yana futowa daga bathroom y fara ango ango kasha kanshi kaga yadda kake kyallin angwanci kuwa,lallai daga ganinka jiya ka kashe arna irin wannan kyau haka y karashe maganar da dariyar shakiyanci,Aslam ne yayi tsaki yace dadina dakai wlh banxa ne wataran in xakayi magana sam baka taunata kawai fadar ta kake,dariya safwan yayi yace to menene acikin magana ta laifi,cikin kufula Aslam yace bkmai,safwan yace nifa yau xan koma dan harnaje na yanki ticket by 5 o'clock flight din xai tashi,Aslam yace OK nima next week xan dawo,cikin mamaki safwan yake kallanshi yace ammh amma da islam din xaka taho ko,wani kallan tara saura kwata Aslam yayiwa safwan yace eh tunda naxama na mamajo ba,dariya safwan yayi yace xaka iya xama hakan ma amma y xame maka dole ka taho da matarka tunda 1 month aka baka hutu,wani kallan banxa Aslam yayiwa safwan yace toh sannu daddy tunda har umarni kake bani,dariya safwan yayi yace ba haka nake nufi ba kasan dai akwai hakkokinta akanka idan ka tauye mata Allah xai iya tambayarka,siririn tsaki Aslam yaja yace ashe mai wa'axi ka xama to ai kamata a samo maka majalasi da loudspeaker kaka wa'axinnaka yafi armashi,murmushi safwan yayi yace to naji yanxu saika kaini nayi sallama da amarya tunda kaga xuwa 5 xan tafi may be nida dawowa garinnan sai kuma suna nan da 9 month,cikin jin haushi Aslam yace god forbid ace nixan hada jikina da banxar yarinyar i can't wlh,cikin mamaki safwan yace uhm uhm dai kar nan gaba kaxo kanamin karamar murya,murmushin gefen baki Aslam yayi wanda har dimple dinshi y loba yace wannan maganar taka shine babban kuskuren daxan tafka a rayuwa ta duk ranar dana xo maka da wannan maganar to ni Aslam na yadda kamin duk abinda kaga dama,to in banda abinka me xannema agurin yar tsakuwar nan ai sainaja tamin rainin dayafi wanda tamin yanxu (nikuwa nace anya Kuwa ??)dariya safwan yayi yace to naji taso dai muje gdannaka Aslam yace wlh sai 4 xanbar gdannan in kaga xaka iya jira fyn in baxaka iya jira ba ai ba dole,safwan yace to naji masifaffe gira daya Aslam y dage yace au sai yau ka sani sukayi dariya a tare daganan sukaci gaba da magana akana cigaban da Aslam yake samu a business din motoci da yakeyi,har safwan yake cewa shima yanaso y fara,Aslam yace ai hakan yana da kyau.

Su islam sai 2 suka kashe kidan sukayi sallah,suna idarwa suka futa surrounding din gdan flowers suka fara tsinka sai da suka cika dan kwalin khausar,mai kula da flowers din gdanne y gansu da saurinsa y karasa yana ku!Ku!!Ku!!,wannan wanne irin iskancine su islam ganin yadda y xaburo da sauri yanayi musu tsawa shine y sakasu runtuma ana kare,karasowa gurin flowers din yayi ganin irin ta'asar da sukayi shine y saka shi yin tsaki,yace wadannan kannan amaryar oga din daga ganinsu fitina xasuyi in banda tsabar rashin ji yaushe anyi Abu domin kawata gda amma suxo suna batawa,yayi kwafa yace tabbas dana kamasu yau to bakaramin bugu xanyi musu ba saboda yadda oga yakeson flowers dinnan nasan xaiji dadi haka yaci gaba da mita haryabar gurin.

Su islam kuwa suna shiga dakin sukace me xasuyi inba dariya ba,dariya sukeyi ba kakkautawa,islam ce ta tashi ta xura dankwalin Amira acikin ta, ta tura cikin gaba take kwaikwayon yadda kurtun sojan y ttumbulo ciki lokacin daya gansu a gurin flowers dariya suka dada tuntsirewa da ita daganan kuma suka fara wasa da flowers din da suka tsinko,cikin 10 minute suka canjawa palon fasali,sukayi kaca2 dashi sun tunkuda center table din palon yayi gefe sun cicciro pillows din kujerun sun tarwatsasu a palon garin wasan jefe2,sai da akayi kiran sallar la'asar sannan suka tashi a wasan sukayi sallah,islam ce tace kuxo muje mudan xagaya gdan haka suka fice bayan gdan ta kofar kitchen sukabar palon kaca2 dan ba abinda suka gyara.

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*
??????
??????
1/8/2017 10:20:48 AM: ?+49?174?6076805?: (1/12/2016 3:00pm) *na umma yahya musa*

????????????
????????
????
??
*GOYON KAKA*
*86*
Chapter 30 · 0% Book details