← Book details Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 58

Sashe 3

Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

????????????
????????
????
??
*GOYON* *KAKA*
*7*
Tun daga lokacin y daina daukarta in tayi laifi shine yake tsawata mata tsoronsa takeji sosai,har y tafi tana fara fitina in kaka tace ga aslam nan yanxu xata nutsu.
Aunty amarya ta kara haihuwar ihsan da tasleem ita kuwa mommy daga kan ameera haihuwar ta tsaya,su islam duk sunxo suna yanxu haka rabon islam da cikin kano tun haihuwar tasleem yanxu da take shekara 3 wannanne dalilin dayasa islam dawowa hannun kaka,yanxu islam tana makaranta a garin gwarxo tana aji 2 amma asha ruwan tsuntsaye takeyi yau taje gobe taki xuwa,sannan duk ranar da raje sai ta nemo magana bata kyale kowa ba daga malaman har daliban kaka kuwa daure mata gindin rashin mutunci takeyi duk laifin da islam tayi in akaxo aka fada mata sai ta bugi kirji tace bata aikata ba,makaranta ma tana xuwa allo dan an korosu itada kawarta hanne daga islamiyya ance basa fahimtar komai sai neman fada duk randa akayi hadda in basu iya ba aka dakesu indai yaro yayi musu dariya to dukan da xasu masa sai yafi wanda malami xai musu shine shugaban makarantar yace y gaji y mayar dasu gda,kaka da aka fada mata cewa tayi tafi nono fari dama me suke koyawa yara in banda xalunci kullum cikin dukan islam sukeyi tayi xamanta ta kaita makarantar allo wannan kenan.
*cigaban* *labari*
Islam tana futa bata xarce ko indaba sai gidansu hanne da guntun hawayenta hanne najin sallamarta ta futo da gudu tana waya dakeki islam bakinta ta cuna gaba tace ba wancan mugun yaya aslam din bane y rangwasheni hanne tace Allah y saka miki islam tace ai wlh dabadan yau xai tafi ba da saina rama dariya hanne tayi tace da munyi masa irinta uncle idris itama dariya islam tayi tace kuma shi da wlh a ruwan wanka xan xuba masa karara dariya sukayi gaba dayansu babar hanne tace Allah y shiryaku gidansu ilah da yusufa avokabansu suka je suka biya musu suka tafi kogi dayake yau ana kamun kifi kowa da fatsarshi a hannu.
Aslam kuwa tasha yaje y shiga mota ana kiran sallar magriba y isa gda direct part dinsu na samari y shiga dakine gado daya sai wardrop sai bathroom aciki wannan nasune shida ameer wanka yayi y futo y tafi masallaci sai da akayi sallar isha'i sannan y dawo direct cikin gda y shiga yaje y gaida maman sa take cemishi yau kwananka 3 fa harka dawo kai da kace sati xakayi a lokacin Abbansa da daddy (aliyu)suka shigo bayan y gaishesu yace wlh mommy dawowa nayi saboda kwata-kwata islam bataji gashi duk abinda takeso shi takeyi kaka bata tsawata mata anan y basu lbrn duk abinda y faru sannan,ran Abba y baci sosai yace dama inaso nasamu dama muje mu taho dasu gaba daya y kalli aslam yace karka damu insha Allah xasu dawo very soon aslam cikin farin ciki yace Allah y yarda,ya tashi yace xashi gurin aunty amarya su kuma suka xauna suna tattauna yadda xasu shawo hankalin kaka ta yadda ta biyosu.

??????
*daga* *sisin* *mama*
??????
[11/12, 8:54 PM] ?+234 703 443 5155?: (5/10/2016 2:30pm)na umma yahya musa

????????????
????????
????
??
*GOYON* *KAKA*
*8*
Da farin cikin shi y shiga part din aunty amarya a xaune y taradda ita ita dasu taslem y karasa y xauna a gefenta dora kanshi yayi akan cinyar aunty amarya,yace aunty na nayi missing dinki ina wuni,tace lfy my son i miss u too yayi dariya,kallan su taslem yayi y hararesu yace baku iya gaisuwa ba cikin rawar murya sukace ina wuni yaya lfy kawai yace,yace dallah can ku tashi ku bamu guri kun tsareni da ido naxoyin magana da aunty na da gudu ihsan ta tashi taslem kuwa kafadarta ta make dariya yayi yace kai aunty wlh yarinyar nan rashin jinta daya da islam itama dariya tayi tacewa taslem taho autata wlh wannan tafi islam jin magana yace aini xan baki lbrn rashin jinta yanxu fa ita ta koroni daga gwarxo ga kaka ta daure mata gindin rashin mutunci komai tayi daidai ne,shiru aunty amarya tayi tace to y xamuyi sai dai mu dinga binta da addu'a.
Aslam yace au ashe fa albishir naxo yi miki ai nasamo solution very soon islam xata dawo,murmushi ne y subucewa aunty amarya tace Allah yasa my son yace ameen y dade suna hira sai wajen 10:00pm yayi mata sallama y tafi part dinsu.
Islam baxaki tashi ba 7:30am fa tayi ko so kikeyi ki makara,kaka ce take tashin islam daga baccin safe saboda ta tafi makaranta,juyi tayi ta cuno karamin bakinta gaba tace wlh ni kaka baccinnan bai isheni ba,kaka tace ashe bakyaso ki xama mai lbrai a gidan radio ko da sauri islam ta mike dan dalilin dayasa take xuwa makaranta saboda tanaso taxama yar jarida shine babban burinta,amma da tuni ta daina xuwa wanka ta cire kayanta ta shiga,baccinta taci gaba dayi a toilet kaka ganin islam ta bata 15 minute bata futo ba shine yasaka ta bita a xaune ta tarar da ita akan kujera tana bacci tsaki kaka tayi tace wlh islam kedai anyi yarinyar banxa ta karasa ta sheka mata ruwa firgigit islam ta farka ihu ta kwala tana kururuwa kaka tace yimin shiru wlh yau in angle idris yayi miki dukan latti ba inda xanje,dariya naga islam ta tuntsire a raina nace mai kuka yana dariya,tace ba angle idris ba uncle idris ake cewa tsaki kaka tayi tace xancen banxa ai nayi kokari ma,amma menene tsakanina da yaran bokoko a wuta a haka kaka ta gamawa islam wankan suna fada.

??????
*daga* *sisin* *mama*
??????
[11/12, 8:54 PM] ?+234 703 443 5155?: (5/10/2016 3:00pm)na umma yahya musa

????????????
????????
????
??
*GOYON* *KAKA*
*9*
Sun fito daga toilet hanne dasu yusufa suka biyowa hanne mai ta shafa ta xauna sukaci abinci,ilah yace wlh wannan taliyar irinta gurin mai shayi dadinta y baci yusufa yace sosaima hanne kuwa lokacin da takai loma tace ai wlh saboda ita bana taba yadda nayi fada da islam,dariya islam tayi tace ba sunanta taliyar gurin mai shayi ba sunanta indomie ta karkatar da baki tace wannan mugun yayan nawa ne y kawomin ita dasu madara harsa biscuit da choculate wai na xuwa makaranta murmushi hanne tayi tace gaskiya y kyauta sai wajen 8:30am suka gama ci dan sunayi suna hira kaka harta gaji da magana islam ta shiga daki ta daukowa kowa chocolate da biscuit kaka kuma ta basu 20 naira sababbi sannan suka tafi.
A hanya hanne tace islam mu biya gonar malam tanimu islam tace a'ah ki bari mu dawo tukun tinda kinga munyi latti kar a dakemu nikuwa nace latti na yaushe basu suka karasa makaranta ba sai 9:00am dudu du tafiyar batafi ta 10 minute ba amma suka dinga canta sai data kaisu 30 minute islam tace yanxu muje mu haura ta katanga dan wlh baba mai gadi ko muna yawo da uwayen mu baxai barmu mu shiga ba yusufa yace haka xa'ayi daraf naga suna kama katanga sai ka rantse da Allah yan biraye ne sai da suka gama durawa Ashe wani fripect y gansu kuma dokar makarantar ce an hana shigowa ta Katanga.
Y kamasu sai office din head master akayiwa kowa bulala 5 masu xafi suka dinga kuka sannan aka sakasu neal down sai da sukayi na 30 minute sannan akace su tafi class aikuwa su islam sunsha takaici saboda basu samu sun siyi komai ba a break gashi an buga bell kowa y koma class.
Nan ma suna xuwa sabon mass teacher dinsu y shigo gashi ranar friday y bayar da assighment cikinsu ba wanda yayi nan y kuma futar dasu y sasu kamun kunne ranar dai su islam sunce da kafar hagu sukaxo makaranta nikuwa nace rashin jinsu??.
Gonar malam tanimu suka wuce sai da suka tsinko mangwaro 1 yahau kai islam tace ainice boss dan haka nixan dauka nan fa dambe y sarkesu har malam tanimu yaxo y kamesu yace gurin mai gari xai kaisu suka dinga bashi hakuri yace wlh sai y kaisu mai gari y musu tsakani.

??????
*daga* *sisin* *mama*
??????
[11/12, 8:54 PM] ?+234 703 443 5155?: (6/10/2016 2:00pm)na umma yahya musa
Chapter 3 · 0% Book details