← Book details Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 58

Sashe 28

Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Subhanallah Ashe kallo na cikin gdan wani kayataccen palo ne dauke da kayan more rayuwa babu abinda babu daga can gefe kuma wani hadadden dinning table ne akwai kofofi guda 4 1 kitchen ne mai dauke da store acikin shi shima irin fadar haduwar shi bata lokaci ne,sannan akwai store komai na kayan abinci akwai a ciki (Abba ne y xuba acewar shi gara yayiwa islam) kofofi biyu kuma bedroom da toilet acikin kowanne yana dauke da wasu hadaddun gado an mafa yan nigeria sunyi bala'in yin kyau domin in ba fada maka akayi ba saika xata yan wajene domin *hamra furnitures company* ba baya bane wajen kera gadaje tamkar yan waje to anan sukayi order su,dayar kuwa wata irin security door ce itace xata sadaka da stair daxai kaika xuwa sama gani nayi duk an tsalallake dakunannan an haura da islam sama shi kanshi stair din abin kallo ne saboda yadda aka kawata shi.

Y salam shine abinda na furta saboda tsaruwar palonnan ba karamin kyau yayi ba kujerune yan dubai dark & light purple sai t.v plasma touch screen akwai wasu manya manyan home theater akwai set light daga gefe kuma dispenser ce tareda wata katuwar show glass dauke dasu turaren wuta,humra kwalakca d.s ga sanyin a.c da daddadan kanshi dayake ratsa duk ilahirin jikina (nikuwa nace hmmmm lallai nan ake kira aljannar duniya garin dadi na nesa ungulu ta hango masai??)suma wasu hadaddun kofofine guda 3 a jere reras 1 naga an murna (wai saura kadan numfashina y dauke ??)wani tamfatsetsen gado nagani wanda y shanye kusurwa 1 ta dakin irin royal bed dinnanne tamkar na sarauniyar england kanshi shimfide yake da wani hadadden bedsheet pillows din dayake kai kuwa sunkai 10 kama da mai sweet mai triangle d.s wata tamfatsetsiyar wardrop ce wadda tsayinta y kusa tabo p.o.p din da akayiwa saman dakin ga wani hadadden mudubi da aka cikashi da kayan make up kai masha Allah gda yayi??,tsakiyar gadon nan aka ajiye islam ai saina ganta wata yar rutsut ??,har lokacin islam kuka takeyi tamkar ranta xai futa,su khausar aka kirawo mata ganinsu nema yadan saka ta daina kukan.

Islam na hango ta baje akan gadonta itada su amira ta war ware laffayar tayi gefe da ita suna ta hira harda kyakyata dariya tamkar ba itace take kuka daxuba,kiran sallar magruba akayi suka tashi suka je sukayo alwala suka futo watako shi kanshi bandakin an kashe masa dukiya lokacin kuma mutane suka fara watsewa gdan y xamana daga mommy saisu khausar dan aunty amarya ma ta tafi itada kaka islam ce ta fara raba ido tana y naji gdan shiru,murmushi mommy tayi tace ai sun tafi,islam ta shagwabe fuska tace mommy amma ku anan xaku kwana ko murmushi mommy tayi amma batayi magana ba.

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*
1/8/2017 10:20:41 AM: ?+49?174?6076805?: (26/11/2016 2:00pm) *na umma yahya musa*

????????????
????????
????
??
*GOYON KAKA*
*80*

Sai da akayi sallar isha'i mommy da kanta ta shiga bathroom ta hadawa islam ruwan wanka wanda yaji turaruka ta futo ta bude akwatin sleeping dress ta dauko mata wasu sleeping dress pink colour mai santsi riga da wando rigar kamar vest take wandon kuma gajere ne iya cinya,kallan su khausar tayi tace kuje palon kasa ku jirani xanyiwa islam magana in nagama saiku dawo to sukace suka futa,kallan islam mommy tayi tace my daughter dukkan abinda xai faru tsakaninki da son y xama sirri karki sake ki fadawa kowa kinji saboda tona sirri dayake tsakanin miji da mata haramunne islam tace toh dan batasan wani sirri akeson ta boye ba,mommy tace sannan ki dinga tsarki da ruwan dumi kidaina tsarki da ruwan sanyi kinji to islam tace mommy tace yauwa daughter na tashi kije kiyi wanka in kin futo wadannan kayan xaki saka,islam tace toh a gaban mommy ta cire kayanta ko kunya kokarin cire vest da under wear takeyi mommy tace a'ah my daughter ki daina cire kaya a gaban mutane yanxu kin girma,cikin jin kunya islam tasa hannunta ta rufe fuska ta dauki towel ta shiga bathroom mommy tanajin islam ta fara wanka tayi sauri taje ta tasa keyarsu Amira sukabar gdan dayake akwai driver dayake jiransu.

Aslam ne kwance a dakinsa safwan y shigo yana haba ango tun daxu an kaimaka amaryar ka y kamata ka shirya muje mu rakaka daganan musai bakin amarya,wani mugun kallo y jefi safwan dashi y doka wani uban tsaki y shige bathroom dariya safwan yayi y samu guri y xauna,20 minute Aslam y dauka y futo daure da towel yana tsane jikin shi da wani xama yayi a gaban dressing mirrow y shirya tsaf y taje kanshi da kwantaccen sajenshi bayan y saka singlet da boxwr y dauko wata arniyar shadda galila ash colour y dauka y saka y feshe jikinshi da turaruka masu dadin kanshi hula dara baka yasa sai takalmi mai danyatsa shima baki ba karamin kyau yayi ba dukkuwa da yanda fuskarsa take a tamke,wayoyinsa y dauka akan dressing mirrow da key din mota y kama hanya xai fice ko kallan safwan da amir baiyi ba,safwan ne yace ah haba ango tun daxu fa kai muke jira muyi maka rakiya amma naga kana shirin wucemu wani yatsina fuska Aslam yayi yace bana bukata ko ana dole yasa kai y fice.

Sallama yaje y yiwa iyayanshi sannan y kama hanya y tafi driving yakeyi amma ranshi duk a jagule,tsintar kanshi yayi da tsayawa gurin mai saida kaxa kulli 2 yasaka akayi masa y cillasu bayan mota y wuce,horn yakeyi a bakin gate din gdannashi cikin sauri gateman y bude yana sara masa yana ur wlcm sir dayake soja ne,direct packing space yaje yayi packing din motar.

Islam kuwa bayan ta futo a wanka gani tayi bataga su Amira ba,harta shagwabe fuska xatayi kuka xatayi kuka sai kuma ta tuna kila suna palo xama tayi gaban dressing mirrow ta shafa mai sai powder tadan xixara kwalli,tasaka lip stick ta mulke jikinta da humra mai mugun kanshi ta dada da body spray sannan ta saka sleeping dress din ta kama gashinta da ribon ganin irin kyawun da tayi da ai sai tahau tsalle da sauri ta saka wani takalmi sosa ta kwasa da gudu ta futo a dakin ganin bataga su khausar a palon ba tayi kasa wayam tagani basu khausar ba alamarsu tahau kwala musu kira khausar!Amira!mommy! Jin shiru ai saita hau kuka da gudu ta haura sama saboda tsoron da taji y kamata direct dakinta ta wuce ta fada kan gado tahau shashshekar kuka tana kiran sunansu.

Futowa yayi a motar bayan y dauko ledojin kajin daya siyo,cikin tafiyarsa ta xaratan maxa yake takunsa cikin kasaita harya karasa shiga palon,siririn tsaki yayi ganin yadda palon y kawata amma sai dai kash ba matar da xaiji dadin rayuwar auransa bace a gdan,bismillah yayi y sakawa kofar key y haura stair tun daga palo yakejin shashshekar kukanta cikin jin haushi da xafin xuciya yayi hanyar dakinnata tura kofar yayi da karfi a xafafe yace kukan uban me kike yiwa mutane sai kace gdan makoki,cikin raxana islam ta dago kanta ganin wanda yake tsaye shine y sakata yin tsaki,a ranta tana Allah y isa tsoron daya bata,ta komar da kanta kan pillow taci gaba da kiransu mommy tana kuka tsaki shima yayi a ransa yana xan gyara miki xamane,cilla mata kunshin kaxa 1 yayi yace gashinan in kinga dama kici yaja mata kofa.

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*
??????
1/8/2017 10:20:43 AM: ?+49?174?6076805?: (28/11/2016 11:00am) *na umma yahya musa*

????????????
????????
????
??
*GOYON KAKA*
*81*

Direct dakinshi y wuce xuciyarshi nayi masa tukukin ciwo,bude kofar yayi wow gaskiya shima dakinnashi y hadu exartly kayan gadon irinna dakin islam ne colour ne kawai y banbanta,cire hularshi yayi da ogogo da wayoyinsa y daurasu kan bedsite cabinet sannan y cire rigarshi y bude wardrop y sakaleta ajikin hanger y xamana dagashi sai singlate bakin gado y xauna tsaki yaja y dafe kanshi saboda baraxanar tarwatsewa da yakeyi saboda tsabar damuwa a ranshi yace gaskiya an cuceni y kamata a yanxu ace inacan inajin dadi irinna ko wanne ango ranar da amarya ta tare amma nisam abin ba haka yake ba saima dan karen damuwa da tamin yawa (nikuwa nace kai kaso ??) tsaki y karayi y kwanta kafafunshi na kasa fuskarshi na facing din p.o.p din dakin y tallafe kanshi da hannuwanshi biyu tunani y xurfafa sosai.

Can wata xuciyar tace masa haba Aslam alkawarin da kayiwa iyayenka kenan xaka rike islam amana,wannan itace amanar ace kaxo ka tarar yarinya na kuka koka lallameta alhalin kasan kuruciya na dibanta kuma tunda take yauce rana ta farko da xata kwana ita kadai a daki ka duba girman alkawari fa,daya xuciyar ce tace to ai na tsaneta banason ganinta sam,daya xuciyar tace dole ka sassauta kiyayyarta a xuciyarka saboda yanxu ita wani nauyi ce da Allah y daura maka,kuma tabbas xa'a tambayeka ranar lahira yaya katafi da hakkokinta na duniya,xuruf naga y mike kamar wanda aka tsikara y fice a dakinnasa dakin islam y tafi a hankali take tafiyar tamkar wadda wani Abu yake masa ciwo a ciki tura kofar yayi har lokacin tana kife akan pillow tana kuka a hankali y tura kofar dakinnata y dade tsaye a kanta,sannan y bude bakinsa yace ke kamar wanda bakin yakewa ciwo.
Chapter 28 · 0% Book details