← Book details Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 58

Sashe 20

Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safwanne yace daddy inada magana daddy yace munajinka,safwan yace Abba a xamanmu da Aslam baitabayin budurwa ba,tsantsar mamakine y lullube su Abba,safwan yaci gaba da magana yace saboda yace baxai taba iya yiwa yarinyar da yakeso kishiya ba dan tun ranar da aka haifeta yake dawainiya da dakon santa,cikin mamaki daddy yace wacce yarinya ce haka,safwan yace *islam* ce,cikin mamaki Amir y maimaita *islam*,safwan yace eh,daddy kuwa murmushin manya yayi yace yaro man kaxa,to amma shine y kasa fada safwan yace jira yake wai saitayi candy,shiru daddy yayi daya tuna dududu islam batafi 14 year ba.

Har wajen 10:00pm Aslam bai farkaba sanadiyyar allurar baccin da aka saka masa a drip,daddy ne y mike yace tomu bari mu tafi tunda bai farkaba,ku saiku xauna dashi amir yace toh daddy,suka futa.

Amir ne y kalli safwan yace abinda ka fada anya gaskiya ne,safwan yace eh kaima kayi mamaki ko,ai koni ba Karamin mamaki nayiba lokacin daya fadamin(ni kaina nayi bala'in mamaki ??).

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*

(14/11/2016 3:00pm) *na umma yahya musa*

????????????
????????
????
??

*GOYON KAKA*
*61*
Lokacin dasu daddy suka koma gda,a tsaitsaye suka tarar dasu aunty amarya a sarraunding din gdan,da sauri suke tambayar shi y jikin Aslam din da sauki sukace baccima yakeyi lokacin da suka taho,sai lokacin hankakin su aunty amarya y kwanta.

Daddy ne yace aliyu jeka kirawo hajiya tunda part dinta akwai mutane saiku taho palo na xamuyi magana toh Abba yace y karasa part din kaka y kirata suka taho.

Xaxxaune suke,kowa yana jiran yaji mai daddy xaice y kirasu a darennan da xai kasa tsayawa har gari y waye,daddy yayi gyaran murya yace dangane da abinda ya samu Aslam ne ba komai yake damunshi ba illah matsanancin ciwon ciki,anan yayi musu bayani dai2 da yadda dr y fada masa,sannan da xabin daya basu.

Kowa hankalinsa y tashi,musamman da yaji har ana shirin yi masa aiki,kaka tace to mai xai hana ayiwa mai sunan malam din aure,Abba ne y tari numfashin ta yace to ai hajiya wai Ashe islam yakeso shiyasa yakiyin aure dan baxai iya hadata da wata mace ba a matsayin kishiya.

Kaka,aunty amarya da mommy ba karamin mamaki sukayi ba,saboda a iya saninsu ba wani shiri tsakanin islam da Aslam kwata2 basa xama a inuwa daya,kakace tace shi Aslam dinne y fada muku haka,daddy yace eh abokinsa y fadawa amma yace wai jira yakeyi ta gama makaranta.

Murmushi kaka tayi tace ai shikenan,yanxu menene shawara,daddy yace jira nakeyi yaji sauki kawai y nemo wata matar y aura,dan inya tsaya jiran islam ciwon xaifi haka tsamari tinda dududu nawa islam din take,in akwai rabo a tsakaninsu ko bayan ta gama makarantar sai suyi aure,aunty amarya tace gaskiya.

Kaka ce tayi tsaki,tace naji xancen banxa koku da kuke tsofai2 daku wane y ajiye mata 2,ta kalli aunty amarya tace ke kuma da kika biye masa fadamin wadda acikinku takeda kishiya,to wlh yadda dukkanku bakuda kishiya haka kuma baxa'a iya islam kishiya ba,na yanke hukunci nanda 2 weeks a shirya aurawa Aslam islam kuma kankanta da kuke cewa yanxu mu a kauye sa'ar islam ai tanada da,dan haka na yanke shawara in akwai mai magana sai yayi,mommy tace hajiya hakan yayi Allah y sanya alkhairi,kaka tace ameen,aunty amarya kuwa shiru tayi tana tunanin wannan kwamacalar.

Daddy ne yace hajiya munji shawararki kuma mun amince Allah y sakawa auran albarka,amma inaso dan Allah kar wanda y fadawa Aslam ko islam xancen aurannan saboda inaso nayiwa Aslam baxata,kaka ta washe baki tace ai wannan mai saukine Allah yayi muku albarka sukace ameen daganan taron y watse.

Aunty amaryace sai juyi takeyi akan gado,saboda tausayin yarda to nawa ma islam take da xa'ayi mata aure,meta sani a cikin rayuwar nan da har in akayi mata aure xata iya kula da mijinta,Abba ne yaga takasa bacci yace wai fateema meya hanaki vaccine,cikin sanyin murya tace wlh Abbn Amir ina tunanin aurannan da xa'a yiwa islam,nawa islam din take da xa'ace xa'ayi mata aure,dan allah kaje ka lallaba hajiya ta janye kudirinta akan aurannan,dan ina tausayawa rayuwar islam,tashi Abba yayi yace haba fateema yanxu kina nufin kinfi hajiya son islam karki manta hajiya ta xabi ran kowa y baci akan ran islam y baci,ni a ganina kawai muyiwa hajiya biyayya dan bahaushe yace abinda babba y hango yaro ko y hau bishiyar rimi baxai hangoba,addu'a xabin alkhairi ita y kamata kiyi ba damuwa ba,sai aunty amarya taji dadi a ranta saboda duk maganar da Abba y fada gaskiya ne tace toh Allah y xaba abinda yafi alkhairi,Abba yace ameen ko kefa.

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*
??????.

(14/11/2016 3:30pm) *na umma yahya musa*

????????????
????????
????
??

*GOYON KAKA*
*62*

Sai 11:00pm Aslam y farka,a hankali y fara bude idonsa ganin dakin dayake shine y sakashi fara kallon dakin a hankali,Amir da safwan y gani a xaxxaune kallansu yayi yace meya kawoni nan,da sauri Amir y futa kiran limits safwan kuwa matsawa yayi,yana cemasa sannu y jikin,Aslam yace kaini fa bangane ba lokacin Amir suka shigo shida dr.

Matsawa jikin gadon dr yayi yace captain A.U Abdul kadeer y jikin Aslam yace ba inda yakemin ciwo sai rashin kwarin jiki,dr yace ai dama hakan xai faru yanxu ga magungunan da xaka shanan in kaci abinci cikin sanyin jiki Aslam y girgixa kai dr y futa.

Amir ne y mike yace bari naje gda na dauko tea flask da abinci yanxu nadawo,safwan yace toh,bayan futar Amir,Aslam y kalli safwan yace meya kawoni asibiti,safwan yace muma mun dawo daga gurin walimar su islam mukaxo muka tarar dakai a kwance a kasa ko numfashi bakayi,sai lokacin Aslam y tuno da matsanancin ciwon cikin daya turnike shi,cikin fargaba yace to su waye suka kawoni asibiti,safwan yace nida Amir,wata doguwar ajiyar xuciya Aslam yayi yace tnx god,safwan yace amma su Abba sun biyomu daga baya,dan su dr ma yayiwa bayanin abinda ke damunka,xaro dara2 idanunshi yayi gaba cikin kidima yace shikenan na kade har ganyena yanxu bani da dalilin da xan fada musu su kyaleni banyi aure ba harna kai 30 years,dariyar shakiyanci safwan yayi yace gashi dr yace in anaso ka rayu ayi maka aure a kurkusa,cikin kufula Aslam yace dayake shine da rayuwar tawa,shiru kowa yayi yana tunani a ransa,Aslam kuwa tunani yakeyi shi yanxu in ance y futo da mata y xaiyi don haryanxu baiga mace irin choice dinshi ba,after 20 minute Amir y dawo dauke da tea flask da food flask,tea kawai Aslam yasha saboda a yanda yakejin ransa ba abincin da xai iyaci,yana gama shan tea yasha magani y kwanta bawai don baccin yakeji ba,sai don kawai yanaso y samu sassauci a ranshi.

Washe gari,daddy,Abba,kaka,mommy,aunty amarya sukaxo duba shi,sun masa y jiki yace da sauki,kaka cikin xaulaya tace nida harna tanadi geron gumba,sai kuma naji ka tashi,kowa dariya yayi a dakin,Aslam kuwa yake kawai yakeyi don yana tsoron hukuncin da daddy xai yanke masa,sai 12:00pm sannan su mommy suka tashi tafiya don su Abba sun dade da tafiya kasuwa,Amir ne y tafi mayar dasu.

Misalin 2:00pm Amira ce ta shigo tace sis ki taso xamuje asibiti kaiwa su yaya Aslam abinci daganan mu duba jikinshi,tsaki islam tayi ta gyara kwanciya tace wlh baxani ba,ke bari kiji indai har sainaje duba hero xai warke to wlh sai dai yayita fama da jinya,tsaki Amira tayi tace kada Allah yasa kijedin ta fice suka tafi dayake yaya haidar ne xai kaisu.

Yau kwanan Aslam 3 a asibiti,amma ko sau 1 islam bata tabayin tunanin xuwa ba,yauma xaune take tana game a t.v kaka ta futo xata tafi asibitin tace islam taso muje kema yau ki duba mai sunan malam,islam ta yatsine fuska tace ash kaka Allah kaina yake ciwo,kaka tace amma kike wannan latse2 islam ta tashi ta kashe game din tace kwanciya xanje nayi tai shigewarta daki,tana cewa Allah y kiyaye naje duba mugunnan.

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*
??????

[11/16, 5:02 PM] ??????Salma??????: (16/11/2016 1:00pm) *na umma yahya musa*

????????????
????????
????
??
*GOYON KAKA*
*63*

Kaka suna futowa sukayi clashing dasu Aslam an sallamosu,kaka ce ta karasa tana washe baki tace gawa taki rami,tunda kace dai baxamuci gumbar nan ba dole na fitar da geron na bayar sadaka,tunda wanda na ajiye dominsa y mike,dariya safwan yayi yace kuma kaka wlh dama na dade banci gumba ba,wani mugun kallo Aslam y jefeshi dashi,Amir kuwa murmushi yayi saboda dama shi bamai yawan magana bane,part dinsu suka wuce kaka ma ta wuce nata.

Bayan sun shiga bedroom din Aslam,bandaki Aslam y shiga yayi wanka bayan y futo y shirya safwan ma y shiga abinci aka kawo musu bayan sun gamaci,aunty amarya da mommy sunxo sun dada duba jikin Aslam,haka yaran gdan sunata shigowa har tasleem amma ba islam ba alamarta.

Cikin xaulaya safwan yace abokina nifa banga jerry dinka taxo dibiya ba dukkuwa da safa da marwan da yaran gdannan sukeyi,Aslam ne y daga gira daya yace so what,dama banaso taxo dannasan in taxo ba alkhairi ne xai kawota ba,shiru safwan yayi yana jadda irin taurin xuciya irinna islam,ace gata yar karamar yarinya amma kwata2 batasan yafiya ba,Aslam ne y katse masa tunaninsa ta hanyar magana yace wlh ni babban abinda nake tsoro bai wuce irin hukuncin dasu daddy xasu yankemin ba,dan tunda kaji sunyi shiru to Allah ne kadai yasan abinda suke kullawa,murmushi safwan yayi yace karka damu abookina insha Allah duk hukuncin da xasu yanke baxai maka tsauri ba,Aslam yace Allah yasa,safwan yace ameen daganan sukaci gaba da hira.
Chapter 20 · 0% Book details