← Book details Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 58

Sashe 27

Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasu yan matane da suke xaune,dayar tace nifa wlh kawata nayi mamakin matar captain a.u dan Allah jibeta ko kirgen dangi bata fara ba,tsaki dakyar tayi tace inajin fari da gashinne y rudeshi,dayar ta tabe baki tace ainaji ance auran xumunci ne cousin dinsa ce,dakyar ta kuma cewa koda naji mana amma ace yana babban yaro haka ba kayan hutawa ajikin matarsa ina jin xan gwada sa'ata,dayar tace ina bayanki kawata Allah y baki sa'a,tayi wani farrr da idanunta tamkar na kwarkwata tace ameen.

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*
??????

1/8/2017 10:20:40 AM: ?+49?174?6076805?: (25/11/2016 1:00pm) *na umma yahya musa*

????????????
????????
????
??
*GOYON KAKA*
*77*

Haka akaci gaba da hidimar biki,anci ansha save ur save ne kowa abinda yakeso yake diba,ba irin kayan more rayuwa da babu kama danaci nasha,can nagano xugar fans din *goyon kaka* sun xage suna kwasar gara.??

An bukaci amarya da ango su futo filin rawa,kicin2 islam tayi da fuska ta xumbura baki gaba,Aslam ne y matsar da bakinshi dai2 kunnanta yace y yan matana xaki tashine ko saina daukeki,da sauri ta daga kai ta kalleshi kashe mata ido daya yayi yace eh maimaita abinda y faru daxu xanyi ai islam batasan lokacin data mike ba,murmushin gefen baki Aslam yayi yana kada kai yana jifan islam da wani shu'umin kallo dana kasa fassarashi,tashi sukayi a hankali suke takawa ji islam tayi Aslam y rige hannunta itadai banxa tayi masa,a ranta tana cewa jarababbe gobennan xamu rabu sai dai ka tare da wata matar a haka suka karasa filin rawa dukkaninsu a tsaye suke kikam babu mai dan wani juyawa nan fa yan'uwa da abokanan arxiki sukaxo aka fara barin nerori (nikuwa nace bidiri watako masu kudi ba ruwansu da buhariyyar nan??) sagir shima tasowa yayi yaxo y fara musu liki islam cikin tsan2 mamaki take kallanshi jikinta duk yayi sanyi shima sanye yake da ankon maxa blue din shadda da hula red,saikuma tayi rau2 da ido tanason yin kuka.

Aslam ganin yanayin da islam ta shiga yayin dataga sagir tuni yaji ranshi y baci xuciyarshi tana masa xafi saboda tsaf y ganeshi cikin xafin nama y danki hannun islam suka juya suka bar filin rawar.

Xaune suke a gurin da aka tanadar musu Aslam yace me wannan banxan yakeyi a gurinnan ubanwa y gayyace shi,wani shekeke islam ta kalleshi tace sainaji matsa tukunna xan amsa maka ta karashe maganar da murguda karamin bakinta,wani shu'umin murmushi Aslam yayi yace ina tausaya miki yarinyar nan dan duk lokacin dana dankeki baxakiji dadi ba,murmushi itama islam tayi tace mudai tausayawa juna domin kasan game dinnamu bama taba tashi 1-0 sai dai duro,cikin tsantsan mamaki yake kallanta har xaiyi magana sai yaji m.c na sanarwar yanxu amarya da ango xasu yanka cake kwafa yayi suka mike a tare.

Suna karasawa gurin wani hadadden cake kalanshi white & pink aka basu wuka aka kirga number 1,2,3 sannan suka yanka cake din ko wannensu fuska a tamke Aslam ne y fara dauka y sakawa islam a baki sannan y bata lemo tuni aka dauki tafi raf3,murmushi islam tayi a ranta tace xaka Sani itama ta dauko wani katon cake Aslam ganin sai y rankwafo islam xata samu damar saka masa cake din a baki shine kawai y sashi yanke hukuncin dagata cak,islam bata ankara ba sai jinta tayi a sama,Aslam y jefeta da wani murmushi dana rasa gane ma'anarsa itama mayar masa tayi y bude bakin kawai saiji yayi ta danna masa wani katon cake dayafi karfin bakinshi da hanxari y dureta saboda yadda yaji y kasa tauna cake din,tuni gurin y dauki sowa da tafi ji kake raf3,islam kuwa data fakaici idon mutane saitayi masa gwalo,wani malolon bakin ciki Aslam yaji y turnike shi.

11 o'clock taron y tashi kowa yana cikin farin ciki anyi rabon sevoniers sosai,safwan ne y mayar dasu islam gda yano to amaryarmu Allah y tashemu lfy,itadai banxa tayi masa saboda bacci takeji tayi shigewarta part din mommy.

Aslam kuwa suna shiga part dinsu kayansa y cire y fada wanka saboda yadda daddadan kamshin islam y dameshi saboda daukarta da yayi.

Harya futo wankan baidaina jin kanshin ba tsaki yayi yace wanne irin mayan turare ne haka,kwanciya yayi y lumshe ido dukkuwa daba bacci yakeyi ba kawai hirar dasu safwan sukeyi ce ta isheshi,safwan ne yace kai abokina wlh kalar soyayyarku kai da islam ta burgeni kaga wani kallan luv da kuke jifan juna dashi,banxa Aslam yayiwa safwan saboda yasan safwan soyakeyi y tanka masa,safwan jin Aslam yayi masa shiru yasa shi cigaba da maganarsa yana kai abokina bafa karamin burge mutanen gurinnan akayi ba yadda cikin xafin nama ka daga islam cake Tamkar ka dau... bai karasa ba Aslam y taso cikin karaji yana is enough nagaji dajin banxan surutunnan naka to innayi mata kallan luv laifine ko inna dauketa haramunne naga mata tace plx don't disturbing me again wata dariyar shakiyanci safwan y saka yace haka nake sonji angon islam cikin kufula Aslam y juyo da niyyar naushin safwan lokacin su safwan harsun kai kofa tashi Aslam yayi yaje y sakawa kofar key.

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*
??????
1/8/2017 10:20:40 AM: ?+49?174?6076805?: (25/11/2016 3:00pm) *na umma yahya musa*

????????????
????????
????
??
*GOYON KAKA*
*78*

Yau y kama wuni shima anyi hidima sosai 4 o'clock aka fara shirin kai amarya,cikin tashin hankali islam ta tafi wajen mommy tana xuwa ta fada kan cinyarta kuka takeyi sosai tamkar wadda ake shirin xarewa rai,cikin tashin hankali mommy tace lfy islam meya faru kuma,cikin ganshekar kuka islam tace mommy bake kika cemin in yadda akarasa hidimar biki ba xakisa hero y sakeni saboda bashi nakeso ba ta dada barkewa da kuka,murmushi mommy tayi domin ita harta manta sunyi wannan maganar da islam a ranta tace yaro man kaxa in banda kuruciya na dibar islam yaushe xataxo gurin uwar yaro tace kuma batason danta,shafa kanta mommy ta farayi a hankali ta fara fada mata maganganu masu dadi,tace haba my daughter yanxu y xa'ayi na manta da plan din mu ai ina sane yanxu idan nasaka y sakeki kowa xai iyajin haushina amma ki bari muyi abin cikin tsari ki bari saikin tare koyaya ya musguna miki saiki fadamin kinga da wannan xan kafa hujja dole y sakeki,cikin jin dadi islam ta dago rinannun idanuwan tayi murmushi ta koma ta lafe ajikin mommy,mommy tace yauwa daughter na tashi muje ki shirya kar a jiraki,islam ta mike tace yauwa mommy amma tare dasu Amira xamu xauna a gdan ko murmushi mommy tayi tace islam rigima ta ina kika tabajin ranar da aka kai amarya an hadata da yan xaman daki,ki bari bayan kin tare da sati 1 sai suxo kuyita xama,xumbura baki islam tayi.

Cikin wani xadadden lace pink colour mai flowers da stones ajikin flowers din sai kyalkyali yake mommy ta shirya islam sannan aka nada mata wata laffaya fara da flowers pink itama da stones ajiki bakaramin kyau islam tayi ba,mommy da kanta ta kama hannun islam suka tafi part din daddy inda acan xa'ayi musu fada itada Aslam,fuskarta a bude suka shiga part din daddy (nikuwa nace islam ba ta ido??).

Ba karamin nasiha akayi musu ba da jan hankali akan xaman aure sannan su kasance masu sauke hakkin junansu daya rataya a wuyansu,su xama masu hakuri domin hakuri shine gishirin xaman duniya baki daya,islam kuwa ko a jikinta illah ma tunani data tafi tace hakkin miji to gashi ni ban iya girki ba tace tab y xa'ayi kenan,sai kuma tace hakuri tab ai wlh in yamin Abu ramawa xanyi domin baxan bari y rainani ba ta karashe tunaninta da muguda baki (nikuwa nace tafa)Abba ne y kira sunanta islam firgigit tadawo daga tunanin data tafi yace kina jina yi nayi bari nabari ko kadan karnaji ko karna gani ance kin sabawa mijinki idan naji kona gani bakaramin saba miki xanyi ba,shagwabe fuska tayi ta tura baki tace to wai Abba ni kadai xan bishine shi baxai biniba naga duk ni kadai akewa fada,ai dariya ce taso kufce musu saboda shirmen da islam tayi lallai sun tabbatar da akwai kuruciya a tattare da islam,Aslam kuwa wani haushi ne y turnike shi watako ita batasan ma hakkin miji akan mata ba shifa dabadan hadin iyaye bane dayace an cuceshi,saboda kwata2 islam baxata iya masa maganin cutar da take damunsa ba,to ta inama yarinyar da kwata2 batasan menene auran bama tsaki yadanyi,daddy yadanyi murmushi yace mamana kenan ai kece a karkashin sa kinga kuwa dole ace kiyi masa biyayya ku tashi Allah yayi muku albarka,islam fa sai lokacin ta fara raba idanuwa ganin da gaske ake wai yau ba'a gdansu xata kwana ba,kawai saita hau ihu ta rungume kaka tana ita wlh ba inda xataje sai lokacin suma mommy aunty amarya kaka suka fara hawaye ganin irin ihun da islam takeyi,su kuwa lokacin su khausar sun dade a gdan amarya,da kyar aka saka islam a mota dayake hardasu mommy xa'a kaita,nikuwa saina ce Allah y kiyaye y bada xaman lfy.

To jama'a ko wanne irin xama xa'ayi tsakanin islam da hero kudai ci gaba da biyoni ni *umma yahya musa* dannaci gaba da nishadantar daku ??

*plz ku tayani da addu'a akan wata bukatata Allah y biyamun da dukkan musulmai baki daya ameen*

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*
??????
1/8/2017 10:20:42 AM: ?+49?174?6076805?: (26/11/2016 1:00pm) *na umma yahya musa*

????????????
????????
????
??
*GOYON KAKA*
*79*

A mota ma islam sai gunjin kuka takeyi su mommy sunyi2 da ita tayi shiru taki har suka hakura,gdan ta dayake nassarawa g.r.a aka kaita gda ne ginin tsarin turawa tun daga compound din abin kallo ne domin kwaltace a shinfide tun daga bakin gate har xuwa inda xai sadaka da packing space daga gefe kuma grass carpet ne shinfide da wasu flowers masu kyau da kanshi akwai garden a gdan da yake dauke da shuke2 kama dasu mango,guaver,apple,ruman d.s sannan akwai sweemin pool tun daga waje gdan abin kallo ne (nidai nan na saki baki da hanci ina kashe kwarkwatar idona)
Chapter 27 · 0% Book details