← Book details Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 58

Sashe 2

Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

????????????
????????
????
??
*4*
A lokacin y kira Aliyu dan yayi masa rakiya unguwar rijiyar xaki yaga sun nufa wani tamfatsetsen gida yaga y nufa dashi a machine din yaya Abdul sukaje a aljihunsa yaga y futo da key y bude gidan mamakine y kama Aliyu kasa boye mamakinsa yayi yace yaya gidan wane,murmushi Abdul yayi yace mushiga tukun shiga sukayi kowanne part an kawata shi da kayan xamani masu bala'in kyau cikin fara'a Aliyu yace yaya naga gida kuma yayi amma ina son karin bayani inji gidan wane,dariyar shima Abdul yayi yace gidanmu ne cikin mamaki Aliyu yake kallan Abdul yace eh namune rimarmu nake tarawa da tayi yawa shine nayi tunanin mai y kamata nayi shine naga y dace kawai na gina mana gda tunda kaima kaga ka isa ajiye iyali,kaga y nuna masa manyan yace wannan daya naka daya nawa,waccan na umma waccan dayan kuwa na yaranmu maxa da xamu haifa in Allah y kawo, farin cikine y lullube Aliyu y rungume yayansa Abdul harda kukansa yace ngd ngd ngd yaya Allah yabar xumunci Abdul yace ameen sai da suka koma sannan Abdul yake fadawa khadija itama taji dadi tayi fatan alkhairi kallan Aliyu tayi tace kanina saura mata ko kuma inaji ni xan samo maka dannaga kamar kanin nawa tsoron mata yake,dariya Abdul yayi yace haba aunty na waya fada miki amma dai nabaki xabi tunda haka kikace,dariya tayi tace xancena gaskiya ne kenan yace eh naji,Abdul shima dariyar yayi.
Da suka je gaida umma a wannan satin Abdul yake fada mata itama tayi farin ciki,Abdul yace umma yanxu haka ma nayo mana order motoci basu karaso bane,tace lallai kaxama magajin malam Allah y kara hade kawunan ku y albarkanci dukiyarku sukace ameen.
Abdul yace yanxu umma yaushe xaki koma can gidan murmushi tayi tace da ace malam yaso xamana a birni daya kaini tun yana da rai da y kaini birni,amma tunda bai kaini ba yanxu ba avinda xai kaini birni xama ina muku dai fatan alkhairi Allah yasa ashiga a sa'a,sukace ameen duk yadda sukaso su shawo kanta ta yadda ta koma firr taki haka suka hakura.
Aliyu yace yanxu yaushe xamu tare murmushi Abdul yayi yace ba yanxu ba ka bari sai nan da xuwa khadija ta haihu kafinnan ka samu mata aliyu yace toh umma tace Allah y raba lfy sukace ameen.

*I* *luv* *u* *all* *my* *fans*

??????
*daga* *sisin* *mama*
??????
[11/12, 8:53 PM] ?+234 703 443 5155?: (3/10/2016 4:00pm)na umma yahya musa

????????????
????????
????
??
*GOYON* *KAKA*
*5*
Ha suka gama xaman ranar duk yadda sukaso su shawo kan umma a'i ta yadda taki haka suka dawo,lokacin da Abdul y fadawa Khadija itama bataji dadi ba.
Cikin ikon Allah akwai wata yarinya fateema da take shigowa take taya khadija aiki kamar wasa khadija tayi mata xancen Aliyu,ta nuna kunya a lokacin,khadija da Abdul da Aliyu ne suke xaune Khadija tace kanina nifa nayi maka mata yarinyar kuma wlh tana da hankali kuma ga kyau saboda bafulatana ce,dariya Aliyu yayi yace kai aunty na wa kika samomin itama murmushi tayi tace Fateema ce yarinyar da take shigowa,Abdul yace gaskiya kinyi tunani dan yarinyar akwai hankali,Aliyu yace toh shikenan Allah y xaba mana abinda yafi alkhairi,sukace ameen.
Cikin ikon Allah Aliyu da fateema sun daidaita tsakaninsu soyayya sukeyi mai tsafta cikin wata uku aka kammata komai aka saka rana 2 months masu xuwa,a lokacin saura 1 months khadija ta haihu.
Cikin ikon Allah wata 1 da saka rana khadija ta haifo santalelen yaronta mai kama da babansa sak tamkar kaki yayi ranar suna yaro yaci sunan kakan shi umar suke kiranshi da (aslam)aslam y taso cikin gata kowa yana nuna masa soyayya.
Bayan haihuwarsa da 2 weeks khadija ta tare a sabon gidan sai lokacin umma a'i taxo barka da ganin gda saboda acewarta jikan fari sannan kuma dan yaronta na farko kwananta 2 ta koma shima dakyar takai da 1 tayi tace xata tafi.
Bayan sati 2 akayi bikin Aliyu xaman lfy sukeyi da matarsa tana masa ladabi da biyayya suna xaman lfy da khadija da take cewa momyn aslam yanxu,ita kuma tace auntyn aslam saboda a gurinta yake wuni sai dai in yana kuka take kai mata shi ta bashi nono in yasha ta koma dashi sai bacci kuma.
Lokacin da Aliyu y gama makarantarshi shima kasuwancin yaci gaba dayi.

??????
*daga* *sisin* *mama*
??????
[11/12, 8:53 PM] ?+234 703 443 5155?: (3/10/2016 4:30pm)na umma yahya musa

????????????
????????
????
??
*GOYON* *KAKA*
*6*
Cikin ikon Allah kasuwancinsu y kara karfafa lokacin arxikinsu y kara bunkasa.
Fateema ma ta samu ciki kula khadija take bata ta musamman har cikinta y isa haihuwa ta haifi na miji aka saka masa sunan yayan Aliyu wayako Abdul qadeer (ameer)haka sukaci gaba da haihuwa inda aslam nada shekara 2 khadeeja ta khadeeja ta kara haihuwa ta haifi namiji aka saka masa Aliyu suke kiransa (Haidar).
Cikin ikon Allah khadeeja tana da yaya 5 duk maxa aslam,haidar,sadiq,khaleefa,usman.
Fateema kuma tana da yaya 3 itama duk maxa ameer,yusuf,khaleefa ,har yau basu samu mace ba burin yaran gidannan y ta'allaka akan su samu kanwa sannan suna girmama tsakaninsu,cikin ikon Allah fateema ta samu ciki yana da wata 2 khadeeja ma ta samu duk ilahirin yarannan addu'a sukeyi Allah yasa babanninsu su haifa musu yan mata.
Cikin ikon Allah fateema ta tashi da nakuda aka kaita asibiti bata dauki lokaci ba ta haifo xankadediyar yarinyar ta mai kamata babanta sak sai dai kawai hasken mamarta ta dauko,murna kuwa gurin iyalan gdan ba'a cewa komai.
Ranar suna aka sakawa yarinya Aysha aslam yace (Islam) xa'a na cemata tun daga lokacin rainon islam y dawo daga makaranta y dauketa ba wanda y isa y karbrta babban abinda yake sakawa aslam y kai islam gurin mamanta shine kuka in tana kuka batasan lallashi ba shine yake hadasu fada,tun lokacin da aka haifi islam kaka ta roki alfarmar tanaso Aliyu y bata ita inta isa yaye tun daga lokacin y amince yaxo y fadawa fateema itama tace ba komai tunda y yarda godiya yayi mata sosai.
Islam nada wata 2 mommy ta haihu itama mace ta haifa aka saka mata zainab sunan maman mommy amer yace shima ameera xa'a saka mata haka kuwa sukece mata ameera akwai hakuri dan in amer y daukota sai aslam yaje y dauko islam amma shi sai y mayar da ita saboda kuka yayita jin haushi kuwa.
Kwanci tashi babu wuya su islam sunyi 2 years a lokacin aslam nada 14 years dan yana j.s 3 wata rana y dawo daga makaranta yaxo y tarar an dauki islam an kaita gwarxo ranar wuni yayi yana kuka ko abinci bai ciba ranar.
Islam acan ma kuka take tanata gwarancin neman yaya dakyar kaka ta lallabeta tayi bacci,satin islam 2 ta ware shikuwa aslam ganin da iyayenshi sukayi damuwa tayi masa yawa yasa suka tattara shi suka mayar dashi boarding skul y koma s.s 1 tun daga nan rayuwa taci gaba da tafiya.
Wani hutu y dawo da murnarshi ya shirya y tafi gwarxo amma lokacin da yaje y tarar islam tanata birgima tana ihu duk ta watsar da abincin tsawa y daka mata tundaga lokacin ta fara tsoronsa harya dawo bata yadda y dauketa inya dauketa kuwa tadinga ihu kenan har saiya sauketa.

??????
*daga* *sisin* *mama*
??????
[11/12, 8:53 PM] ?+234 703 443 5155?: (4/10/2016 2:00pm)na umma yahya musa
Chapter 2 · 0% Book details