← Book details Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 58

Sashe 34

Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaka ce tace to yar dadi miji baxaki sakko daga cinyar tashi ba kika wani dane cinyar miji ko kunya ta bakyaji,Aslam ne yace naji tsohuwar nan da iyayi to ina ruwanki koma metayi mini kema fa mijinta kikace ba wani ba ke wama yasan irin tabarar da kika yiwa naki mijin dan inaga kinada 9 years akayi miki aure,islam ce ta kyalkyale da dariya tace Allah my prince kaka tana 9 years akayi mata aure,wani dadi Aslam yaji a ransa jin irin sunan da islam ta kirashi dashi,yace eh mana islam tace tab wayaga gwida yara,a tare suka kyalkyale da dariya Aslam da islam,kaka ma dariya tayi tace naji ja'iran yara kun tasani gaba kunamin shakiyanci sai a lokacin islam ta sakko daga cinyar Aslam tace eyya kaka ta ba wani shakiyanci abinne da ban dariya kina fa 9 years kaka ce tace oho muku dai,sai lokacin suka gaidata ta amsa mika mata ledar dinta da sukayo mata shopping atamfa 1,turare1 sai sabulu cikin jin dadi ta karba tayi godiya tana saka musu albarka Aslam ne y tashi yace my princess xomuje part din su mommy tace toh ta mike hannunsu sakale cikin na juna suka fuce,kaka kuwa tsantsan farin cikin datake ciki yaki boyuwa tace ai dama nafada ana auradda yarannan xasu shirya gashi kuwa nagani da kaina ta tashi tahau rawar murna.

Su Aslam kuwa suna futa,Aslam yace yayi kyau aljanar kaka kinaso wasanna mu yayi kyau,murguda masa baki kawai tayi yace kin manta matsar da nayiwa bakinki daxu ko,da sauri tasa dayan hannunta ta tamke bakin,dariya yadanyi mai sauti a haka suka karasa part din mommy suka gaidata itada daddy dayake yau sonday basu futa kasuwa da wuri ba,suma sun basu tsarabarsu sunji dadi sun saka musu albarka daddy ne y kalli islam yace my daughter dftn dai xaman naku babu wata matsala,murmushi tayi sai data kalli Aslam taga shima ita yake kallo tace,dammm kirjin Aslam y buga,lfy qlau dady,wata ajiyar xuciya Aslam yayi har sai da daddy y kalleshi,da sauri y sunkuyar da kansa,daddy yace da gaske kike daughter bayayi miki komai tace eh daddy kanta a kasa,yace to Allah yayi muku albarka sukace ameen suka tashi,part din aunty amarya suka shiga suma sunji dadin ganinsu bayan sun gaisa Abba yace son dftn dai bata baka matsala a xamannaku,Aslam ne y sunkuyar da kansa yace eh daddy muna xaune lfy tanamin abinda nakeso,murmushi Abba yayi yace to Allah yayi muku albarka y baku yaya da xasuyi muku biyayya,cikin jin kunya Aslam yace ameen nan ma suka ajiye musu tsaraba suka koma part din kaka.

Islam ce tace kaka ina Amira ne,kaka ce ta karkata baki tace kinsan kasace ita tana daki tana bacci mikewa Islam tayi ta cire after dress din jikinta,tace bari naje na tasota,kaka kuwa ruke baki tayi tace yanxu islam xaku futo ma baxaki iya saka kaya na mutunci ba,islam ce tana tafiya tace to kaka menene aibun kayannan,kallan Aslam tayi tace ai laifin kane da kana gani tasaka kayan baka hanata ba,murmushi yayi yace kaka ai sam2 banason bacin ran islam dan haka abinda takeso takeyi y kwantar da kanshi a kujera y lumshe ido kaka ce tayi tsaki tace Allah y kyauta.

Islam kuwa tana shiga dakin kan gado ta haye ta janye blanket ta dakawa Amira duka firgigit Amira ta farka a baccin da take,ganin islam ce ta tashe ta da sauri ta rungume ta,tana oyoyo 6 yaushe kikaxo,islam tace ban sani ba kedai ba kinanan kina bacci ba,Amira tace haba 6 bama haka dake fa,islam tadan yatsina fuska tace daxu ta tashi tana ki sameni a palo ta futa Amira kuma ta shiga bathroom.

Haka su islam suka wuni a gda Aslam sai nan2 yakeyi da ita kamar gaske itama tasaki jikin ta,da akaxo cin abinci firr Aslam y dage shida islam xasuci domin a gda tare sukeci a cewarshi,haka sukaci abincinnan yana bata a baki tana basa ko kunyar su mommy basaji har suka koshi.

Da kyar Aslam y yadda Islam taje gdansu khausar,hakan ma sai da Amira tace ai yaya sagir din y tafi Jordan karatu,mammy taji dadin ganin islam da xasu tafi mammy ta bata xumar mata tace tadinga sha kullum da daddare islam sarkin kwadayi ta dandana taji xaki tace toh ta gode suka futo ita da Amira,da khausar.

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*
??????
1/8/2017 10:20:53 AM: ?+49?174?6076805?: (8/12/2016/ 3:00pm) *Na Umma Yahya Musa*

????????????
????????
????
??
*GOYON KAKA*
*95*

Sai da akayi sallar isha'i bayan Aslam y dawo a masallaci sunyi dinner y kalli islam yace to my princess ki tashi mu tafi,cikin shagwaba ta fara magana harda diddira kafa haba my prince nifa naxata ka dawo dani gda kenan,cikin mamaki su mommy suke kallanta,daddy ne yayi murmushi yace haba mamana ina kika taba ganin an aurar da ya ta kuma dawo gdansu da xama,a lokacin harta fara hawaye da sauri Aslam yaje y kama hannunta yasa nashi hannun yana goge mata hawaye yace haba princess harda kuka kuma,ki bari nayi miki alkawari next week xan dada kawoki kinji,cikin jin dadi ta washe hakora tace Allah my prince kansa kawai y gyada yana murmushi kallansu daddy tayi dayake hardasu Abba a palon tace mun tafi saina dawo,dariya Abba yayi yace ja'ira y kalli Aslam yace kai kuma ka takarkare kana wani lallashinta harda goge mata hawaye ko kunyar mu bakaji,lokaci daya dukkansu suka dau dariya,banda islam data tura baki gaba,Aslam kuwa keya y sosa,mommy ce ta mike tace xonan my daughter taja hannunta suka shige daki,ta kalli islam tace daughter kina tsarki da ruwan dumin danace miki murmushi islam tayi tace eh ai kwata2 ma bana tsarki da ruwan sanyi cikin jin dadi mommy tace yauwa white misk ta dauko a wata babbar kwalba tace ungo duk dare ki dinga inserting dashi kanji,cikin mamaki islam tace mommy ban game a,anan mommy tayi mata bayani,dariya islam tayi tace to maganin mene,murmushi mommy tayi tace maganin sanyine sannan xakina kanshi kinji karfa ki dinga mantawa,gyada kai islam tayi tace ai baxan mantaba mommy tace yauwa daughter na tashi muje Allah yayi miki albarka,islam tace ameen suka futa,xaune suka tarar dasu daddy 5k daddy da Abba suka bawa islam karba tayi tana godiya suka futa part din kaka sukaje sukayi mata sallama sannan Amira da sauran yaran gdan suka rakosu mota suka tafi.

Tafiya sukeyi a cikin mota ba wanda yayi magana,islam ce ta kalli Aslam ta marairaice murya tace hero ice cream da shawarma nakeso,harara y dallah mata yace to mai cikin xani naga yanxu kika gamacin abinci,itama harararsa tayi ta murguda baki tace naji mutum da cikinsa ba'a hanashi cin abinci ba wasu ma yanxu suna gadon asibiti so akeyi suci amma babu hali,murmushi yayi a ransa yace yarinya tausayin ki nakeyi amma hmmm,parking ya futa y siyo mata shawarma da ice cream y mika mata,dariya tayi tace ngd yaya,kallanta yayi yace da akayi me?ta yatsina fuska tace kawai,murmushi yayi a ransa yana yarinyar nan ta daban ce watako ita bata barin takwana.

Tun a mota islam ta fara cin shawarmar ta kafin suje gda harta cinye 1 tasha ice cream rabin roba,gate man y wangale musu gate Aslam y danna hancin motarsa yayi parking suka futo,islam mika tayi tace wash Allah nagaji hero kallanta yayi yace me kike nufi,kashe masa ido 1 tayi tace wai daka goyani duka yakai mata takwasa a guje sai data je dai2 kofar shiga gdan ta tsaya saboda key din yana hannun Aslam,girgixa kai Aslam yayi yace narasa wanne hukunci xanwa yarinyar nan ta dinga shakkata,sai daya dauko ledar shopping din da bilal yayiwa islam a wani dofane yana yatsina fuska tamkar y dauko kashi,sannan y dauko ta shawarma da ice cream y rufe kofar motar y karasa mikawa islam ledar kayan yace dallah can rike kin barni da rike kaya kamar wani danki,murmushi tayi tace to naga daxu ma kaika dauka acan gda,banxa yayi mata bai magana ba suka karasa shiga gdan.

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*
??????
1/8/2017 10:20:53 AM: ?+49?174?6076805?: (8/12/2016 4:00pm) *Na Umma Yahya Musa*

????????????
????????
????
??
*GOYON KAKA*
*96*

Washe gari islam sai 10 o'clock ta tashi kamar yadda ta saba bayan tayi sallar asuba ta koma,bayan tayi mika tayi salati ta daura da addu'ar tashi daga bacci bathroom ta shiga tayi brush ta wanke fuska futowa tayi saboda kugin da cikinta yakeyi mata sai data leka dakin Aslam ta tarar dashi fes tabe baki tayi tace oho dai baka fini tsafta ba nima dan inajin yunwa ne shiyasa ban gyara bedroom din ba down stair ta fara sauka tun tana kan step takeji wani hadaddan kanshi y doki hancinta dada hura hancin tayi ta shaka sai kuma ta lumshe ido tace kai hero ba baya bane wajen iya girki karasa sauka tayi ta leka dinning area taga bayagun,kitchen ta tafi ganinshi tayi tsaye a gaban gas cooker yana daure da eprome da hula murmushi tayi tace gud morning hero,juyowa yayi ganin ko wanka batayi ba murmushi yayi dan yasan may be yunwa ce ta korota,yace morning how are u,yatsina fuska tayi tace I'm not fine because I'm feeling hungry murmushi yayi,yace to acici meyasa baki futo tun daxu kin dafa ba xakixo ki dameni da yunwa kikeji,hakora ta washe a ranta tace baxan mayar maka ba dan bakasan yunwar da nakeji bane, tadan sosa kai tace kasan kafini iya abincine shiyasa,dai2 lokacin y gama soya kwai yace to naji xoki dauki try dinnan kikai dinning dauka tayi takai shima y futo dauke da wani try din.

Yau lfyr Allah sukaci abincinsu,chips da kwai sai pepper soup na kayan ciki da tea daya saka su citta da kanin fari,bayan sun gama islam ta mike tace toh alhmdllh bayan ci xama tsegumi tana shirin barin gurin,rikota Aslam yayi yace kina nufin anan xaki bar kayan murmushi tayi tace namanta kwashe kayan suka yi suka kai kitchen futa islam take shirin yi da sauri Aslam yace ai baki isaba saiki wanke kayannan,cikin xumbura baki islam ta matsa sink din wanke2 ta fara kayan shikuma y dauki nasu get man y kirasu a waya sukaxo suka karba.
Chapter 34 · 0% Book details