← Book details Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 58

Sashe 47

Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Xaune ta tarar da Aslam ya bude kayan tsarabarshi y bawa su khausar tsarabarsu cikin manyan leda sannan yabawa khausar ta mommy kuma har sagir y siyawa agogo islam taji dadi sosai sannan y sakawa kowa tashi tsarabar a leda kama da mommy,aunty amarya,kaka,daddy,Abba,dadai dukka yaran gdan y deba ya kalli su Amira yace ku taso mu tafi islam tayi xuruf tace basuci abinci bafa khausar tace maci in munje gda abincin su joseph islam ta dauko ta biyosu Aslam kawai ji yayi an bude front seat an shigo dago kansa yayi ganin islam yayi ta kame a xaune ko after dress din bata saka ba tana rike a hannunta dauke kansa yayi daga kallanta yace ke kuma wayace ki futo rau2 tayi da ido cikin shagwabar murya tace binku xanyi tsoro nakeji shiru yayi mata yaja motar suna karasawa wajansu joseph ta mika ma peter abincin joseph kuma y bude musu kofa suka futa.

Suna xuwa gdan kaka dukkansu suka futo Aslam ganin islam nashirin tafiya a haka shine yace to baxaki saka rigar taki ba xaki tafi xumbura baki tayi ta saka after dress din suka wuce part din kaka,aslam y rabawa kowa tsarabarsa sun karba suna godiya dasa albarsa sai wajen 10pm su islam suka tashi suka tafi gda suna xuwa abinci kawai sukaci,sannan Aslam yace pretty muje kema ki karbi tsarabarki cikin jin dadi ta mike suka karasa palon akwati guda y bude mata acikinsa englih wears ne,dogayen riguna takalma jakunkuna harda jewelries da bangles masu kyau cikin jin dadi islam ta fada kan Aslam ta bashi peak a kumatu tace tnx my hero Allah y kara budi yace Ameen,dayan akwatin dayake gabanshi y shafa yace wannan kuma na amarya tane mai xuwa nan bada jumawa ba kar cikin xuciyar ta taji saukar maganar cikin jin haushi ta tashi ajikin cikin masifa islam tafara magana tace to saime aini baxaka birgeni ba sainaji gobe ana ayyuriri an kawo maka amarya shine xansan kacika,Aslam tsantan kishinsa y hango kwance akan fuskar islam amma sai ya waske duk da dariya yakeson yi jin yadda ta balbaleshi da masifa yace haba yan matana saurin me kikeyi nan da 4 month xata shigo karki damu tamkar yaune cikinjin haushi ta wuceshi ta suka haura stair tabar kayannata anan shima tashi yayi xuciyarsa fes saboda ko banxa ya gano sansa a xuciyar islam kuruciya ce kawai ta hanata gane tana sonsa shima y haura stair y wuce dakinsa.

Washe gari haka islam ta dinga cin magani ita bata yadda ba tana fushi Aslam kuwa sai fakon idonta yakeyi yana mata galo tsahon 2 days islam ta dauka tana fushi daganan ta ware.

*A GURGUJE*
Haka rayuwar su islam taci gaba da tafiya kullum islam da kalar abinci da xatayi safe rana dare sannan duk lokacin da tayi abinci tana xubawa su joseph,haka Aslam xai xauna y narki abincinsa amma hakan baxai hanashi y kushe ba tun islam najin haushi harta gaji yanxu haka tasaka an fara cikita mata yarinyar da zata dinga taimaka mata da wanke2.

Yau saura 2 days su islam su tafi pkotercort pepper soup tayi na kifi amma sai ta xuba a flask ta daura a try hade da plate dan a garden takeson ci kallan Aslam tayi da yake amfani da laptop dinsa yana magana akan motocin da xa'a shigo masa dasu tace hero nidai natafi garden saika taho murmushi yayi yace saurin me kikeyi da baxaki jirani ba tace a'ah ni baxan jira kaba sai dai ka taho ta fice tana dan wake2 ta.

Xaune take a garden ta bude flask din pepper soup dinta na kifi ta xuba a faranti ta rufe sauran ta saka spoon ta faracin pepper soup dinta cikin jin dadi ashe abinda islam bata sani ba magece a can nesa da ita kadan nanfa mage taji kanshin kifi a hankali ta fara daga hancinta tanabin sahun inda taji kanshin kifi nan fa idonta yayi arba da plate din kifi kan cinyar Aslam lokaci daya magennan ta taho da gudu tayo kan islam, sai a lokacin islam ta kula da magen ai da hanxari ta mike ta kwasa a kuje hannunta rike da plate din kifin magen ma ganin haka ta mara mata baya gudu islam takeyi magen na Binta Aslam kawai take kwalawa kira tana ihu hero!hero!!hero!!! a bakin kofa sukayi kicibis da Aslam saboda yajiyo ihunta y taho da gudu lokacin yayi dai2 da tayi fatali da plate din kifin wata muguwar suka magen tayi ta tafi gurin kifin islam kuwa taxaci kanta xata fada haka ta fada luuuu kan Aslam ta sume.

*_ngd sosai yan uwa da addu'o'inku a gareni da tayani murnar xagayowar ranar aurena Allah yabar kauna y kara xumunci ngd ngd ngd sosai_*

*_may be nan da 2 days baxakuji posting dina ba saboda wani uxiri daya tasomin amma inna samu yadda nakeso ko gobe xakuga posting dina dftn xakumin uxiri_*

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*
??????
1/8/2017 10:21:01 AM: ?+49?174?6076805?: (1/1/2017 3:00pm) *Na Umma Yahya Musa*

????????????
????????
????
??
*GOYON KAKA*
*125-126*

Cikin firgici Aslam y fara girgixa ta jin ko motsi batayi da sauri y tafi dispenser y tsiyayo ruwa yaxo y yayyafa mata jin har lokacin batayi motsiba shine y saka shi kama kanshi yace oh god y xanci gefenshi y kalla yaga magen harta gama cinye kifin daya bare a kasa tana lashe romon dayake kasa cikin xafin nama Aslam yayi kan magen yayi mata wata muguwar danka har saida magen tayi kara saboda taji damkar da akayi mata direct waje Aslam yayiwa da ita.

Su joseph y fara kwalawa kira joseph! peter!! kuna inane wai cikin tsoro suka futo daga dakin da aka tanadar musu a gdan jikinsu yana rawa saboda kiran da sukaji ogannasu yanayi nusu xubewa sukayi a gaban Aslam cikin gurbatacciyar hausar sukace gamu oga wani mugun kallo y jefesu dashi yace acikinku wane ya kawo mage cikin gdannan tuni cikin peter y bada wani kululululuu saboda duk magunan gdan nashine tuni jikinshi y dauki rawa cikin barin baki yace nawa ne oga wani mugun kallo Aslam yayi y wulla masa magen datake hannunsa cikin peter yace ka tabbatar ka futar da duk wata mage da take gdannan cikin 5 minutes inka kuskura ka wuce time din dana dibar maka kasan cewa tamkar ka rubuta takardar barin aikin kane y juya y wuce peter cikin barin jiki y tattara magunan gdan ya sakasu a cikin buhu y fice dasu daga gdan.

Aslam yana komawa cikin palon ruwa y dada debowa wannan karan kwarawa islam yayi wata muguwar ajiyar xuciya tayi hade da jan numfashi bude idanuwanta tayi taga Aslam a kanta a tsaye da sauri ta tashi taje ta rungumeshi tace wlh hero magennan kasheni takeson yi dan taga ina tsoronta shine take xuwa gurina ta tuni hawaye suka fara ambaliya tare da shashshekar kuka Aslam har cikin ranshi yakejin kukannata a hankali y fara shafa bayan ta yake y isa kiyi shiru daga yau baxaki kara ganin mage a gdannan ba domin nasaka an fitar da ita daga gdannan a hankali ta xare jikinta daga nasa ta koma kan three seater ta wani lafe tamkar marainiya tuni Aslam yayi wani mugun tausayinta y kara kamashi da kansa y futa yaje garden y dauko kifin y dawo kitchen y shiga y dauko plate da kansa y xubawa islam amma sam taki karba gani takeyi tamkar inta karba magen xata kara dawowa.

Yau su islam xasu tafi photercort tafiyar tasu ta hada da Amir,Amira,khausar xasu tafi flight suka bi lokacin da suka isa photercort safwan ne yaxo airport y daukesu sai wani rawar kai yakewa khausar itama haka ta xage tana nuna masa kalar soyayyar datake masa direct gdansu ya kaisu mammy ce ta fara nan2 dasu khausar kuwa sai wani kunya takeji mammy ce ta kula ta kasa sakewa mammy ce ta janyota jikinta tace yata ki saki jikinki dani nima mahaifiyarki ce sannan khausar ta ware.

Yaune reception din da aka hadawa su Aslam na dawowa daga singapore lfy bayan jawabai da akayi hade da paretty da sojoji suka gabatar daganan aka fara rabawa su Aslam lambar yabo islam itace ta raka Aslam y karbi nasa inda khausar ta raka safwan y karbi nasa bayan pics da akayi hade da ciye2 da shaye2 taro y watse kowa yaji dadi.

Washe gari su islam suka shirya xasu koma kano saboda ranar monday xasu koma makaranta amma banda Aslam saboda shi baiga amfanin komawar shi gda ba dan inya koma ma hankalinshine xai na tashi dan sam islam ta futo da wata tsurfa sam ta daina saka atamfa ko lace a gdanta sai english wears shiyasa yace baxai koma ba danshi kenan kullum cikin shan ruwan lipton hade da lemon tsami saboda bakaramin kokari yakeyi ba ganin y jure xama da islam duk da yana cutuwa gata dason jiki in dai suna xaune to dole tana jikin sa.

Yau monday bayan su islam sun shirya isya driver shine y dauke su y kaisu makaranta acan suka tarar da khausar bayan anyi assembly aka bawa islam dan kwalin head girl khausar assistant head girl Amira kuma labour prefect sannan kowa y koma class sukayi attending lesson.

To tundaga wannan my mukami da aka bawa su islam iyayi y karu da rashin m dan dama su islam ba baya bane ita da khausar gwanda Amira itace ma bed babu ruwan ta.

Aslam kuwa baya xuwa gda sai bayan 2 to 4 weeks saboda sam baxai iya da halin islam ba shikenan duk randa yaxo kano sai ciwon cikin shi y tashi dan haka cikin fridge dinshi baya rabuwa da lemon tsami sannan koda yaushe cikin saka islam yake ta dafa maga ruwan lipton.
Chapter 47 · 0% Book details