← Book details Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 58

Sashe 42

Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khausar tana shiga dakin itama ta hada wayar tata ta jonata a chargy,khausar tace 6*s yanxu fa munxa ma manyan yara,Amira tace gaskiya fa,islam kuwa yatsina fuska tayi tace aini na dade da xama babbar yarinya kune dai sai yanxu,dariya sukayi sukace aike cus ce keda kike married woman suka karasa da kyalkyalewa da dariya wani malulun bakin ciki islam taji y turnike ta,khausar ce tace uhm ni ku tashi mu tafi naje nayiwa yaya amir godiya,Amira tace toh ta mike islam kuwa kwanciya tayi tace wlh ba inda xani yaushe rabon dana futo waje sai yau to kuwa sai dare xan koma,dariya sukayi suka futa a dakin sagir suka gani xaune yanata ware kayayyaki mammy tace ina kuma xakuje kukabar islam din,khausar ce tace godiya xanje nayiwa yaya Amir islam kuma tace baxata tafi yanxu ba,wai sai dare dariya mammy tayi ta mika musu laffaya masu kyau da tsada guda 3 tace gashinan ku kaiwa su hajiya inji dansu to sukace suna godiya suka futa saboda yau a sa'a tayi musu mammy tashi tayi ta debi nata kayan ta tafi daki,islam jin shiru a palon shine y sakata futowa da niyyar tafiya part din yaya sagir turus ta tsaya ganinsa xaune a palon a hankali ta karasa ta xauna tace sannu yaya sagir dftn ka dawo lafiya,har cikin kanshi yaji muryar tata sai da yayi addu'ar tsari daga shedan sannan y dago kanshi murmushi yayi mata yace lfy qlau 6* dftn nasameku lfy,cikin jin dadi islam tace lfy qlau,yace masha Allah,ya kara magana ina mijinnaki har kika samu damar futowa yawo,xumbura baki gaba tayi sannan tayi magana y tafi wani course xaiyi 2 years a singapore girgixa kanshi yayi yace Allah y dawo dashi lfy tace ameen,shiru dukkansu sukayi sagir kuwa yana jinjina lamarin a ransa yadda Aslam y iya tsallakewa y tafi wata uwa duniyar yabar islam a gda,wata xuciyar ce tace to ina ruwanka kawar da tunanin yayi a xuciyarsa su Amira ne suka dawo nan y bawa kowa tsarabarsa sunyi murna sosai da godiya.

Haidar ne y shigo dakin kaka toxali idanuwansa sukayi da wayoyin su islam da mamaki y karasa yana kaka wadannan wayoyin nasu wane itama kaka sai lokacin hankalinta yakai Kansu tace ni banma kula dasu ba sai yanxu y tafi da niyyar dauko wayoyin su islam suka shigo da gudu ta karasa tana haba yaya haidar y xaka cire mana wayoyin mu alhalin basu cika ba.

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*
??????
1/8/2017 10:20:58 AM: ?+49?174?6076805?: (22/12/2016 2:00pm) *Na Umma Yahya Musa*

????????????
????????
????
??
*GOYON KAKA*
*111*

Bayan Amir y futa murna su islam suka fara harda rawarsu da sauri suka tafi suka sassaka chargy,islam ce ta kalli Amira tace anya 6 ba sonki kuwa yaya Amir yakeyi ba kuwa,Amira tace ki jiki da fassara me kika gani,sai da islam ta kada idanuwanta sannan tace alamu sun nuna yaya sanki yakeyi dan gane da irin kallan daya jefeki dashi sannan bakiji yace saura yaga numbobin samari a wayar taki ba indai ba sonki yakeyi ba ina ruwansa da samarin da xakiyi,Amira hmmm kawai tace,islam ce tace yauwa dan Allah yi maxa ki tashi muje gdansu khausar mukai mata tata kan kakannan ta futo tace baxan futa ba,Amira tace ki bari mana sai anjima islam tace wlh baki isa ba ta tashi tasa hijaba bakisan yadda kafata take kaikayi ba rabona da futa waje fa tun ranar friday da mukaje makaranta kuma kinga munyi hutu yanxu wa yaga ranar kara futa ta tayi waje Amira ma hijabi tasaka ta dauki ledar tasa wayar khausar din tabi bayan islam.

Amira tace to uwar axarbabi da kika bar wayar da in kinje me xakice wa khausar din dariya islam tayi tace ai mantawa nayi a nutse suke tafiyarsu har sun kai bakin kofa islam ce tajiyo miryar aunty amarya tana ku islam ina xakuje cak islam ta tsaya ta kalli Amira tace nabanu yanxu aunty amarya xata hanani futa,aunty amarya ce ta fara takowa wajensu islam ganin haka da gudu ta kwasa ta fuce waje dan a yadda takejin kafarta na mata kaikayi wlh ko daddy ne y hanata futar nan saita fita,aunty amarya ta karaso tace Amira ina xakuje ne,Amira tace gdansu khausar, aunty amarya tace me xakuyi acan da tsakar ranar nan,Amira tace waya xamu kai mata,aunty amarya ta maimaita waya!,Amira tace eh yaya Amir ne y siyo mana aunty amarya tace y kyauta to meya saka islam guduwa kuma,Amira tace wai tsoro takeji karki hanata futa dan kafarta kaikayi takeyi,dariya aunty amarya tayi tace Allah y shirya islam watako saboda tsabar yawo kafarta har kaikayi take,itama Amira dariya tayi aunty amarya tace to saikun dawo,Amira tace toh ta fice.

Xaune Amira ta tarar da islam akan wani sock away da yake gaban gidansu kadan,Amira tace to tashi mu tafi,islam tace toh wlh dadin iskar waje ma daban take data cikin gda ta wani lumshe ido,murmushi Amira tayi tace gaskiya islam ban taba ganin mace mai shegen son yawo irinki ba watako iskar cikin gda data waje har banbanci ne da ita,yatsina fuska islam tayi tace eh ni wlh ma wannan hutun dole a gwarxo xan yishi,dariya Amira tayi tace harda dole kamar kin manta bake kikeyin iko da kanki ba,tsaki islam tayi tace Allah sai naje saboda mugunta irinta hero y barni da igiyoyin auransa a kaina suna hanani rawar gaban hantsi ta karashe maganar da murguda baki,dariya Amira ta karayi tace watako 6 xanso naga ranarda bakinki xai mutu,wani birki islam taja tace tab yasin ba ranar da bakina xai mutu sai dai in mutuwa nayi gaba 1,dariya Amira ta karayi tace bama saikin mutu ba yaya Aslam xai kasheshi cikin masifa islam tace Allah y kiyaye lokacin yayi dai2 da karasawarsu gdansu khausar shiga sukayi suka gaida baba mai gadi suka wuce.

A xaune suka tarar da mammy da sagir suna hira gaishesu sukayi mammy ce kawai ta amsa sagir kuwa mikewa yayi,islam sai taji duk ba dadi dan rabonta dashi tunda y tafi cairo karatu sai yau ta ganshi gani tayi y kara girma sosai,islam tace mammy ina khausar fa mammy tace tana daki tashi sukayi suka shiga dakin kwance suka tarar da khausar tana bacci daka mata duka islam tayi tace toh kasa sarkin bacci saiki tashi firgigit khausar ta mike tana sosa cinyarta hararar islam tayi tace wannan wanne irin iskancine,islam tace naji mai da wukar naga yaya sagir yaushe y dawo,khausar tace tun ranar friday islam tace shine bakixo kin fadamin ba,khausar tace amfanin me fadar xaiyi miki shiru kuma islam tayi Amira ce ta daura mata ledar a cinya budewa khausar tayi ganin waya aciki kuma wadda ake yayi iphone 6+ shine sakata waro ido waje tace wayar waye.

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*
[truncated by WhatsApp]
1/8/2017 10:20:59 AM: ?+49?174?6076805?: (25/12/2016 3:00pm) *Na Umma Yahya Musa*

????????????
????????
????
??
*GOYON KAKA*
*116*

Yau islam jinta takeyi cikin farin ciki tunda ta tashi ita kanta tarasa dalili alhalin jiya da daddare dakyar ta iya bacci saboda missing daddadan muryar Aslam da tayi 3:00pm suka fara shiri saboda bikin wata kawarsu da xa'ayi wadda sukayi islamiyya tare kamu ne xasuje a gdan dan hausa dakyar ma islam tasamu aka barta xuwa bikin sai da tadinga kuka tana roko sannan aka yadda taje bakaramin kyau sukayi ba yan matan 3 musamman islam da tasha gyaran jiki tamkar a tabata jini y futo simple makeup ita tayi saboda tasan kotayi tafi haka yawa sai ansa ta goge amma bakaramin kyau tayi ba ankon kamunne a jikinsu sky blue din material mai raga2 anyi musu landing da pink swiss tafita aciki sai suka daura pink rose sarka da dankunne duk pink ne iri 1 bakaramin kyau kayan yayi musu ba saboda dinkin y xauna das ajikinsu tamkar ajikinsu aka dinkashi.

Islam tasaka takalmi da pose pink sai Amira tasaka sky blue khausar kuma baki mayafai suka yafa duk pink wow masha Allah xanso fans din goyon kaka kuga wadannan hadaddun yan matan ga kuma wani sihirtaccen kanshi dayake tashi a jikinsu amma saika matsa kusa dasu xakaji.

4:00pm suka futo cikin shirinsu suna tafiyarsu cikin nutsuwa tabbas duk wani da namiji mai lafiya yayi toxali da wadannan yan matan dole y susuce yaya haidar suka samu y taimaka y kaisu gdan dan hausa sai daya gama wulakanta su sannan y kwashesu lokacin daya kaisu yace wlh kar kuma naga yarinyar data kirani tace nadawo na dauketa dan sam baxanxo ba Wlh, islam ce ta harare shi tace to kada Allah yasa ka dawo daukar tamu kaga in xamu dawo a kasa toni harkamin iyayin mota ma karka manta ni motace sukutun dani kaikuwa fa ta karoro ce duk taran aro naushin sitiyarin motar yayi yace lallai ma yarinyar nan kinyi bala'in rainani ke dabadan kina matar yaya ba wlh da yau saina yimiki tsinannen duka dariya tayi tace mafashi ta kalli su Amira da suke bayan mota tace ku futo mu tafi, harta xura kafarta a waje ta juyo tace bari nayi maka tayan kauye karamin mai gda saina dawo ta kashe masa ido 1 ta futa a motar, haidar tsintar kansa yayi dayin dariya yace lallai yarinyar nan ta samu sake yaja motarshi yabar gurin.

Lokacin dasu islam suka shiga nanfa kallo y koma kansu amma saboda kwarjinin da suka yiwa samarin gurin kaf sun rasa wanda xai tunkaresu har suka karasa cikin theater dayake anan gurin akeyin kamun kawarsu bakaramin dadi tajiba lokacin data gansu.
Chapter 42 · 0% Book details