← Book details Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 58

Sashe 56

Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Cikin islam nada 6 months ta dada kiba da cika gashi majority kayan da take sawa sunyi mata kadan gashi suna shirye2 tafiya kano bikinsu amira wanda xa'ayi upper week xaune take ta tasa dan silif a gabanta ga kuma katon cikinta da shima yayi nasa xaman a gabanta tanacin dan silif data saka tumatur da albasa kallan Aslam tayi tace gaskiya hero kayimin wayo yanxu in mukaje kano suka ga katon cikinnan ai kunya xanji, murmushi yayi yace menene na kunya bayan cikin sunna ne ajikin ki, rau2 tayi da ido alamar son kuka tace to yanxu kowa kuma inya ganni yasan ta yadda akayi na samu ciki ko kawai sai tahau kuka,ai dariya da Aslam yakeson rikewa kasawa yayi kawai y tuntsire da dariya ba kakkautawa islam ganin haka ganin haka tace me kuwa xatayi inba kuka ba,kuka tahau yi sosai harda turturxa kafafu wa irinna yara tana wlh nafasa maka rainon cikinnaka ka kaini asibiti a cire a saka maka kayan ka kuka takeyi sosai tamkar ba gobe Aslam ganin haka da sauri y hadiye dariyarsa y taso yaxo y rungumeta ta baya yace haba my princess y xaki wahalar da kanki sannan ki wahalar mana da babyn mu banxa tayi masa kamar batasan me yake cewa ba takara volume din kukanta iska y fara hura mata a kunne hade da shafa mata baya a hankali ta fara sauke ajiyar xuciya sai da Aslam yaga islam tayi shiru sannan y daga ta suka koma kan kujera suka xauna yace haba princess ke bakya gajiya da kuka ne koda yaushe kamar wata karamar yarinya anayin magana kadan ki bare baki kihauyin kuka kokin manta kin kusa xama mommy ne sai data goge hawayen fuskarta da hannunta tace to ai kaine ka sakani nayi maka magana inaso ka samomin solution amma kawai sai kahau kuka murmushi yayi a ransa yace princess rigima wanne solution xan nemar miki bayan kin rigada kinyi ciki sabanin haka a fili sai yace to shikenan duk wanda xaiyi miki magana kice a ruwa kika sha tunda ai ana shan ciki a ruwa ko baki sani ba kanta ta gyada masa alamar bata sani ba yace toh shikenan daga yau ki sani ana shan ciki a ruwa kinji murmushi tayi alamar jin dadi tace Allah hero hancinta y lakace yace kujimin mara kunya kin iya xuwa ki tasani a gaba saina baki xumata amma yanxu kin samu gud result daga gareni kice xakiyi min iyayi dariya tayi ta rufe fuskarta a kirjinshi domin ita kanta tasan mijinta jarumi ne yasan kalolin salon dda xaiyi amfani dasu ganin y samu abinda yakeso a wajenta cikin sauki domin duk da girman cikinnan nata baya hanata bashi hakkinsa domin itama koda yaushe cikin bukatarsa take.

Yau suka tafi kano domin saura 3 days a fara bikinsu Amira bayan sunje nan fa su khausar suka tasata a gaba sunayi mata shakiyanci wai ita mai cewa baxata bawa Aslam kanta ba saitayi candy ai yanxu sunga candy tunda gadan baba nan y tona asirin da take boyewa dama sunsan cika bakine ta dade da mallakawa Aslam kanta ta rufesu bai2 banxa tayi dasu sai data ga sun fara isarta sannan ta fara mayar musu da martani ta wajen cewa eh din ai dadinta mijinta ne kuma masoyinta shewa suka saka sukace yau kuma keda kika ce baxaki tabasan hero ba ganin suna shirin kure ta shine y sakata tashi a kufule tabar musu dakin ta tafi gurin kaka tana mata korafi wai su Amira suna yi mata dariya dan tana da ciki, nan fa kaka ta mike ta futo ta samu su Amira ta farayi musu fada domin sun taba yar lelenta dakyar suka samu kaka ta kyalesu.

Wani tashin hankalin islam lokacin dasu khausar suka kawo mata ankonta nanfa tayi2 ta gwada amma ina duk sukaki shigarta ihu tahau yi su Amira kuwa suka ce me xasuyi inba dariya ba ganin kukannata bamai karewa bane shine saka su kiran Aslam ba shiri y taho y ratsa cikin matannan jin princess dunshi wai tana kuka bayan yaje y tambaya meya faru anan suka fada masa dalilin kukan ta a mota y dauketa suka tafi kasuwa suka siyo exactly irin angon y wuce da ita gurin tela a take aka gwadata a lace din dinner akayi mata buba a atamfar kamu data yini da material din dinner photercort akayi mata dogayen riguna telan yace xuwa dare su dawo sai lokacin ta saki ranta ta fara fara'arta.

YaYaune kamu amare sunyi kyau sunsha makeup islam kuwa duk da bawani makeup tayi ba amma tayi kyau sosai anyi kamu lfy an gama lfy,yau juma'a bayan idar da sallah a masallaci dubunnan mutane suka shaida daurin auren Abdul-qadeer Aliyu Umar (Ameer) & Zainab Abdul-qadeer Umar da kuma safwan Abbakar sadeeq & Khausar yusuf nadabo akan sadaki 50k daganan angwaye suka wuce reception.

8:00pm aka fara shirin tafiya dinner yau dai islam ta tsaya ta tsantsara makeup sosai tayi kyau Aslam ma y saka m ilk din shadda gixna sai y saka brown hula xanna bukar hade da takalmi mai ddan yatsa brown sai agogon fata na gucci shima brown ba karamin kyau sukayi ba inda amare da angwaye ma sun hade cikin hadaddun kayansu bakaramin kyau sukayi ba islam da Aslam sune a hight table islam sai nan2 take da hero dinta ganin yan mata nakawo masa farmaki 10:30pm aka tashi a dinner din anci ansha anyi raba kayayyaki kama dasu kalandu memo key holder harda t shirt Aslam da islam sunyi rawar gani abikin sunyi barin naira sai dai fatan Allah y bada xaman lfy.

Washe gari akayi wuni shima y kayatar anci ansha anyi rabon tobobi manya manya,washe gari mutane basufi 20 ba suka tafi photercort kai khausar tasha kukan rabuwa da mammy da yaya sagir a tafiyar harda Amira saboda akwai dinner din da xa'ayi acan gdanta na cikin gdansusagir aka ware mata part an xuba kayan more rayuwa sosai gdanta yayi sai dai sam barka da fatan Allah y basu xaman lfy sannan an xuba mata wasu kayan a gdanta na barrack saboda acanne safwan yake aiki inda take makotaka da islam.

8:00pm aka fara tafiya dinner din itama tayi kyau ta kayatar inda sosojoji da matayensu suka je harda Amir da Amira sai 12:00am sannan aka tashi a dinner din.

Washe gari tun 8:00am yan rakiyar amarya suka fara shirin dawowa kanon dabo suka bar amarya a gdanta dadinta 1 an barmata islam a ranar kuma aka kai Amira itama gdanta dayake kusa da gdan islam na kano to mudai sai dai muyi fatan Allah y bawa amare xaman lfy da kwanciyar hankali a gdajensu.

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*
??????
1/16/2017 9:27:50 PM: ?+234?803?560?7375?: (16/1/2016 3:00pm) *Na Umma Yahya Musa*

????????????
????????
????
??
*GOYON KAKA*
*143-144*

Bayan bikin su Amira da sati 2 Aslam su Aslam sunje asibiti akayiwa Islam scanning anan aka gane twice ne acikinta kuma duk mata xo kuga dadi agurin islam har wani iyayi takeyi wai xata haifi yaran da xata koyi kitso a kansu Aslam kuwa sai dariya yake mata yana ita da tace batason babyn cikin masifa tace to yanxu inaso tunda matane da xa'ayi musu kwalliya 3 days letter Aslam y dauki Islam suka tafi dubai siyo kayan jarirai kaya suka siyo sosai acan satinsu 2 suka dawo inda cikin islam yake da 8 months nan fa ta xama, xama dakyar tashi da kyar dan dole Aslam y dauketa y kaita kano saboda yadda mommy ta dameshi da waya akan y dawo mata da daughter dinta haka y kaita badan yanaso ba amma duk sati yana hanyar xuwa kano cikin wannan halin cikin islam y cika 9 months nan fa aka fara tunanin haihuwa domin yau ko gobe ake saka ranta.
Chapter 56 · 0% Book details