← Book details Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 58

Sashe 23

Goyon Kaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty amarya da kanta ta tashi ta shiga kitchen ta xubo abinci a plate,da kanta ta xauna tayi feeding dinshi tana bashi lbrai masu dadi,cikin farin ciki yakecin abincin harya cinye baisan y cinye ba,bude baki yayi aunty amarya ta xura masa cokali,cikin mamaki yace ina abincin lakace masa hanci tayi tace ka cinye a tare suka tuntsire da dariya,aunty amarya tace ko a dado makane Aslam yace a'ah nakoshi,y lumshe ido yace aunty na ngd Allah y kara lfy da nisan kwana,murmushi aunty amarya tayi ta tsiyaya masa lemo exotic a glass cup ta mika masa tana ameen,Aslam yace gaskiya ne da akace wanda y rasa uwa yayi kuka domin shine babban maraya saboda nidai gashi nagani rabona danaci abinci spoon 3 harna manta dan ina faraci xanji yanamin daci,amma yau da uwata ta sakani a gaba gashi harna cinye cikin plate bansani ba,dariya aunty amarya tayi tace my son bakada dama wlh,dariya yayi shima y mike yace bari naje naji preparation din dasu safwan suka tsara saboda yau aunty na ta bani kwarin gwiwa y fice,murmushi aunty amarya tayi ta dauke try din data sako abinci takai kitchen.

Da farin cikinshi y shiga part dinsu xaune y tarar da safwan da amir shima xama yayi yana guys wanne shirye2 kuka tsara abikinnawa ne,cikin mamaki suke kallanshi tamkar ba Aslam ba mutumin da yakeyi musu masifa in suna hirar program din da xasu gudanar a bikin amma yau shida kansa yake tambayar su,Amir ne yace kawai mun shirya receiption bayan daurin aure shikenan tunda kace bakasan ayi duk wani Abu dan baxaka halarta ba,yace OK naji yanxu najanye duk wani kudiri na,after wedding fateeha akwai reception yes haka yayi,da misalin 4:00pm sai ayi kilisa a fadamin nawane kudin hayan dawakai,ranar asabar 2:00pm akwai parety da daddare kuma akwai dinner sai a nemo hall mai kyau,cikin jin dadi sukace gaskiya hakan yayi.

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*
??????
[11/18, 5:54 PM] ??????Salma??????: (18/11/2016 4:00pm) *na umma yahya musa*

????????????
????????
????
??
*GOYON KAKA*
*68*

Misalin 4:00pm su Aslam suka futa neman hall din da xasu yi reception da dinner dakyar suka samu saboda sunxo a kurarran lokaci,country mall anan xasuyi reception,sai the afficent inda xasuyi dinner aikuwa sunsha kudi saboda hall din manya ne,a gajiye suka koma gda bayan sunyi wanka Aslam da kanshi y kirawo abokanansa yana sanar musu daurin auranshi nan da 3 day aikuwa sai tsiya suke yi masa akan bikin saida yaxo daf xai sanar musu hakuri kawai yake basu yace wlh shima auranne yaxo ba xata sunyi masa fatan Allah y bada xaman lfy kuma insha Allah xasu xo daurin auren,kallan safwan yayi yace ka sanarwa yan photercourt ne safwan yace eh ai har general nasanar masa kuma yace insha Allah xaixo,Aslam ne y cillah masa pillow yace dan rawar kai sukayi dariya a tare.

Yau alhamis mai gyaran jiki taxo tayiwa islam sannan tayi mata kunshi ja da baki aikuwa tuni islam tahau kyalli,ga daddadan kanshin da takeyi koya ta gifta a guri saita bar kamshinta,kowa masha Allah kawai yake cewa saboda yadda islam tayi wani sihirtaccen kyau gaba daya kamarta ta canja,mommy ce tace yata futo ki rakani unguwa islam tace toh hijab ta xurma suka fice isya driver mommy tasaka ya kaisu gurin returching islam tace wlh mommy narasa meyasa kawai saina dingajin xuciyata tana bugawa kuma ina yawanjin tsoro murmushi mommy tayi tace kidinga karanta *inna lillahi wa inna ilaihirraji'un*,islam tace toh suka karasa aka yiwa islam returching aikuwa yayi kyau saboda yadda gashinta yadada tsayi har gadon baya ga wani sheki da kyalli da yakeyi ana gamawa suka koma gda lokacin anyiwa Amira da khausar gyaran jiki da kunshi sai dai nasu baikai kyanna islam ba gwalo islam tayi musu tana cewa yeah nafiku yin kyau ko kunshina yafi kyau,cikin jin haushi sukace eh munji don sunsan ba karya islam tayiba.

Yan'uwa sun xaxxaxo kowa yaga islam saiyace islam irin wannan kyau haka ko yar gda xa'ayi keda Aslam din cikin jin haushin maganarsu take cewa Allah y kiyaye mexanyi dashi,ganin kowa yaxo haka yake cewa ko itace amaryar cikin kuka ta tafi gurin kaka tana ihu dakyar kaka ta lallabata tayi shiru tace waya tabaki cikin xumburo baki islam tace ba mutane bane dan sunga nayi kyau shine suke cewa wai ko nice amaryar hero nikuwa nace mexanyi dashi Allah y kiyaye ta karashe maganar da murguda baki,murmushi kaka tayi tace rabu dasu karki kara kulasu wasa sukeyi miki islam tace toh ta tashi ta futa,kaka kuwa murmushi tayi saboda yadda tasan irin darun da xa'ayi kafin islam ta yadda da aurannan.

Islam ce kwance kan gado sai juyi takeyi sakamokon yadda taji duniyar duk tayi duk taji ranta a jagule,Amira da khausarne suka shigo dakin cikin murna suna kiran islam 6* ganin islam a kwance khausar tace tashi kika kayan mu ke naki mommy tace gobe xata baki,cikin masifa islam tace dan Allah karku dameni ku kyaleni da abinda ke damuna,Amira tace kayan bikin yaya nefa kuma kowa set 5,tsaki islam tayi tace ku bikin hero y dama da harxaku tashi hankalinku dan an baku kayan anko set 5,tayi tsaki ta gyara kwanciya,sukuwa cikin murna suka gwargwada kayannasu lace 2,material 1,atamfa 1,shadda 1,suna gama gwadawa suma suka kwanta,islam kuwa sai juyi takeyi sam ta kasa bacci tashi tayi ta shiga bathroom ta dauro alwala ta shimfida sallaya tayi nafila raka'a 8 ta dade a sujjadar karshe tana addu'a Allah y sassauta mata xafin xuciyarta sannan bugawar da kirjinta Allah yasa lfy ne,koda ta idarda sallah a sallayar ta xauna taci gaba dajan carbi saboda sam batajin bacci,bacci barawo dai shine y sace islam kan sallayar.

To jama'a kuna ganin alkawarin da Aslam yayiwa aunty amarya xai iya cikawa idan yaji islam ce matar tashi ko kuwa dai xai karya alkawarin kuci gaba da biyoni donjin yadda xata kaya.

Taku har kullum *sisin mama*

??????
*mrs hamisu taura*

??????

[11/19, 8:30 PM] ?+234 810 749 9249?: (19/11/2016 7:00pm) *na umma yahya musa*

????????????
????????
????
??
*GOYON KAKA*
*70*

Mai kwalliya ta nada mata dan kwali tamkar nadin gwargwaro,inda ta xubo mata da wani gashin ta gaba har kafadarta y sauka,ragowar kuma aka sakeshi ta baya y sauka har gadon vayanta,wayanta mai kwalliyar ta dauko ta fara gyarawa islam pics,gaban dressing mirrow islam ta tafi wani dadine y mamaye mata xuciya saboda irin kyawun da tayi itadai tasan tunda uwarta ta haifeta bata tabayin kyau irinna yau ba,mommy kuwa masha Allah kawai take cewa tace daughter na kinga kyawun da kikayi tamkar zarah acikin taurari,islam cikin jin dadin furucin mommy tace yauwa mommy bari naje nanunawa su khausar kwalliyata in musu gwalo nasan nafisu yin kyau,hannunta mommy ta kamo tace a'ah bari naje na turo miki su ko kinaso ki futa mutane suyita tankaki,cikin gasgata maganar mommy tace a'ah ta koma kan kujerar dressing mirrow ta xauna tanata faman murmushi inta kalli kanta tacikin mirrow mommy kuwa kai ta girgixa ta fice.

Aslam kuwa suna futa kofar gida,dubunnan cincirindon mutane ne a tsaitsaye,kamada masu fada aji a gwamnati,yan kasuwa,sannan da manya2 sojoji harda kananu,saboda ance a nan kofar gdan xa'a hadu aje gurin daurin aure,a hankali Aslam yaga mutane suna shiga cikin masallacin unguwarsu,a ranshi yace kenan yarinyar da xa'a auramun yar unguwar nan ce,ras girjinshi y buga tunawa da yayi kaf layin ba yarinya datafi 18 year dukkansu daga 18 year ne xuwa kasa,cikin sanyin jiki y fara daga kafa y tafi domin karasawa masallacin turus y tsaya sakamakon jin maroki na sanar da auranshi kamar haka an daura auran *umar Abdul/khadeer umar* tareda amaryarshi *Aysha aliyu umar* akan sadaki naira 50k lakadan ba ajalan ba ras2 dam daran dam kirjin Aslam y buga sakamakon jin sunan amaryar da aka daura masa aure da ita.

Cikin firgici yajanyo hannun Amir,yace kaji sunan yarinyar da aka daura aurannan kuwa kar daifa da aljanar yarinyar nanne,murmushi Amir yayi tunawa da abinda safwan y fadawa su daddy,amma yace anya bana tunanin da islam aka daura maka aure nafi tunanin mai irin sunanta ne,ajiyar xuciya Aslam kawai yayi amma xuciyarshi tana soko masa islam a matsayin matarsa,runtse idanunsa yayi saboda irin yadda xuciyarsa take tafarfasa,mutane sai xuwa sukeyi sunayi masa Allah y sanya alkhairi yake kawai yakeyi amma jinsa yakeyi tamkar y karma ihu,wata xuciyar ce tace haba Aslam a yadda iyayanka sukasan lalurar da kake fama da ita menene xai saka su aura maka wannan yar tatsitsiyar yarinyar da wannan tunanin yadan ware har aka tafi wurin reception amma kowa y kalleshi xai hanko tsantsar damuwa da firgici a tattare da Aslam,su safwan kuwa sai raba get pass na dinner din da xa'ayi gobe 8 o'clock.

Haka aka tashi a reception dinnan Aslam ko ruwa y kasa sha sai tsaki dayake ta jerawa yafi 1000,bakin da sukaxo daga nesa suka fara jigilar kaiwa masauki basu gama basu masauki ba sai 2 oclock kuma gashi 4 o'clock xa'ayi kilisa gashi daddy yanata kiran wayarshi yaxo yanason magana dashi.

Islam ce dasu khausar suna hira,cikin farin ciki domin islam ita tama manta da ana biki a gdan,saboda kwata2 basajin wata hayaniya,mommy ce ta shigo dakin cikin farin ciki ta kallesu,akwatunan lefe ta bude ta daukowa islam wani hadaddan takalmi milk color mai dan tudu hadeda mayafi shima milk tace my daughter xoki saka takalmi da mayafi dadynku na nemanki,islam ko a jikinta taje ta saka takalmin domin lokacin da mommy take debo kayan hankalinta baya gurin,tace mommy takalmin kuwa mai kyau tana washe baki,murmushi mommy tayi ta mika mata mayafin tace yafa muje ana jiranmu,islam ta karbi mayafin ganin ta yafashi y sauka harkasa shine y sakata yin dariya tace mommy ai yamin yawa kawai mutafi a haka,mommy tace a'ah yafa a haka muje cikin xumbura baki tace kawai ni mayafinnan xai batamin kwalliya suka futa.
Chapter 23 · 0% Book details