← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 61

Sashe 7

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A b'angaren Umma Karima da Siyama kuwa.
damuwa yataru ya dame su, Siyama ta dubi Aunty'n nata da duk nutsuwa ya kaurace musu ta ce
"Aunty Karima yanzu shike nan komai yatashi a banza shi ke nan, na kara narasa Abdulrahim a karo na biyu, na shiga uku ina zan sa kaina, ji nake kamar naje na kashe Feeryal sannan na kashe kaina kwa ya rasa gabad'an mu."
"Uhum nafiki shiga tashin hankali Siyama,
tashin hankalin da nake jina ciki yanzu yafi na lokacin aurenshi da Kuraiba,
sannan babban bakincikina ma boka ya gaza ganin su cikin kwaryar tsafinsa, bare yasan matakin da ya kamata ya d'auka a kansu,
wanan sinanniyar yarinyar wlh sai naga karshenki a duniyar nan!
yadda kike ta b'ata min shiri sai kin biduniya ba takalmi in zanyi yawo tsirara wlh sai na sa kin tsani kanki."

Hajiya na samin labarin shigowar kayan gidan tasa a kirawo mata Daddy.
Daddy ya shigo ya sameta a parlour'n ta.
bayan ya gaishe ta tayi masa ya jiki ya ce da sauki.
Hajiya ta gyara zama tana fad'in
"Naji labarin wai an kawo kayan d'akin da yarinyar nan, ashe kasan turawa ka aika aka siyo,
to ni dai damuwa ta karka mance da ko waye ita, kar ka zauna kayita wahalar banza a kanta, 'yar da ba wani asali take da shi ba,
tun da ka nace kace sai ka had'a ta da abokin turawa to shi ke nan ni dai ina gudun wani abun da zaizo ya biyo baya."
"Hajiya insha'allahu babu abin da zai faru sai alhaki, Allah dai ya wuce mana gaba."
Hajiya ta kawar da kai tana fad'in
amin.
Daddy ya yi saurin mikewa dan ya gano so take takuma b'aud'e hanya gara ya yi azama tun kan, ta karkace hanya...

Kiran wayar Mom d'in Kuraiba ce yashigo wayar Mommy.
Mommy ta d'aga da sallama gami da fara'a tana fad'in
"Hajiya Luba an wuni lafiya ya gidan."
daga cikin wayar Hajiya Luba ta ce
"Ina ko lafiya tun daga gidan ki rashin lafiya ya soma har zuwa gida na,
yanzu fisabilillahi Hajiya Halima irin sakayyar da d'anki zai mana ke nan,
a tun tarihin kawayen mu babu wata wanda aka tab'a mata haka, ace aure ko shekara baiyi ba d'anki ya kuma karo aure,
haba wace irin rayuwa ce wannan; ga shi tashin hankali ya haifar mata zuban jini tana da ciki, gata a kwance ta shigo min a firgice, haba Hajiya Halima taya za'ayi mana haka gaskiya baku kyauta mana ba."
Mommy ta ce
"Allah ya baku hakuri Hajiya Luba wlh wannan auren ba da son raina aka d'aura shi ba, nayi duk iya bakin kokari na ganin hakan baifaruba amma an nuna min fin karfi,
amma ina mai tabbatar miki auren nan babu in da zaije za'a watse dan wlh Abdulrahim bazai tab'a zama da yarinyar nan ba,
yanzu ina Kuraiba'n take Allah dai yasa cikin bai fita ba."
"Gata nan kwance tana numfarfashi a gaya masa yazo ya d'auke ta ya jinyata ciwon da ya sa mata,
kuma a gaskiya idan kika bar auren nan ya zaunu bakiyi mana adalci ba."
"Haba Hajiya Luba kar ki damu yarinyar nan bana kaunarta sam-sam a rayuwa ta, babu abun da zaisa na barta tayi zaman aure da d'ana, yanzu kuwa zaizo ya d'auko ta."

Mommy na kashe wayar ta lalub'o number Abdulrahim dan tasan yau weekend yana gida.
yana d'agawa ta ce yazo yanzu tana nimansa kada ya b'ata lokaci.
bai b'ata lokaci da yawa ba yashigo kiran Mommy.
tun kan ya zauna Mommy ta rufe shi da bala'i.
"Baku isa ku kunyatani kai da mahaifinka a cikin kawaye na ba, ga matarka can Kuraiba tana kokarin yin b'ari, ka fita kayi gaggawar zuwa gidan su kaje ka d'auko,
ka magance maysalar da ke kolarin aukuwa kada ka sake cikin nan ya b'are,
ina ga irin ta and'agawa yarinya hankali har ya kaiga tana kokarin yin b'ari, to wlh bazan yadda ba,
yazama dole a kiyaye cikin a hakura da abin da bata so,
akan karin banza auren aljana a halakamin jika wlh bazai sab'uba,
maza kaje ka d'auko ta yanzu."
kafad'a ya d'aga ya juya ya fita.

Hajiya Luba tayi ta zuba idon ganin sa shiru, takuma kiran Mommy,
Mommy tayi mamakin da taji ance bai je ba, duk da tasan hakan ba wani abun mamaki bane a halin sa.
tayi ta baiwa Hajiya Luba hakuri, daga karshe dai ita taje ta dawo da Kuraiba dan shi kam yaki zuwa.

Sashin Daddy Mommy ta wuce ta tarar da shiko zama bayiba ta ke fad'in
"Yanzu Alhaji kaji ka aminta auren nan sai an zauna sai Abdulrahim ya zauna da yarinyar nan,
mene ne ajikin auren wannan yarinya da kake so ka jonawa Abdulrahim ita,
yanzu gashi can damuwa nason sa cikin jikin Kuraiba zuba,
nifa ban aminta da auren nan ba z
bazai taba'a sab'uwa ba."
"Ke Hajiya Halima ki maida hankalin ki kada ki sake zuwa min da wannan shirmen,
d'ana ne ko naki? haka naga dama dashi,
idan baki dai-dai ta hankalin ki ba zaki iya kaucewa ki bamu guri a gudanar da komai lafiya, kar ki sake zuwa min da wannan zance."
"Au haka zakace ma Alhaji, to sai me ko mai ma kayi."
ta juya fuuu tayi waje.
Mommy tayi sashin Hajiya da kukan ta wai Daddy ya ce zai koreta ta akan auren, ga shi kuma
cikin Kuraiba na shirin fita sanadin damuwar auren.
Hajiya ta ce
"Ai ko bai isa ba sai dai in a fasa tarewar, dama Kuraiba'n tana da ciki ne, amma dai bai fita ba ko?
ikon Allah ashe dai tana kunshe da abun, ai yafi aure kusan shekara babu motsin ciki ai ba kanta,
jeki zan kira shi ai karma ya soma."

Kwana uku da shirya kayan Feeryal a side d'in Abdulrahim Daddy yasa su Ainty da goggo Bishira da Ammah suka shiga babban kasuwar su suka had'o wa Feeryal lefe.
kud'in da Daddy ya narka wajen had'o lefen Feeryal sai da ya baiwa Aunty tsoro.
kwana uku sukayi suna shiga kasuwa, inda gidan gaba d'aya ya d'auki zancen, masu habaici sunayi masu mugun fata sunayi.

Aunty zaune tana waya da Hajja Umma. Mommy ta b'ankad'o kofar parlour ta shigo.
tana bin Aunty da kallon banza tana fad'in
"Hajiya Fatima burinki ya cika kinyi kutun-kutun kin sa an jona d'ana da d'iyar tsintuwarki, tsintacciyar aljanar ruwa mara asali,
amma kisani har a gobe nice nan uwar da ta haifi Abdulrahim nayi nakudar sa nasan zafin sa, wanda har a gobe bakisan ya ake nakuda bare nishin haihuwa ba;
ina so na sanar miki cewa baki isa kisa ayi wani shagalin biki ba dan d'ana bazai jera da aljanar ruwa ba,
idan kuma kikace zakiyi to mu zuba mu gani, mttsss!."
taja dogon tsaki kana ta juya tafita tana banko kofa.
Aunty ta bi bayanta da kallo tare da sauke numfashi.
tana dad'a gyara rukon wayar da ke kunnen ta.
Hajja Umma dataji komai ta cikin waya itama ra sauke numfashi tare da fad'in
"Fatima Allah dai ya miki albarka da baki tanka mata ba, dama kin shirya wani shagalin biki ne a tarewan nata?."
"Aa wlh ban shirya komai ba Hajja Umma, ta daiyi tunanin ko hakan zai faru ne."
Hajja Umma ta ce
"Yauwa to kada ma ayi dan gujewa wani tashin tashina,
muma babu wanda zaizo daga nan idan Allah yasa ta tare Allah ya kawo rabo in da rai zamuzo suna, zamuyi musu fatan zaman lafiya daga nan, zamuyi ta tayaku addu'a Allah ya kad'e fitina."
Aunty ta ce "Amin ya Allah amma Hajja Umma ni dai zanfi jin dad'i idan na ganku kusa."
"Fatima kiyi hakuri bazai yuwu muzo a irin wannan halin da ake ciki ba, kar azo a b'ata goma d'aya bai gyaruba, 'yan'uwanki bazasu zuba ido ayi musu cinkashi su share ba, to maganin bari kar a soma, kiyi hakuri kawai zamu zo ai nan bada jimawaba idan Allah ya nufa."
Aunty ta girgiza kai kawai, sukayi sallama.

Da yamma Daddy ya shigo.
jikin Aunty ya yi sanyi san da Daddy ya sanar mata a karshen satin nan Feeryal zata tare.
Aunty ta dubeshi jiki a sanyaye ta ce
"Daddy beyi wuri ba baza'a bari a kara lokaci ba."
"Fad'imatu karki ce komai dan Allah kiyi musu addu'a da fatan alkhairi, bana so najinkirta, ina so nayi amfani da wannan damar ne kafin Hajiya takuma waiwayowa kan lamarin,
yadda taga naji saukin nan zata iya kuma tada bori ta ce bata amince ba."
Aunty ta girgiza kai
ta ce
"Allah yasa hakan shine mafi alkhairi."
"Yauwa ko ke fa amin ya rabbil izzati, shin kinshirya wani hidima ne Fad'imatu?."
"Aa babu abun da na shirya Daddy ayi addu'a a kaita Allah ya basu zaman lafiya."
kai Daddy ya jinjina tare da kuma amsawa da amin amin.

Miemie zaune da Feeryal a d'akin ta, Miemie ta b'ata rai tana fad'in
"Ni wlh naji haushin da akace babu wani shagali a auren nan ni da nagama hasasho yadda shagalin zai gudana,
Allah ban so ba."
Feeryal ta bita da ido dan ita da ido take kallon duk wani mai magana kan auren nata da har yau take ganin kamar karya ko mafarki.

Ranar da ya kasance rana ce da Feeryal zata tare a side d'ib Abdulrahim, ranar ta tsinci kanta cikin tashin hankali sosai. ranar wuni tayi sukuku daga bisani kuma tasoma kuka,
Aunty ta sunkuya rarrashi.

Abdulrahim ne zaune a parlour'n Mommy da tayi masa kiran gaggawa.
ta dube shi tana cewa
"To bawai kaga an kaima wancan kyalkyal banzan sashin ka, ka saki jiki da ita ba,
tun da ya matsa sai ka aure yarinyar nan, ka bud'e kunnen ka da kyau kajini,
kar ka soma gangancin kusantarta dan kyan d'an maciji ne gareta, kasan takunka idan ba haka ba wallahi sai ta fasa kai duk ta wasa mana dafin tsiya, kaji na gaya maka ke nan."
baki ya tab'e ya mike ganin ta gama maganar nata ya yi gaba.
Chapter 7 · 0% Book details