← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 61

Sashe 52

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sarki Al'Ayzaan ya yi wa su Aunty da Daddy godiya sosai da suka zame mata uwa da uba,
batare da sanin wace ce itaba.
ya ce ikon Allah ne ya jefo ta Nigeria, ta fad'a a hannun su mutanen kwarai, uwar da ta raine ta bata san cewa d'iyar d'an uwan ta ba ce ita.
ya kuma bukaci Uncle Aliyu ya zo musu da ita, domin taga dangin mahaifiyar ta.

kowa ya cika da mamaki da al'ajabi, Daddy bakin sa ya kasa rufuwa sai fad'in
"Alhamdulillah Alhamdulillah."
yake, Abdulrahim yana tsaye daga bakin kofa.
Hajiya Mommy Mom Ammah da sauran mutane kowa na tsaye da d'in bin mamaki.

Feeryal na tsaye sai gani akayi ta yanki jiki ta fad'i kasa.
salati parkour'n ya d'auka har da su Sarki Al'Ayzaan da sauran mutanen da suke tare da shi,
suke kallon abun da ke faruwa ta cikin waya.
wani irin d'ago kafa ya yi ya karaso cikin parlour'n,
yana isowa kanta da sauri cikin wata iriyar murya na maza ta ce
"Aa Garkuwar god'iyar mu, mu ba macuta bane kuma bamuzo dan mu cutar da ita ba,
hasali ma mune masu bata tsaro a lokacin da baka tare da ita Garkuwa,
munzo ne don mu fayyace duhun da ya shigewa kowa cikin lamarin b'atar god'iyar mu a lokacin da take jaririya,
sunana Waziri Kutup nine Wazirin Sarkin Aljanu."

A wani karni shekaru masu tsawo alokacin da zalunci ya yawaita,
baga bil'adama ba ga jinnu ba.
ta ko wani fanni zalunci ya yi yawa,
kwasam aka haifo shugaba Matip ya taso da farar zuciya, yaci burin gyara al'umman sa,
ya yi yaki da karfin sa wajen ganin azzaluman aljanu da wad'an da suke baiwa jinsin bil'adama bokaye da matsafa sa'a,
wajen yin bokanci da tsubbace-tsubbace masu surkulle da 'yan bori, ya rushe sansanin su da karfin izzarsa.
yasa kowa ya rusuna bisa gwaiwowin sa, dan dolen su sukayi murabus da zaluncin da suke yi, cikin jinsin mutane da 'yan'uwan su aljanu.
ya shafe babin azzalumai aka daina zalunci, ya zame mana sarki.
tun daga lokacin adalci ya wanzu kwasam bayan shud'ewan wani lokaci.
aka sami munafukin shaid'ani daga cikin masarautar ashe ya dad'e yana munafurtar sarki Matip,
ya kafa sansanin sa a gefe batare da sanin sarki ba,
ya jone da bil'adama bokaye da matsafa, suna zalunci a bayan fage.
da labari ya zowa sarki Matip yasa aka hukuntashi sannan aka koreshi a fada, dama hukuncin duk wanda aka kama da laifin zalunci ke nan.
yana barin fada ya je ya kafa sansanin sa in da ya rika jan ra'ayin wasu daga cikin mu duk suka tattara suka koma karkashin sa,
kafin wani lokaci ya tattara kusan rabin fada da iya makircin sa,
daga nan ya nad'a kansa a matsayin sarkin bakaken aljanu,
ya fara wanzar da zalunci, cikin Aljanu da mutane,
ya baiwa bokaye lasisin cin karen su ba babbaka zalinci ya wanzu.
kafin wani lokaci yayi karfi fiye da sammani ya zamo shine mai fad'a aji,
fadarsa tayi karfi fiye da tunani.
a lokacin ya shirya yaki da sarki Matip ya shiga fadarsa da mayaka suka yake mu, aka karkashe da yawa daga cikin mu in da wasu kuma da yawa sukayi mubaya a suka koma bayansa, wasu kuma suka sami nasarar gudu subar gurin,
daga nan ya shiga yakama sarki Matip da ni wazirinsa ya sa aka d'aure mu, ni aka jefani a kurkuku,
Sarki Matip kuma akayi masa kejin karfe mai tsananin karfi, wanda in duniya zasu taru bazasu iya b'allashi ba,
kejin da aka kerashi da manya-manyan matsafa aljanu da mutane aka tsafe kejin karfen,
wanda bashi da makari sai abu guda, hawayen jaririya macen bil'adama 'yar baiwa mai idon ganin wasu jinsin da ba iya jinsin mutane ba,
shine kad'ai makarin sa,
da zai iya bud'e kejin karfen,
sai idan jaririyar tayi kuka hawayen ta ya d'iga a jikin kejin daga nan kejin zai bud'e.
aka d'auke sa aka jefashi a tsakiyar tekun Matip tsawon shekaru dari uku, Sarkin bakaken aljanu ya ke shinfid'a mulkinsa yadda yaga dama.
sai da nayi shekara d'ari uku a kurkuku sannan aka sake ni a matsayin bawa,
mai bautatawa fadar sarkin bakaken aljanu.
kwasam wata rana ina cikin aiki a fad'ar na tsinci maganar bakaken aljanu da mabiyansa wanda suke kusa da shi sosai,
da kuma bil'adama bokaye, suna cewa sunyi bincike sun gano an haifo irin yarinyar da zata iya kub'utar da Sarkin Aljani Matip,
'yar baiwa da Allah ya halitta mai iya ganin jinsin da ba nata ba kad'ai, suka kuma tabbatar da cewa sun gano kasar da aka haifeta,
dan haka zasuje kasar domin bincikota, su kashe ta kafin ta zame musu matsala, dan sun san idan sarki Matip ya kub'uta bazai kyale su ba.

Tun da naji labarin a ranar na zurfafa bincike har na gano a kasar Lebanon aka haifo ta,
washegari aka tura dakarun bakaken aljanu domin su je su d'auko ta,
ni na rigasu tafi.
tun da aka gano na gudu a fadar aka tura dakaru nima na,
akayi ta jefa kifiyar tauraru tana sukana,
mutuwa ce kad'ai banyi ba amma nasha wuya sosai kafin na isa ga in da take,
dan naci alwashin sai na kub'utar da ita daga zalincin su, sannan na kaita ta taimaki shugaban mu.
na sauka a gidan su na d'auke ta tare da sarkar masarautar mahaifiyarta domin na tabbata komin daren dad'ewa zata had'u da danginta,
ta sanadin lu'ulu'un masarautar su,
na had'a da hoton ta na sakata a kwando na tafi da ita.
ina fita na bayyana a babban tekun Bahar Rum.
na tafi ta sama har na shigo kasar nan na sako ta a dai-dai tsakiyar tekun Matip,
in da yake d'aure a karkashin tekun, ta isa kasan tekun taje ta ceto shugaban mu,
shugaba bai barta ta halaka ba a lokacin data ceto shi, aka fito da ita sararin duniya."

Sanda Waziri Kutup ya kawo nan
Abdulrahim cikin b'acin rai ya damki wuyar ta yana fad'in
"Da kun sa ta mutu fa! ina ruwan ta da lamarin ku ita tana mutum ku kuna aljanu, kuje ku magance lamarin ku mana!."
Waziri Kurup ya yi dariya ya ce
"Haba Garkuwa d'an sassauta rukon,
da mun barta ai da dakarun sarkin bakaken Aljanu sunje sun kasheta,
a cikin ruwan da muka barta tana yawo ai ba ita kad'ai bace a rike a hannun yaran mu take,
bazasu bari komai ya same ta ba, duk da muna da tabbacin zata fuskanci kalubale a duniyar nan,
dan munsan sarkin bakaken Aljanu bazai kyale ba,
bamu barta ita kad'ai ba kullum a cikin bata tsaro muke,
ko kuda bamu yadda ya sauka a kanta dan cutar da ita ba,
kwasam binciken mu ya gano mana kai, ta hanyar jefa taurarun bincike,
muka gano wasu tarukan baiwa a tare da kai,
da tabbacin kaine Garkuwar ta
har lokacin da ka bayyana a gareta, hakika kai Garkuwa ne a gareta tsaron ka a kanta yafi namu, domin kai d'in Garkuwa ne,
kana da wasu sirrukan da kai kanka baka san kana da shi ba, kai d'in daban ne acikin mutane."

Fuska ya murtuke ya ce
"Babu ruwan ku da wannan ku kauce ku bamu guri, kar ka sake mu kara gamuwa."
"A gafarce mu Garkuwa."
tana fad'in haka ta sauke wasu tagwayen atishawa jikin ta ya sake.
parkour'n ya kacame da hayaniya.
acan fadar Sarki Al'Ayzaan kuwa da suke biye da wayar suna ganin komai ta cikin waya,
Uncle Aliyu ya sanar musu abunda ya faru da harshen larafci,
suma suka cika da al'ajabi.......!

Rasheedat S Director
Mommyn Twins ce🤙🏻

Kowa yacika da d'in bin al'ajabi.
Allah ke nan buwayi gagara misali, su Hajiya jiki ya dad'a sanyi hakika sarki ya tabbata ga Allah.
su Ameerah kowa sai ido wacce ake ta wa gori a baya ita ba kowa ba, sai gashi tayi musu fintinkau.
jinin larabawa jinin sarauta uwa da uba hamshakan masu kud'i.
Mommy ko sai sunkiyar da kai kunya ya dad'a lullub'e ta.
kowa ya watse da al'ajabin abun.

Tuni labari ya isarwa su Abban Abuja da Hajja Umma, Feeryal 'yar Uncle Aliyu ce, farincikin su bazai fad'uba.
ashe jinin su ce ita shiyasa suke jin ta a cikin ransu.
labari ya zaga dangin su gaba d'aya, sukayi murna sukayi farinciki mara misaltuwa.
a ranar Uncle Aliyu ya koma Abuja wanda ya so tafiya da Feeryal a ranar Abuja sabo da su wuce Lebanon ya kaita wa dangin mahaifiyarta kamar yadda suka bukata.
Daddy ya ce ya bari ta shirya tukun ana gobe zai koma zataje Abujan ta same shi sai su wuce.
Chapter 52 · 0% Book details