Sashe 22
Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Aunty ta koma d'aki in da Feeryal take da sauri.
ta jika towel tarika share mata jiki dan zafin ya ragu.
ya d'au tsawon minti 20 kafin ya shigo, kansa a kasa.
Aunty na ganin sa ta mike tana fad'in
"Bacci ya d'auke ta amma jikin har yanzu da zafi, inaga ko sai anyi allurar zaiyi sanyi."
kai kawai ya jinjina batare da ya bari sun had'a ido da Aunty ba.
lura da yadda yake ta sunkuyar da kai Aunty ta fita a d'akin ta janyo kofar.
a fili yaja numfashi tare da furzar da huci cikin bakin sa, kana a hankali ya tako bakin gadon idanunsa akanta.
tana kwance tad'an dunkule cikin bargo, idanunta da suke a lumshe duk a kukkumbure,
fuskarta ya kara haske alamun tana jin jiki da zazzab'in.
kuma duk ya d'an sussunduma na kukan da ta sha jiya da daddare.
janye idanunsa ya yi a kanta kana ya d'au laidar da magani da alluran suke ciki, ya had'a allura syringy biyu sanna ya janye bargon gefe,
tana sanye da riga mara nauyi iya guiwa.
ya d'an dad'a matsowa, yaja rigar sama wandon rigar mai kama da pant ya bayyana.
ba shiri ya rumtse idanunsa jin yadda kirjinsa ya yi wani irin bugawa.
sai kuma a hankali ya ware idanun a kanta da d'an sauri ya kai hannu ya d'an janye wandon kasa kana ya saita allurar ya nitsa mata.
zabura tayi tana kokarin mikewa yayi saurin masa ruwar allurar kana ya zare.
kara ta sake tana mike wa zaune.
tana yin ido biyu da shi tawani irin zabura dayafi wanda tayi san da ya saka mata allurar, tana binsa da kallon tsoro.
d'aya allurar ya d'auka, yayi mata alama da hannu ta matso, da sauri takuma yin baya tuni idanunta suka kawo kwalla,
murya na rawa ta ce
"Kayi hakuri Sahab dan Allah kar kayi min."
fuska ya gimtse tare da zama bakin gadon, ya fisgota jikinsa ya matseta, kara ta sake tana kokarin kwace jikinta ya dad'a rungume ta da kyau, sai da yayi mata ya mulmula gurin kafin ya saketa.
ta masa can kuryar gado tana toshe bakin ta da kuka ya kwace mata.
ido ya zuba mata itama shi take kallo da idanunta da suke tsiyayar da kwalla masu cike da tsoron sa.
ya mike yafice a d'akin yana fita Aunty ta shigo da sauri ta hayo gadon tayi mata pillow da cinyarta, ta shiga rarrashi.
"Yi hakuri Feeryal jikin ki yayi zafi dole sai allura ce zata sa jikin tayi sanyi, sannu kinji Allah dai ya baki lafiya yayi miki albarka."
ita dai sai masar kwalla take,
idanun ta a lumshe takasa iya bud'e su dan jiri take ji.
zuwa can kuma bacci ya yi gaba da ita..
bara farka ba sai daf magriba, zuwa lokacin kuwa jikin nata yayi sanyi zazzab'in ya sauka.
ko da Aunty ta riketa zasu shiga bathroom tafiyarta ba irin ta d'azu ba, dan kuwa hatta zafin da take ji a kasanta yarago sosai.
da kanta tayi wanka ta d'auro al'wala ta fito.
Aunty bata d'akin bayan ta gyara mata d'akin saf ta tafi kitchen dan sama mata abun da zata ci.
kayan da Aunty ta aje mata shi bakin gado ta d'auka ta saka, shima kamar irin na d'azu ne rigar iya guiwa da wandon sa mai kamar pant, kana ta saka babbun hijabi har kasa ta haye kan
sallaya ta tada sallar magriba da taji an shiga a masallaci.
tana idarwa Aunty na shigowa rike da tray ta dire shi gabanta.
plt biyu ne kan tray'n sai cup.
d'aya perpesun zabbin da hajiya ta kawo mata ne ta d'uma ta d'ibo mata, d'aya kuma mutumin ta ne cake, sai tea mai kauri a cikin cup d'in sai kuma gorar yogurt mai masakaicin sanyi.
Aunty ta ce
"Cire jibab d'in maza ki ci sai kisha magani, kinji 'yammatan Ammie."
batayi musu ba ta cire dan tana jin yunwa.
zatafa cin cake d'in Aunty ta ce aa tafara shan tea sai taci perpesun kafi cake d'in.
d'an kad'an tasha tea ta aje. tad'au cokali ta d'au d'an madaidai cin naman ta kai bakin ta.
ido ta waro cin yaji ya gauraye mata baki, tana kokarin fito da shi Aunty tace
"Maza ci kar ki fito da shi."
da kyar ta tauna ta had'iye da kyar tana yarfe hannu da kwab'e fuska
"Ammie yaji ni dai na ko shi."
"Aa Feeryal d'an kara ko kad'an ne."
"Ammie da yaji sosai fa."
"Eh nasani Feeryal kad'an zaki kara."
da kyar ta lallab'a ta taci yanka uku har tana hawaye, Aunty ta ce to ta bari taci cake d'in ta, ta barta nan tatafi domin yin sallah.
tana gamawa ta mike taje bayi ta wanko hannnu ta fito.
ido ta ware cike da murnar ganin su, sai kuma ta gwab'e fuska.
Chuchu da Chulu suka bita da murmushi.
ta karaso ta zauna bakin gado in da suke zaune tana cigaba da kwab'e fuska.
Chuchu ta dafa kafad'ar ta tana cewa
"Laifin me mukayi ake fushi da mu?."
baki ta cuno tayi raurau da ido sannan ta ce
"Ba kunce zaku taimake ni idan zaiyi min mugunta ba, amma ai baku zo ba."
Chulu ta dafa d'aya gefen kafad'ar ta tace
"Tuba muke a wannan lokaci bamu isa mu kawo kanmu gareki ba, ko da muka ganki cikin tashin hankali shugaba ya kwab'e mu da sake waiwayan ki, dan aiwatar da hakan zunubi ne a gare mu, har idan kina tare da Garkuwar."
raurau tayi da ido tuno da zillar data sha jiya a hannunsa ta ce
"Shifa mugu ne bayi da imani kuma baya jin dan Allah."
murmushi sukayi mata kana suka sako mata wata hirar.
ko da Aunty ta shigo taga tana magana ita kad'ai fita tayi ta bata guri.
sai da sukaji an shiga sallar isha kafin suka tafi.
itama ta mike taje ta gabatar da sallah.
bayan tayi shafa'i da wuturi tayi addu'a kana ta mike ta nad'e sallayar tare da cire hijab d'in ta aje su. tana kokarin zama aka turo kofar ta d'ago tana fad'in
"Ammie.."
da sauri ta had'iye abun da take shirin fad'a ganin shi ne, tayi baya da sauri tana binsa da kallon tsoro.
ya tako a hankali har zuwa gaban ta, kana ya mika hannu ya janyo ta jikin sa.
idanunsa dake rikitata ya zuba mata yana rike da ita batare da ya saketa ba,
ya kai d'aya hannun sa kan goshinta ya gangara zuwa wuyan ta.
zafin jikin ya sauka sosai.
ya cire hannunsa a wuyanta ya zura cikin aljuhunsa, dad'a mannata ya yi da jikinsa, kana yayi kasa da hannunsa ya kamo kasan rigarta ya yi sama da shi.
da sauri tayi kokarin janye jikinta kirjinta na bugawa, ya dad'a mannata da kyau a jikinsa ya zagaye ta da hannayen sa, sannan ya d'an ja wandon jikinta ya soka mata allurar.
kara ta kwalla tare da kankameshi tana cusa fuskanta cikin kirjinsa.
bata sammaci allurar ba dan bata ko gani a hannunsa ba.
Aunty ta sako kai da sauri cikin d'akin jiyo ihun ta, ganin sa rungume da ita, ta juya da sauri tayi baya bata bari ya ganta ba, sam bata san da shigowar sa ba.
a hankali ya zare allurar yana mulmula gurin.
lamo tayi a jikinsa tana jan sheshsheka hawaye na gangara, tana jiyo bugun zuciyarsa da sauri-sauri. a hankali take shakar kamshin dake fita da kirjinsa,
gyara kanta tayi tana dad'a manna fuskarta da kirjinsa.
tana jin wani d'umi yana rasata har tana lumshe idanu tana jin wani bacci nason d'aukarta.
kamar an zabure ta ta zare jikinta ta matsa gefe tana kwab'e fuska da cuno kyakkyawan lips d'in ta gaba.
bayan hannunta ta kai ta na share hawayen fuskanta, tana mai dad'a cuno baki gaba,
tana kuma jan shashsheka.
a sannu ya juya yafice a d'akin,
ta zube bakin gado tana jin wani sanyi na shigarta, da sauri ta kwanta taja bargo ta rufe jikinta.
Bayan fitarsa Aunty ta shigo idanunta a lumshe bacci na son d'aukar ta.
ta bud'e lumsassun idanunta tana wani kwab'e fuska kamar zatayi kuka ta ke fad'in
"Ammie kice ya daina min allura bana so akwai zafi."
Aunty tayi murmushi tare da shafa kanta ta ce
"In ban da abinki 'yammatan Ammie ai sauki ake son sama miki, ke ya kika ji karfin jikin ki, na yanzu da d'azu kafin ayi miki na farko, kiyi hakuri in kika sami sauki ai baza'a miki ba, ana yi ne don lafiyar ki."
"Ammie akwai zafi fa."
ta fad'a murya a shagwab'e.
Aunty ta kuma shafa kanta ta ce
"Ai zafi shi ke cire zafi, idan kin warke shike nan, ke dai ki daure."
lumshe idanun takuma yi da take jin su suna shirin rufewa da kansu, allurar yafara tasiri a jikinta.
ai kuwa take bacci ya d'auke ta.
Aunty ta fice ta ja mata kofar bayan ta tofe ta da addu'o'i.