← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 61

Sashe 26

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar da Maryam tayi arba'in,
da kwana biyu suka shirya da Feeryal zuwa kasuwa.
direba ne zai kaisu suka fito, Feeryal na rike da jaririn daya ciki sunan baban Nasir ana ce masa Aiman.
direba yajasu zuwa kasuwa.
suna tsakiya da yin sayayya Feeryal ta rumtse idanunta da karfi jin yadda kanta yayi wani irin masifaffen tsarawa.
sigar jikinta ya tashi.
da sauri ta bud'e idanunta jin wani irin sauti mai gauraye da maganganu na tashi a can cikin kunnuwan ta.
ta ware idanun nata kan wasu samaruka uku dake tsaye gefe suna duba kaya,
da karfi ta kankame Aiman dake rike a hannunta duk suka juyo suna kallon ta,
sikar jikinta yakuma tashi tana jin sautin na dad'a karuwa cikin kunnuwanta,
jikinta ya d'auki b'ari gaba ki d'aya jikin ta kyarma yake.
dafa Maryam tayi cikin mashahuriyar tsoro ta ce
"Aunty Maryam kiga wad'an can suna kallo na, zo mu tafi gida."
Maryam ta juyo ta ce
"Ina suke Feeryal."
da hannu tayi mata nuni ta ce
"Gasu can Aunty Maryam zo mu tafi!."
tayi maganar cikin matukar tashin hankali, jikin ta na kyarma.
Maryam ta yi saurin karb'ar Aiman dake shirin fad'uwa a hannunta ta ce
"Ni ban ga kowa ba ai babu mai kallonki kowa harkar gaban sa ya ke, ki natsu mana Feeryal."
baya tashiga ja idonta a kansu,
dai-dai kafad'un su take ganin wani jan haske kamar wutan kendir ke ci a gurin.
kamar yadda suma kuke kallon dai-dai saitin goshin ta da wani haske ke fita da kad'an kad'an yana zagaye tsakiyar goshin nata kamar nannad'in mantega.
da gudu ta juya ganin suna dumfaro in da take,
tana sa gudu suka biyo ta a guje......!

Babu editing

Da iya karfinta take gudu bata ko kallon in da take jefa kafarta,
tana waigen su tsoro tashin hankali su suka bayyana a gareta.
tamkar hankalin ta zai bar jikin ta sabar tashin hankilin da take ciki.
Maryam da ta biyo ta tana kiran sunanta hankali tashi, Maryam ta saka ihu ganin tasa kai zata sallaka titi, batare da tsayuwa duba titin ko jiran ababen hawa su wuce ba.
karan ababen hawa kake ji suna taka burgi.
jama'a sai d'aura hannu suke a kai suna salati.
wani irin burki wata moyar da tayi daf da ita tayi,
duk da haka sai da gaban motar ya tureta ta zube kasa.
da sauri ta mike a zabure ganin sun dumfaro titin, ta karasa sallake titin da gudu a kid'ime ta yi bayan wata mota dake pake gefen titi.
tab'oye jikin ta na kakkarwa.
tarika rab'ewa jikin motar tana tafiya da gefe da gefe.
yana zaune cikin motar gaban wani shago yana jiran Dr Imran daya shiga shopping cikin shagon.
tun ihu da salatin mutane ya maida hankalin sa kan titin, sai dai sam bai lura ya gane ko wace ce ba, sai yanzu da yake kallon ta ta cijin
glass d'in motar.
kamar gilmawar walkiya suka ketaro titin wani igigitaccen kara ta sake ganin sun bayyana a gaban ta.
da karfi cikin zafin nama ya bud'e motar,
dai-dai sanda tayi baya luuu zata zube kasa ya yi saurin rukota ya janyo ta jikinsa.
da karfi, hannu ta shiga nunawa tana fad'in
"Gasu nan sun biyo ni, bana son ganin su ina jin tsoron su!."
hannunta ya sake jikin ta ya sake gaba d'aya,
idanunta ya rufe.
da sauri ya d'ago yana duban in da take nuna masa, bai ga kowa ba.
da sauri ya ciccib'e ta ganin hankalin mutane yafa dawowa kansu.
ya bud'e mota ya shinfid'a ta a sit d'in baya, kana ya dawo mazaunin direba da karfi ya figi motar.
Dr Imran daya fito da kaya niki niki a hannunsa ya bud'e baki yana kallon yadda ya figi motar.

A bakin wani katafaren had'ed'd'en gida yayi hon,
aka wangale mata get.
yasa kai ya shige ciki, a farfajiyar gidan ya yi parking, ya bud'e ya fito da sauri kana ya bud'e gefen da take ya ciccib'o ta ya yi ciki da sauri da ita.
kai tsaye bedroom ya wuce da ita ya shinfid'a ta a kan gado.
kugu ya rike yana kallon fuskarta da idanunta suke a lumshe.
numfashi ya fesar kana ya juya har yakai kofa zai fita, yaji ta yi wani irin gurnani.
da sauri ya juyo, tayi wani irin mikewa ta fincike d'ankwalin kanta ta yamutsa gashin ta dayake a tsefe ta kuma yamutsa shi tare da girgiza kan.
ta duru a gadon tana kokarin rufawa a guje.
da karfi ya tako ya dawo da baya, ya damko hannunta.
ihu ta kuma yi ta fizge hannunta ta d'aga kafa zata kuma sa gudu.
ya kuma damko ta ya d'au ke ta da wani irin gigitaccen mari da sai da ta kife kasa.
har sai da gefen bakin ta ya fidda jini.

Ta d'ago tana wani irin kecewa da dariya, da wani irin murya mai fidda amon sautin muryoyi daban daban har kala uku.
"Hahahahaha yau ba makawa sai mun tafi da ita, tun da muka samo ta."
ta mike yayi saurin rigata isa jikin kofar,
ya rufe tare da murza key ya zare key'n ya jefa cikin aljuhun wandon sa.
da wata irin murya take fad'in
"Tun da muka samo ta dole zamu tafi da ita, shekaru masu tarin yawa muke jiran zuwan wannan rana,
tun ranar da muka sami tabbacin zuwanta duniya muka d'aura d'amarar samo ta,
mun zaga duniyar nan muna niman ta,
an baza mu ta ko ina dan nemo ta, tun da muka samo ta dole mu tafi da ita, mu karb'o kambun karramawa, dan mu mukayi nasarar samo ta,
muna da hanyoyin fita da yawa basai ta kofar can ba."
ta yi wani mikewa da karfi cikin b'acin rai ya sa mata kafa ta zube kasa.
wani irin ihu gami da hargagi tayi, ta d'ago tana binsa da wani irin kallo da kwayar idanunta suka sauya isuwa wani kala na ban tsoro.
mari ya d'auke ta da shi cikin fusatacciyar murya ya ce
"D'auke idanun ku a kai na!."
kururuwa ta sayi tare da birgima a kasa tamkar wacce aka zubawa ruwan zafi a jiki.
tana fad'in
"Kai bil'adama karka sake dukan mu da wannan hanun naka,
mai kamada garwashi, idan ba haka ba zamuga bayan ka."
bata rufa baki ba yakuma d'auketa da mari,
ihu ta kuma tana birgima da maganganu barkatai da muryoyi daban-daban.
ayoyin alkur'ani ya soma karantawa yana tufa mata, tuni jikin ta ya d'auki rawa tana.
tana fad'in
"Ka dai na kona mu ka daina kona mu, bazamu fita a jikinta ba har sai mun kaita ga sarkin bakaken aljanu,
bazamuyi asarar shekara da shekaru muna neman ta mu same ta yanzu mu kasa tafiya da ita baaaa, ka dai na kona muuuuu!
bazamu janye baaaaa sai mun tafi da itaaaaa!."
ta zabura zata mike ya shako wuyanta tare da taka kafafunta da nashi kafan.
sannan yaci gaba da tofa mata ayoyin Alkur'ani.
wan da tuni jikin ta ya shiga kakkarwa, tana kokarin janye hannunsa a wuyanta ta kasa.
nan da nan zufa ya shiga tsastsafo mata.
ko wani hudan gashi na jikin ta, fita yake da zufa hatta daga cikin gashin kanta kuwa zufa ne ke gangarowa zuwa fuskarta.

Da kyar ta iya bud'e baki cikin muryar jin azaba suke fad'in
"Zamu fita zamu tafi ka dakata kada ka kashe mu, mun rantse maka zamu kauce a jikin ta."
a fusace ya ce
"Fita zukuyi duka a jikinta ba kaucewa ba! idan kuka sake muka kara karo da ku to na rantse muku da girman zatin Allah sai na kashe ku! kada ku sake tunanin dawowa jikin ta, idan kuka kuma sai na kashe kuuuu!!."
yayi maganar cikin karaji sosai mai firgita kunnuwan duk mai saurara.
kai take gyad'awa ba kakkautawa tana fad'in
"Mun rantse munyi alkawari duk randa muka kara dawowa ka kashe mu, sakar mana manumfasa zamu tafi, zamu fita a jikin ta bazamu sake dawowa ba mun d'au alkawari, hannunka akwai garwashi ka sake mu zaka kashe mu, zamu fita zamu fita."
ya sake mata wuya yana binta da mugun kallo, da karfi ta saki tawayen atishawa sau uku a jere jikinta ya sake ta sulale kasa.

Ya mike tsaye yana jan dogon tsaki, ya gyara zaman rigarsa.
ya sunkuya ya d'ago ta cak ya nufi cikin bathroom da ita.
cikin bathtub ya direta,
a sannu yashiga zare kayan jikinta,
ya tub'e ta tsaf batare da ya cire bra da pant d'in jikin ta ba.
yana tallafe da ita, yana daga wajen bathtub d'in.
kana ya soma tara ruwan d'umi cikin bathtub d'in.
nannauyan numfashi ta sauke jin d'umin ruwan na rasa ta, ta juya kai ta dad'a manna kanta jikin hannunsa kamar jaririya a hannun uwanta.
a hankali take sauke numfashi.
ido ya kurawa fuskarta bacci tayi a hannunsa.
d'aya hannun nasa ya saka cikin ruwan ya d'iba ya wanke mata fuska yayi hakan har sau uku.
kana a hankali yakai hannunsa zuwa bayan ta, ya b'alle mab'allin bra'n jikinta ya zare shi yana kauda kai da ganin ta.
sannan ya cirota ya had'eta da kirjinsa ido ya rumtse jin zuciyar sa ya buga.
a sannu ya ware idon akan ta, da sauri ya d'auke kai daga kallonta.
ya zaro towel ya nad'eta da shi,
yafice a bayin da d'an sauri ya karasa bakin gado ya kwantar da ita.
ya janyo blanket ya rufeta yasa hannu ta cikin bargon ya zaro pant d'in jikinta, da yake a jike.
ya ajiye shi nan bakin gadon kana ya juya ya nufi kofa ya zaro key cikin aljuhun sa ya bud'e kofar ya fita.
Chapter 26 · 0% Book details