← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 61

Sashe 3

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da gudu Miemie ta shigo sashin Aunty ta wuce dakin Feeryal.
Feeryal tana kwance a bakin gado tana buga game, Miemie tayi tsalle ta haye gado tana tsallen murna had'i da rangad'a gud'a.
cikin muryar dariya da farinciki sosai take fad'in
"Kai gaskiya wannan had'i ba karamar dacewa tayi ba, wlh na jima banyi farinciki irin na yau ba,
ayyiririii Feeryal amaryar Ya Abdulrahim."
da sauri Feeryal dake binta da dariya ta waro ido tare da fad'in
"Ke Miemie rufamin asiri babu ruwa na, ko me irin sunan Sahab ma babu ruwa na dashi bare wannan Sahab mugun, ki raba sunan mu kar ki sake had'awa."
tayi maganar tana turo kyakkyawan bakin ta.
Miemie ta zauna ta kalmashe kafa tana cewa
"Ke dalla matsa can, kuma shi Ya Abdurrahim da kike ganin shi babu ruwan shi yana da saukin kai sosai idan ba wai laifi kayi ba babu ruwan shi da kai."
"To ni ina ruwana ma da shi, yayanku ne ai ba Yaya na ba."
tayi maganar tana dad'a cuno baki."
Miemie ta bigi kafad'ar ta cikin muryar zakuwa da son fad'in maganar dake missinin ta ta ce
"Ai ko ke kike da ruwa da shi tun da yanzu ya zama ango."
shigowar da Aunty tayi ne yasata maida hankalin ta kan Aunty.
Aunty ta kira ta da hannu tana cewa
"Zo FEERYAL Daddy na niman ki.......!

Mommyn Twins ce

Feeryal ta mike Aunty ta ruko hannun ta suka fita.
a bedroom d'in Aunty suka tadda Daddy zaune, Aunty ta zauna gefen sa ita kuma ta zauna kasa kan carpet.
Daddy ya bita da murmushi yana cewa
"Anyi breakfast kuwa Feeryal?."
"Nayi Daddy."
ya ce "Badai cake da Yogurt ba ko, an d'an tab'a abu mai nauyi"
"Daddy nasha tea da chips."
ta fad'a da murmushi kan kyakkyawar fuskarta.
Daddy ya jinjina kai tare da gyara zama ya d'an yi gyaran murya sannan ya ce
"Feeryal magana nake so muyi dake a matsayin uba a gare ki nake so ki fiskance maganar,
a karancin shekarun ki nasan kin san abubuwa da dama dan rayuwar gidan nan makaranta ce a gare ki."
ya d'an numfasa sannan ya cigaba
"Feeryal na yanke hukunci a kanki batare da niman amincewar ki ba, sai don ina gadara da iko na uba a gare ki,
inaso ki sani duk wata 'ya hakki ne akan uba ya nima mata abokin rayuwar daya cancanta da rayuwarta,
shiyasa na zab'a miki wanda nake ganin shi ya dace yakuma cancanta da rayuwar ki, ki natsu da kyau ki saurare ni,
Feeryal na yanke hukunci a kanki batare da ni man amincewar ki ba, a yadda kike d'in nan aure shine rufin asirin rayuwar ki, shi yasa na zartar da hukun ci, kanin mahaifina wanda shine a matsayin uba a gare ni,
bani da uban daya fisa a yanzu shima ya zartar da hukunci nan take,
Feeryal an d'aura miki aure da Abdulrahim,
da na zab'ar miki shi a matsayin miji, ina fata bazaki kalli lamarin dawata fuska ba,
sai da fuskar da kika taso cikin sa, wato kallon mu mahaifan da muka haife ki."
da sauri ta d'ago tare da waro manyan idanunta.
"Sahab!." ta furta a kan labbanta, soro mai had'e da fargaba ya bayyana a kan fuskarta.
Aunty ta kura mata ido tana son karantar yanayin ta.
Daddy ya jinjina kai kana ya ce
"Hankali na ya kwanta dana aurar da ke,
ina da yakinin mijin dana aura miki zai kula da ke,
Allah ya yi miki albarka kicigaba da hakuri da rayuwa, kamar yadda kika saba, ki toshe kunne kiyi kamar bakyajin duk wani abun da zakiji,
wata rana sai labari tashi kije Allah ya miki albarka,
kar ki sawa ranki damuwar komai babu komai."

A hankali ta mike tana nanata kalaman cikin kwakwalwarta, abin kamar almara yake zuwar mata.
har ta fita ta shige d'akinta nutsuwa bai dawo gareta ba.
Miemie na ganin ta tawashe baki tana fad'in
"Iye kaga amaryar Dr AA FIYA wlh ni yau wani dad'i had'i da dad'in kallon ki nake ji, kinsan fa haka amarya take ko kullum tare kuke kwana kuke tashi ranar da akace tazamo amarya, to daga ranar ta zame maka sabuwa, kallon ta baya isar ka."
Miemie ta kwashe da dariya tana cigaba da zolayarta.
a hankali ta zauna bakin gado jiki a sanyaye.
ta dubi Miemie tayi rau-rau da ido ta ce
"Miemie wai dama da gaske ne maganar da kike?."
"Au dama baki sani ba wai Feeryal?."
kai ta gyad'a sai ga hawaye sharr.
Miemie ta ce
"Ai kuwa ba gidan nan ba hatta dangin da suke nesa labari ya isar musu, gaskiya Feeryal ke mai sa'a ce, samin miji irin Ya Abdulrahim ba karamin babban nasara bace a kan kowata mace,
miji ne na nunawa sa'a na kece raini, amma zan iya cewa duk kunyi dace dan ke ma ta mai rabo ce, gashi mai rabon ya yi huff da ke."
hawaye yakuma zuba mata Miemie na dariya ta ce
"To meye na kukan kuma ai ke abin farinciki ne ma ace mutum kamar Abdulrahim kika mallaka a matsayin miji,
had'uwa iya had'uwa ya had'a komai babu makusa."
kai ta kawar gefe itafa har yanzu abun a almara yake zuwa mata, taya za'ayi ace hakan ya kasance, aure ita da Sahab!.
ta girgiza kai mene ne auren ma tukun kawai dai sun had'a ne amma hakan ai ba mai yuwuwa bane.
maganar Miemie ce ya dawo da ita daga duniyar tunanin data lula.
"Feeryal ba dai bijerewa Daddy zakiyi ba?."
da sauri ta girgiza kai cikin muryarta mai sanyi ta ce
"Bana fatan ranar da zatazo na bijirewa Daddy kan duk abin da zai umurce ni, amma Miemie tsoro nake ji dama wani ne cikin su Ya Ajmal ba Sahab ba."
"To ai kuwa duk cikin su babu wan da ya dace da ke sai Ya Abdulrahim zab'i mai kyau Daddy ya yi miki, dan shi ya dace da ke, in kuma musu zakiyi masa to."
Feeryal bata kuma magana ba sai kwantar da kanta da da tayi jikin pillow.
Miemie ta duro a gadon tana cewa
"Bari naje na dawo na zo mu fara shirya yadda shagalin bikin nan zai kasance, abu namu maganin a kwab'e mu."
da ido ta bita har tayi waje.
a hankali ta lumshe idanunta, ya yin da komai yake zuwar mata tamkar a mafarki.

A can d'akin Aunty kuwa Daddy ya mike ya dubi Aunty ya ce
"Kije ki sameta lamarin zai iya yi mata girma a karancin shekarun ta, bana so ke ma kisa damuwa cikin ranki."
kai ta jinjina suka fito tare shi ya fita ita ta shiga d'akin Feeryal.
tana kwance idanunta a lumshe bawai dan tana bacci ba.
a gefen ta ta zauna ta janye pillow da ke kanta tad'ago kanta tayi mata pillow da cinyarta.
bud'e ido tayi ta kalli Aunty tare da sakar mata murmushi.
Aunty ta d'an lumshe ido ta bud'e tare da jinjina kai tana maida mata murmushin.
kanta ta shafa a hankali cikin dabara ta soma magana
"Yanmatan Ammie sai kayi hakuri kake kai ga gab'ar cin nasara a rayuwa,
Daddy bai tab'a yin wani abu domin ya musgunawa rayuwata ba, duk abin da zaiyi alkhairi ce ga rayuwa ta,
kisaki ranki bana so ki sawa ranki damuwar ko mai, duk wanda kikagani a duniyar nan tun kafin yazo duniya aka hukunta mata mijin aure ko matar auren shi,
kicire duk wata damuwa aranki kicigaba da rayuwar ki yadda kika saba,
bana so ki sanyawa ranki damuwar komai,
Allah zai baki ladan biyayya, ko bakya son ladar ne?."
a hankali ta ce
"Ina so."
"Yauwa to ko kefa, Allah ne kad'ai yasan ladan da kika samu, ko nayi addu'a Allah ya raba mana ladar?."
murmushi tayi
"To shike nan rike ladarki ke kad'ai, tun da kinga kin girma yanzu ke ma kina son tara lada, bari na tafi tun da bazaki sammin ladar ki ba."
Aunty ta mike da sauri ita ma tamike cikin muryar dariya take fad'in
"To Ammie kiyi addu'a ladar a raba mana."
Aunty tayi dariya ganin ta saki ranta ta ce
"Anya kuwa maganar nan takai can cikin kasar zuciya?."
kai ta gyad'a tana dariya.
"To shike nan zanyi addu'a a bani kad'an a bar miki mai yawa, yi sallah ki fito mushiga kitchen ayi rige-rigen tara lada."
ai ko da sauri ta shige bathroom, Aunty ta fice cike da jin dad'in yadda tayi saurin shawo kanta, hakan kuwa baya rasa nasaba da karancin shekarun ta da kuma tarbiyyar da aka shinfid'a shi cikin rayuwarta tun batasan kanta ba.
bayan ta idar da sallah ta tafi kitchen ta sami Aunty suka soma aiki kamar yadda suka saba..
Chapter 3 · 0% Book details