← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 61

Sashe 5

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ajmal ya dubi Shamsuddin ya ce
"Me yasa ka kawo matar nan nan tazo ta d'agawa mutane hankali kawai."
bai kai ga bashi amsa ba su Abbieh dake cikin d'akin da Daddy yake suka fito da sauri sukayi kan maiafiyar tasu,
Abbie ya ruko ta yana fad'in
"Hajiya taso kije ki gani Yaya Abubakar bai mutu ba."
Hajiya ta taso a dibirbirce da sauri ta soma Abbieh dake rike da hannunta tana fad'in
"Allahu Akhbar Abubakar, ina Abubakar d'ina yake? taso kaji wlh na kanye maganata na yafe maka idan baka d'aura musu auren bama kaje ka d'aura na amince."
tana ganin Daddy na numfashi ta fashe da kuka ta karasa inda yake ta ruko hannunsa tana cigaba da fad'in
"Abubakar bud'e idanunka wlh na janye maganata ta tashi kaje kasa yarinyar ta tare sashin abokin turawa,
kayafe ni d'ana karka mutu idan ka mutu ina zamu shiga ina wannan tarin iyalen zasu shiga,
tashi ka yafe ni Abubakar."
Daddy da maganganun Hajiya ke yawo cikin kwakwalwatsa yad'an motsa,
allurar bacci na jikin sa idanunsa a rufe amma sai da ya yi murmushi.
Abdulrahim dake tsaye hannayen sa suna sufe cikin aljanu,
ya tab'e baki tare da zaro d'aya hannunsa dake d'aure da agogo, ya kalla kana ya fubi su Dad ya ce
"A barshi ya yi bacci."
da sauri Abbie ya janyo hannu Hajiya ya na cewa
"To to Hajiya zo muje waje mu jira."
Hajiya da gaba ki d'aya take a firgice ta ce
"Amma dai zai tashi ko bazai tafi daga baccin nan ba, ku tayani fad'a masa wlh na janye duk wani abun da na fad'a ya tashi ya gafarceni."
"Hajiya bazai mutu ba insha'allah Yaya Abubakar zai tashi, muje mu jira a waje."
suna fita ya matso ya d'an duddubashi, kana shima yafita yaja masa kofar.

Inda su Ajmal ke tsaya ya karaso yadan dube shi.
"Kaine ko?."
ya fad'a yana kallon Ajmal.
Ajmal ya ce
"Ai in ba an mata haka ba bazata bar mutane su huta ba, mata da fitina haka, kullum sai ta d'agawa Daddy hankali."
ya yi kwafa yana taune lips.
"Be careful ana wasa da mutuwa ne."
ya fad'a yana wurga masa kallo mai kama da hararar, yana nade hannun rigarsa.
kwafa Ajmal ya kuma tare da taune lips gami da girgiza kai.

Nutsuwa da jin dad'i ya ziyarci Aunty sai godiya da tasbihi ta ke wa Allah subhanahu wata'ala.
Mommy ta matso in da Hajiya take tana cewa
"Hajiya cewa fa kikayi kin amince da auren, Hajiya ko kin mance wa aka aura masa ne."
Hajiya da hankalin ta yafara kwanciya ganin Daddy na da rai bai mutuba ta ce
"Ke da'alla Halima rabani koma wa ya aura masa in dai har bazai mutu ba."
Umma Karima da maganganun Hajiya ya shanye mata ruwan kai,
da sauri ta zame jiki tabar asibitin, dan tana jin idan tacigaba da zama zuciyarta zata tarwatse a yadda take jin kanta..

Sai daf magriba Daddy ya farka, har yanzu su Aunty basu gusa ba, saima kara tuttud'o wa dangi suke,
sai dai da sun zo za'a dakatar da su awani keb'ab'b'en parlour, dan ba'a so a dami shi da surutu.
Daddy na farkawa ana sanar da farkawar nasa, Hajiya ta suri kafa tayi room d'in da yake.
Abdulrahim na tsaye yana cire masa ruwan da yaka re yanzu.
Hajiya ta karaso bakin gadon tana cewa
"Abubakar ka tashi? sannu kaji kayi hakuri ka gafarce ni, in Allah ya yarda bazan sake wata magana ba,
rayuwar ka da lafiyar ka yafi min ko mai, ya jikin naka Abubakar?."
Daddy ya yi murmushin jin dad'i ya ce
"Jiki da sauki sosai Hajiya."
"To madalla zamu tafi gida ba anjima ko."
Daddy ya kalli Abdulrahim yana cewa
"Zan iya tafiya gida anjima ko?."
"After 7 days kafin mu gani ko zaka iya koma wa a kwanakin."
ya fad'a yana gyara rukon ruwan allurar daya zuko cikin Syringe ya kamo hannunsa yana masa ta cikin cannula.
Daddy ya ce
"Hajiya kinji sai nayi kwana bakwai kafin a sallame ni na koma gida."
Hajiya ta ce
"To-to ai shike nan in dai zaka sami lafiya ko wata guda ne ai za'a zauna,
kai abokin turawa zai warke dai babu abun da zai same shi ko?."
baki ya tab'e ba tare da ya yi magana ba ya zare syringe'n.
Aunty ta turo kofar da sallah Ajmal da Shamsuddin su na biye da ita.
wani murmushin farin cikin gani Daddy zaune Aunty ta sake.
daga in da Daddy ke zaune shima ya maida mata murmushin.
Mommy ta turo kofa ta shigo tana wani shashshan kamshi tana cika tana batsewa.
Abdulrahim ya dubi Aunty yana cewa
"A sama masa wani abun ya ce yanzu."
kana ya maida dubansa ga Daddy ya ce
"Daddy zaka iya yin sallah bayan ka d'an tab'a wani abin."
kai Daddy ya jinjina, da sauri Aunty ta fita.
Mommy tabi bayanta da harara, Aunty ta isa in da ta aje basket d'in abincin data koma ta girka masa, dan tasan dama idan ya farka dole zai bukaci abinci.
ta d'auko ta koma d'akin ta soma had'a masa abunda tasan yafi bukata.
bayan Ajmal ya taimaka masa yaje ya wanko bakinsa ta aje masa saman gadon ya soma ci.
"Kai dun gidan ku ina tambayar ka yaushe zaiji sauki kayi burus da ni."
Abdulrahim ya tarkasa 'yan kayakin sa yana cewe
"Ki jira lokacin mana."
ya sa kai ya fice.
Daddy ya ce "Hajiya zanji sauki ai in Allah ya yarda."
Hajiya ta ce "To Allah ya kawo manzon sauki da gaggawa."

Kwanan Daddy uku a asibiti kullum a can su Aunty suke wuni, kwana kuma Ajmal da Shamsuddin ne suke kwana a kanshi.
Umma Karima kam tun da tazo ranar farko bata kara zuwa ba, sai ta fake da wai itama bata jin dad'i ne.
sai yau Feeryal itama ta sami zuwa duba Daddy, dan kullum in tace zataje ta gaishe shi, Aunty takan ce tabari tukunna.
yau Aunty da kanta tace ta shirya suke.
Feeryal bata sake ba dan su Farida da su Ameerah Nabila Sahla yau duk suna gurin, gashi Miemie bata zo ba,
sukayi ta mata habaici tana gefe.
dataga zaman shirun ya dame ta sai ta d'au wayarta tasoma sana'ar ta wato buga game.
magana taji a kanta tayi saurin d'ago wa.
wani saurayi ne yana tsaye a kanta ya kurawa kyakkyawan surar ta ido yana fad'in
"Sarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci wannan sura."
"Feeryal zo ki rike min wannan."
ta jiyo maganar Aunty daga bayan su.
ta mike da sauri tana d'agowa suka had'a ido da Abdulrahim.
da sauri ta bi hanyar da Aunty take.

Da daddare kamar yadda suka saba, direba ya kwashi su Hajiya da Mommy da wasu daga cikin 'yan gidan.
Aunty ta d'au jakar ta tana kokarin fita taje ta same su su koma gida.
Daddy ya ce
"Fad'imatu yau banda ke a tafiyar ki zauna ki taya ni zama kad'aici na dami na."
"Daddy naga gasu Ajmal da Shamsuddin, basu wadatar ba."
"Su ba sa'an hirata bane basusan wace irin hira nafi so ba, ke kad'ai kika sani dan haka ki zauna ko kuma mutafi gidan tare."
"Aa Daddy baka gama warkewa ba, ai da Abdulrahim ya sallame ka, to Daddy Feeryal fa da wa zataje gida, kasan bazai yuwu ta bisu ba."
Daddy ya ce
"Baga mijin ta ba in zai tafi sai ya d'auki matarsa su koma gida tare."
Daddy na rufa baki Abdulrahim na shigowa yana rataye da jakan kayan system nasa da wasu 'yan tarkacen sa.
ya karaso yana fad'in
"Daddy ya jikin akwai wata matsala ne?."
Daddy ya ce
"Babu komai jiki da sauki sosai Abdulrahim zaka iya tafiyarka, amma ka d'auki matarka tana waje ku koma gida tare."
bai yi magana ba ya sa kai yana fad'in
"Sai da safe.........!

Yana fita Dr Imran ya taho inda yake.
"AA na kiraka baka d'aga ba ashe kana gurin Daddy."
tafiya ya soma yana dad'in
"Ya akayi?."
Dr Imran ya ce
"Dr Daniel ne ya kirani yace ya kiraka baka d'aga ba."
"Kace masa Daddy na is seriously ill, next week zan shigo."
Dr Imran ya ce "Okay zan sanarasa."
Nurse Samira ke takowa tana nufo in da suke.
Dr Imran ya ce "Oh yau tana night ashe, anya bazakayi na uku da ita ba kuwa?."
Dr Imran ya yi maganar cikin zolaya.
bai kulashi ba ya ci gaba da tafiyarsa.
Samira ta karaso da sauri tana narke murya
"Sir the patient of that room his BP is higher."
"Je ka duba shi."
ya ce wa Dr Imran, fuska tad'an kwab'e bata so haka ba ta so a ce shine zaije da kansa dan ta samu damar tsayuwa kusa da shi, ta shaki kamshinsa mai dad'i.
Dr Imran ya yi hanyar room d'in tabi bayan sa.
Chapter 5 · 0% Book details