Sashe 13
Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Ya na gamawa ya d'au wukan ya fita.
Jim kad'an ya dawo rike da allura daya rigada ya ja a sirinji.
ya tako bakin gado allurar ya d'ago tare da cire murfin Kansa, d'an tsayuwa ya yi kamar mai nazarin wani abu.
gajeren tsaki yaja yakai hannu ta kasan towel d'in yarike sai kuma ya sake, tare da furzar da fuci daga bakin sa.
ya juya da sauri har yakai bakin kofa yakuma juyowa,
yadawo bakin gadon.
ya janyo bargo ya rufe ta daga kafafunta zuwa kugun ta.
sannan yajanyo towel d'in ya zaro shi daga cikin blanket d'in, ya d'an zamo bargon kasa kad'an dai-dai in da zai mata allurar yana luma allurar da sauri ya d'auke kai.
Ajiyan zuciya ta sauke sanda allurar ya shige ta, a hankali yake matsa ruwan allurar a jikin ta.
zabura tayi dai-dai san da ya zaro shi, ya d'au cup da yagani kan bedside da ruwa a ciki ya tsiyaya a tafin hannunsa ya wasa mata a fuska.
dogon numfashi ta sauke,
ta kuma zabura tare da ware idanunta, suka sauka kanshi.
cikin harhad'a kalmomi ta ce
"Kar..kar...kayimin allura."
tana fad'in haka jikin ta ya sake gaba d'aya bacci ya d'auketa cikin yanayin da take ciki.
ya juya da sauri yabar d'akin.
Sanyin asuba ne ya farkar da ita tayi mika gami da salati a hankali ta mike zaune tana mussike idanunta.
a sannu ta zamo bakin gado.
ta na saka kafafunta kasa ta tuna da kamar wani abu ya faru.
da sauri ta ware idanunta tana rarraba ido cikin d'akin,
d'akin fess babu komai. shiru tayi tana juya abun cikin ranta.
tabbas wani abu ya faru taga Zaraddin ya shigo d'akin nan, har yayi mata maganganu, daga nan kuma wuta ya d'auke wani ya shigo, taji ihun Zaraddin takuma ji alamun ana dukan sa.
daga baya wuta ya kawo taga jini a d'akin.
tana ta son tuna abun da ya faru bayan nan, amma duk iya tunanin ta nan ya tsaya.
ido ta dad'a warowa cikin d'akin babu jini hasali ma fess ya ke.
kai ta girgiza a fili ta furta
"Ko mafarki ne?."
sai kuma ta kwab'e fuska
"Mafarki ne ma me zai kawo Ya Zaraddin nan."
takuma fad'a
tare da kallon jikinta towel d'in dai data d'aura jiya ne bayan tayi wanka, ke nan bacci ne ya d'auke ta ke nan har ganin da ta wa Sahab ma a d'akin nan da allura a hannunsa duk mafarki ne?.
takuma kwab'e fuska, mafarkin sam baiyi mata dad'i ba.
ta mike a hankali ta shige bathroom.
sai da ta yi wanka da ruwa mai zafi dan tana jin jikin nata yana yi mata nauyi.
ta d'auro al'wala ta fito, ta saka kaya sannan ta haye sallaya ta tada sallah.
bayan ta idar tayi azqar, ta kuma kwanciya.
Karar ringing d'in waya ne yata da ita daga baccin da take.
a hankali ta mike zaune tana waige-waigen ta in da sautin ke tashi.
ta janyo wayarta tana mamakin ta yadda akayi sautin wayar nata ya koma haka.
da sauri ta waiga ta gefen da ta ji sautin na tashi.
ta zamo bakin gado ta sunkuya ta in da take jiyo sautin.
wayar ta gani a ta d'an karkashin gado, ta d'auko tana juya shi a hannunta da mamakin me yakawo waya nan.
kiran na yanke wa fuskar wayan ya bayyana, da mamaki take kallon hoton da yake fuskar wayan, yana zaune turawa sun sashi a tsakiya, dukkanin su da shigan likitoti.
fuskarsa d'auke da kyakkyawan murmushi mai burgewa.
mamaki yakuma kamata, a hankali abun da ya faru jiya yashiga dawo mata, Zaraddin ya shigo da gaske bayan nan kuma shima Sahab d'in ke nan tagani rike da allura azahiri ba mafarki ba.
to me ya kawo shi har ya bar wayarsa anan?.
baki ta cuno a kasan ranta ta ce
"Ai Sahab d'in nan mugu ne allura yayi min ina bacci, shiyasa naji nan namin zafi,
alhalin lafiya ta lau."
ta tab'a gefen mazaunan ta.
ta aje wayar ta mike tana tuno kalaman da Zaraddin yayi amfani da su a kanta, duk da har yanzu takasa banbance shin hakan yafaru ko mafarki ne,
to in dai mafarki ne to ya akayi wayar Sahab ya shigo d'akin ta.
fuska ta kwab'e jin tunani nason hargisa mata kwakwalwa.
ganin goma saura
ta mike rike da wayar ta tafi kitchen.
ganin lokaci ya tafi batayi wani breakfast mai wahalaba,
Sudan tea ta girka, sai chips. tana cikin yanka albasan da zata soya kwai wuka ya zarce ya yanke ta.
kara tayi tare da sakin wukan da albasan kasa, tashiga yarfe hannu...
Da shirin fita ya shigo d'aukar Sudan tea d'in sa, baya yayi tare da leko kitchen d'in kasancewar kofar kitchen d'in a bud'e yake.
idan ta kalli hannun sai taji ya kara zafi, sai yarfe hannu take d'an jinin da yake fita duk ya b'ata mata jiki.
tuni hawaye yacika idanunta, kad'an ya rage su zubo.
tana d'agowa suka had'a ido, a hankali ta sunkiyar da kanta tare da kwab'e fuska tana mai dad'a yarfe hannun.
kamar zai wuce dinning sai kuma ya juyo ya tako zuwa cikin kitchen d'in.
da d'an sauri ta d'ago tana duban shi, ganin yana takowa cikin kitchen d'in.
sai kuma ta kuma sunkuyar da kai, san da ya iso in da take.
hannun da tayi yankan ya ruko.
da sauri ta d'ago da idanunta da suka ciko da kwalla sai sheki suke kad'an yarage su zubo.
suka had'a ido, fuskarsa a d'aure.
a hankali ta kuma sunkuyar da kanta.
sakin hannun nata yayi sannan ya juya ya fita.
bayan sa tabi da kallo tana kuma yarfe hannun, ta jingina da jikin cabinet, tana son yin kuka.
jim kad'an ya dawo har lokacin tana tsaye tana sharar kwalla.
baki ya tab'e baiga wani yankan kirki ba sai raki take.
da sauri ta dago jin ya kuma kamo hannunta, taji ya manna mata abu a kan yankan.
'yar karamar kara tayi, ya sake mata hannun, ya juya yafita......!
Aikin da bata karasa ba kenan ta koma d'aki.
mintuna kalilan ta nimi zafin ta rasa.
Ko da ya fita sashin Daddy ya tafi.
yana zaune suna gaisawa su Ajmaal Shamsuddin da Faisal suka shigo.
a kasan carpet suka zauna, kana suka shiga gaida Daddy.
sannan suka juya ga yayan nasu.
Daddy ya dube su yana fad'in
"Zaraddin yau ma bai kwana a gida ba ko, na tambaye security sunce min shine kad'ai bai shigo ba."
Shamsuddin ya ce
"Eh Daddy bai kwana ba tun jiya da safe da ya fita bai dawo ba, yana can gurin gantalinsa, Daddy dama nace zan gaya maka har giya ranar yashigo da shi gidan nan."
Ajmaal yad'an tab'a shi ta kasa kan ya yi shiru, shiko yaci gaba da fad'in.
"Kuma wlh Daddy saran da ya samu yanzu, idan ya tabbatar da kasan ya dawo,
cikin dare yake fita ya tirsasa security sai sun bud'e masa get, sai gari ya waye kafin ya dawo."
Daddy ya yi shiru yana saurarar sa kana ya jinjina kai tare da fad'in
"Allah kashirya Zaraddin daya zamo jarabawa cikin ahali, zansa aje a nemo sa idan ba anyi masa hukunci ba bazai dai na abunda yake ba, daga nan musa ayi ta masa addu'a da saukan alkur'ani, Allah ya shiryar da shi."
Abdulrahim ya yi kwafa ya mike tare da taune gefen lips d'in sa, yanufi kofa.
Daddy yabi bayan sa da kallo.
su Ajmaal ma suka mike suka fita.