Sashe 28
Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ta karaso ciki tana fad'in
"Doctor naga shigowarka lokacin ina duba wani mara lafiya ne, ba dai bigeta kayi da mota ba, subhanallah buguwar a ciki ke nan, Allah yasa babu wata matsala sosai? ."
ya ce
"No, she is my wife."
zaman gilashin idanunta ta gyara da kyau, kana ta kalli Feeryal dake kwance sannan ta maida idanunta kan computer ta waro ido tana cewa
"Wow! I congratulate you."
kai ya jinjina yana kokarin numfashin ta ya dawo.
Dr Khadija ta masa ta gurin kafafunta ta saka tafin hannunta tana gogo tafin kafanta.
ta ce
"Doctor, hurry up and get her breath back, don't take too long."
bata rufa baki ba ta ja numfashi, ta zabura tana kokarin mikewa.
Dr Khadija ta bita da murmushi tana fad'in
"Sannu kinji."
ido ta kura mata ta lumshe idanunta ta bud'e su a kanta.
firgigit tayi ta mike zaune tana kokarin durowa a gadon.
tayi saurin ce mata
"Bi a hankali, a kwai drip a hannunki."
da sauri ta kalli hannun nata kana ta kalle shi.
Dr Khadija ta ce
"Dr Allah ya sawaka bari naje akwai patients a layi."
ta fita tana mata Allah ya sawaka.
tana ganin fitarta ta kuma yunkurin sauka, hannun ta da ruwa ke shiga ya rike.
kuma yunkurin sauka tayi ya ce
"Ki jira ya karasa shiga."
kallon ruwan tayi saura kiris, ta kalle shi tana kwab'e fuska zatayi kuka.
cikin muryar da ke kunshe da son yin kuka ta ce
"Ni gida zan tafi."
tayi maganar tana kokarin kwatar hannunta ta kasa.
ido ya zuba mata hawaye ya fara gangara fuskarta.
bai sake ta ba yana rike da hannun nata bai kuma yi magana ba.
yana kallon yadda hawaye ke bin fuskarta.
yana tsaye rike da hannun nata har ruwan ya karasa shiga,
ya cire mata.
ai ko da sauri ta dire a gadon tana yarfe hannu.
key ya d'auka ya bud'e d'ya kofar wan da kofar fita ce ta baya.
alama ya yi mata ta zo ta wuce.
a hankali ta tako ta wuce yabi bayanta.
ke b'abb'en hanya ce wan da shi kad'ai yake bi, idan zai shigo asibitin ko zai fita, a kwai motar hawan sa a d'an ma dai-dai cin parking lot a gurin.
motar ya bud'e ya shiga san nan yayi mata alama da ta shigo.
jikinta na d'ari-d'ari ta shiga yaja motar mai gadin dake bakin get d'in wannan hanyar ya bud'e suka fita.
tana ta raba ido wai ya akayi ne ta ke ta ganin ta a wurare daban-daban, wan da ba ita take kawo kanta ba.
tunanin ta ne ya tsaya ganin iya titi ya ketare yayi not a bakin wani katon get.
ganin yana kokarin shiga gidan tayi saurin kallon shi murya a sanyaye ta ce
"Sahab nan ba gidan bane."
kallon ta yi sannan ya kuma mai idanunsa ga hanya, ya karasa ciki ya gyara parking sannan ya bud'e ya fita.
ya zaga gefen da take ya bud'e yayi mata alama data sauka.
jiki a sanyaye ta zuro fararen kafafun ta da babu takalmi kasa.
ya juya ya samo tafiya tabi bayansa bayan ta rufe motar.
tana tafe tana waige-waige wai shin a Nigeria take ko a wani kasar dan gidan bai yi mata kamada a Nigeria take ba.
a bun da ya kuma bata mamaki yana isowa jikin kofar wanda yake na glass ne gaba d'aya glass d'in ya kawo haske da kaloli masu kyau, sauti kuma ya biyo baya
"You are welcome sir."
ido ta ware sosai tabbas daga jikin gilashin sautin ke tashi.
sannan ya zuge da kansa, ya sa kai ya shi tabi bayansa a hankali.
ganin ta bayyana cikin wani hamshakin parlour taja ta tsaya.
Wani kofa ya bud'e ya shiga jim kad'an ya fito har lokacin tana tsaye.
ya tako cikin parlour'n ya zauna kan d'aya daga cikin kujeru na alfarma dake cikin parlour'n, ya d'au rimut ya kunna tv batare da ya kalli in da take ba ya ce
"Kije kiyi sallah."
da sauri ta kalle shi ta ce
"Ni gida zan tafi."
d'agowa ya yi ya wurga mata wani kallo mai shiga jiki
"Ba zakiyi sallar ba?."
ya fad'a yana tsare ta da ido.
baki ta cuno ta tare da yin kasa da kanta.
sanna ta soma d'aga kafarta ta nufi kofar da taga ya shiga.
tabi d'akin da kallo lallai in ba ta mance ba wannan d'akin ta bud'e ido ta ganta a ciki kafin yanzu.
a hankali ta taka ta nufi kofar da tafi yakinin nan ne bathroom ta bud'e ta shiga.
a sannu
ta tub'e kayan jikinta tayi wanka tare da yin al'wala ta d'auro towel da tagani a bayin, tad'anyi jim bata iya wanka ta maida kayan da ta cire.
a hankali ta bud'o kofar ta leko babu kowa da sauri ta fito.
rike da kayan tana tunanin taya zatayi sallar ba hijab kayan kuma bazata iya mayarwa jikin ta ba.
tana saka da tunanin aka turo kofar, da sauri ta kalli kofar tana kare jikinta da gyalen ta.
ya karaso cikin d'akin ya aje laidar hannunsa bakin gado ya juya ya fita batare da yace ko mai ba.
yana fita tayi sauri ta matso ta bud'e laidar.
abaya ce a laidar sa da hijab shima a cikin laidar sa, da pant da bra.
da sauri ta saka kayan tazura hijab dai-dai lokacin da ake kwad'a Kiran sallar magriba.
ta haye sallayar da ta gani cikin d'akin, ta fuskanci ta in da sallayar ke kallo ta tada sallah.
tana idarwa ta mike da sauri ta fito parlour.
ganin baya nan ta nufi kofar sai dai ta rasa ta yadda ake bud'e kofar,
ta koma d'akin da tunanin masallaci ya tafi.
tana zaune tajiyo kiran sallar isha
bayan ta gabatar ta zauna zaman jiran shigowar sa ya bud'e mata ta tafi.
ta gumi ta buga tana tunanin ta yadda akayi ma tazo nan.
tabbas tasan kasuwa sukaje taga wasu suna kallonta sannan suka biyo ta daga nan bata kuma iya tuna ko mai ba.
akasan ranta take fad'in
"To ina Aunty Maryam kar dai ace itama sun bita,
to ya akayi kuma na ganni a nan tare da Sahab??."
haka ta rika tambayar kanta da kanta da bata da amsar da zata baiwa kanta.
gashi bata ga wayarta ba ba bare ta kira Maryam d'in ko Hajja Umma.
bata ankara ba taga 8 ta gota, ta mike da sauri ta isa bakin kofa, sai jin kofar tayi a rufe.
da mamaki ta koma ta zauna bakin gado, ta kuma buga tagumi.
sai wajen takwas da rabi taji alamar ana bud'e kofar.
yana shiga ta mike da sauri.
ya karaso ya aje mata basket d'in abincin da Dr Khadija ta aiko masa da shi, sanin su biyu ne abincin yafi na inda da take aiko masa.
tun kafin yayi magana
ta shiga girgiza kai tana fad'in
"Na koshi na koshi bana jin yunwa, dan Allah Sahab gida zan tafi."
tayi maganar da sauri kamar zatayi kuka.
kallon ta yayi ta marairaice fuska hawaye ya cika kyakyawan idanunta.
ya juya tabi bayan sa da sauri har tana had'a wa da sassarfa.
ganin ya shige wani bedroom taja ta tsaya jim kad'an ya fito da makullin moto tabi shi da sauri.
tun kafin yace ta shiga mota ta bud'e ta shige.
sai da taga sun haura titi kafin tasoma jin nutsuwa.
ta rungume hannayenta ta cikin hijab dan sabo da sanyin EC dake tashi cikin motar.
idanunta akan hanya tana alla-alla su isa.
tafi mai nisa sukayi gidan Alhaji Tahir Abbas da gidan sa da rata sosai.
suna haurawa titin da zai sada su da gidan Alhaji Tahir Abbas ta kuma jin dad'i.
suna isa dai-dai get d'in gidan yayi parking a bakin get.
da sauri ta kai hannu zata bud'e kofar taji sa a rufe,
ta juyo a d'an sanyaye ta kalle shi.
da sauri ta janye idanunta sakamakon had'uwar da idanunsu ya yi.
'yar karamar laida mai d'auke da tambarin pharmacy a jiki ya mika mata, a hankali tasa hannu ta karb'a.
"Kullum kisha har ya kare."
ya fad'a yana janye idanunsa daga kallonta.
a hankali ta gyad'a kai ya bud'e motar da sauri ta fita.
yabi bayanta da kallo har ta karasa get ta bubbo mai gadi ya bud'e ya leko,
ganin ita ce ya bata hanya ta shige gidan da sauri har tana had'awa da sassarfa.
sai da yaga shigarta kafin ya ja motar ya tafi.