← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 61

Sashe 2

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bappa Salihu na fita Mommy ta kamo Kuraiba tana fad'in
"Zo nan aikin banza sukayi dan wlh ba abun da zai sa Abdulrahim ya zauna da yarinyar nan,
kwantar da hankalin ki kar ki wani tada hankalin ki ki sawa ranki damuwa,
muga yadda za'ayi su kai masa ita, yadda aka d'aurashi a titi haka zai watse a titi,
koma b'angaren ki kije ki kwanta ki huta kibarmin komai a hannuna."
"Mommy kin tabbata?."
"Aa ba ni na gaya miki ba ai ni yarinyar ce sam-sam bani kaunar ta, dan me zaisa na zuba ido a had'a ta da d'ana,
kije nagaya miki ke dai."
Kuraiba ta juya ta fita
gefen Abdulrahim ta nufa, tana shiga ta ganshi ya fito cikin shirin tafiya asibiti.
tasha gabansa tana taunar cingam tana yi masa wani kallon sama da kasa sannan ta ce
"Abdulrahim auren mu baiyi shekara ba aka kuma yi maka aure, baka gaya musu cewa ba wani isasshen lafiya ce gareka ba,
kai kana likita ma baka fahimta ba,
in ba haka ba zuwana gidan nan zan iya kirga sau nawa ka kusanceni, shima sai nayi tattaki nazo gare ka,
saboda ina maka kallon namiji mai lafiya da bazai iya rike kansa batare da mace kusa da shi ba, baka tab'a yin awa 3 a kaina ba,
a hakanne za'a kuma baka mata, wannan yarinyar da tasan mazama ina zata iya zama da kai."
"Bani hanya na wuce!."
yafad'a cikin tsawa fuska babu wasa.
duk da rashin mutunci na gaban goshin ta sai da ta girgiza da tsawan daya buga mata.
ta matsa gefe tare da sakin kukan makirci sannan ta rungume shi ta baya tana fad'in
"Ban tab'a ganin haka ba aure bai shekaraba ace za'a kara aure, me kawaye na zasu d'auke ni, please mijin Kuraiba kace baka son auren nan."
fezge jikin sa ya yi yasa kai yafice a a parlour.
yashiga motarsa yabar gidan.

Umma Karima da labari ya isar mata ta garzaya sashin Mommy a bujajan.
ko zama batayi ba, ta soma fad'in
"Amma kin bani mamaki Hajiya Halima, kina da ranki a cikin gidannan ki zuba ido a aurawa d'anki aure da wannan annobar yarinyar da take son ganin bayan mu,
kuma kina zaune kin rungumi hannu kin yi shiru,
shikenan burin Hajiya Fatima ya cika, ta mallaki mijin ki ta mallaki d'anki,
to me yayi saura baki da wani amfani kin zamo 'yar kallo."
Mommy ta ce
"Zauna Hajiya Karima, wlh na rasa yadda zanyi ne sun d'aure ni da jijiyata, Baba ya tsaya tsayin daka cikin lamarin, jira nake ya tafi wlh bazan tab'a zuba ido na bar auren nan ya yuwuba tun da aka d'aura wlh sai ya sake ta,
zan nunawa Hajiya Fatima ni na haifi Abdulrahim."
Umma Karima da gaba d'aya hankalin ta ya kai kololuwa wajen tashi ji take tamkar zatayi hauka.
ta zauna tana fad'in
"Uhm yanzu naji batu, idan baki sa auren nan ya watse ba, ina mai tabbatar miki ke zaki watse, dan wlh Hajiya Fatima da wannan mayyar aljanar ruwan sai sun kora mu a gidan nan mun zama 'yan kallo daga can bakin get."
Mommy ta buga kirji ta ce
"Ai insha'allahu sai dai su subar gidan nan ba dai mu ba,
yau Baba zai bar garinnan ai wlh bazan kyale ba bazan tab'a bari d'ana ya zauna da yarinyar nan ba."
Umma Karima ta jijjiga kai tana jan kwafa zuciyarta na wani irin tukuki abin mamaki wai Feeryal ce aka aurawa Abdulrahim.
idan ta tuna haka sai taji tamkar tayi ta kururuwa ko zataji saukin lamarin, bata tab'a sammani ko hasashen hakan zai iya kasancewa ba,
da tuntuni tayiwa tufkar hanci.
ji tayi zaman parlour'n Mommyn yamata kad'an ta koma sashinta tasa direbanta ya kai ta gurin bokanta.

Umma Karima na zube gaban boka Mali tana haki, cikin matukar tashin hankali.
baka Mali nata zane-zane da buga kasansa,
idonsa na kan katon kwaryar tsafin dake gabansa.
ya d'ago yana cewa
"Mun kira su daga shi har ita basu bayyano ba, meke faruwa ne a duk sanda muka kirasu bama ganin su, duk iya makircinmu mun gaza ganin su da ido,
idan muka gwada wannan sa'ar ta gagara to tabbas sai anyi babban gaggarumin shiri a kan su."
"Boka koma meye a yi kai nifa in da halima a kawar da yarinyar tabar duniya ko zan huta, wlh boka ji nake kamar nayi hauka wannan shegiya tambad'ad'd'iyar yarinyar, bana kaunar bud'e ido na ganta daga ita har uwar goyon nata,
boka dan Allah ka taimaka min kamar yadda kasaba taimako na,
wlh bansan ina zan sa rayuwata ba idan auren nan ya zaunu, duk yadda za'ayi a wargazara auren asa ya yi mata saki uku basai an kai ga tarewa ba, ka fi kowa sanin matsala ta."
wani kazamin dariya ya sheke da shi.
kana ya d'au wani bakin ruwa ya na zirarawa cikin kwaryar tsafin nan, yana yi yana kiran sunan Feeryal da Abdulrahim.
har ya juye ruwan duka.
ya d'ago a daburce yana fad'in
"Basu amsa kiranye ba me suka takaaaa!
dole sai munyi aiki cikin duhu da bakaken aljanu."
Umma Karima ta ce
"To boka ni dai ko ma meye ayi bukatata kada auren nan yayi tasiri ya wargaje cikin gaggawa."
"Tashi kije cikin duhuwar dare zamu soma aikin ki."
ta mike tana fad'in
"Nagode boka dan Allah a wargaza auren na, wlh ban san ina zan sa rayuwa ta ba idan auren ya zaunu."

A hanyar komawar ta gida Umma Karima sai fifita take da d'ankwalinta, duk AC da ke motar ita gumi take.
ta gyara zama tare da jan tsaki gami da kwafa a karo na sau ba adadi, tana fad'in
"Tsintacciya tambad'ad'd'iya da ni Karima kike narantse in zanyi yawo tsirara sai na wargaza auren nan, bake ba zama a matsayin matar Abdulrahim baki isa ki kuma b'ata min shirina a wannan karon ba."
direbanta ya juya ya kalleta yana cewa
"Ayi hakuri dai abi a hankali Hajiya, kar ki kwashi kud'i kiyi ta dankarawa mutumin nan mu tashi a tutar babu."
wani uban harara ta dankara masa tare da jan dogon tsaki
"Mtttsss in kud'ina gaba d'aya zai kare wlh sai na hana Feeryal zama da Abdulrahim, yi sauri muje gida da'alla."

Tun a daren ranar Bappa Salihu ya yi shirin tafiya,
Daddy yayi-yayi ya bari ya yi ko da kwana uku ne,
ya ce ina aje kawai a shirya masa tafiya, da safe zai tafi.
akwai abin da zaije ya yi a gida.
washegari
Daddy Dad da Abbie suka fito rako shi zuwa sashim Hajiya dan yaje ya mata sallama.
a waje suka had'u da Abdulrahim zai shiga gaida Bappa Salihu.
cikin girmamawa duk ya haishe su.
Bappa Salihu ya dafa kafad'arsa tare da bubbugawa ya na fad'in
"Babban mutum Allah ya maka albarka."
"Amin."
ya furta a kan lab'b'ansa idan ba idon ka na kallonsa ba bazaka san ya amsa ba.
ya nad'e hannayensa a kirji suka taka zuwa sashin Hajiya.
Hajiya ta karkata baki tana fad'in
"Um to Allah ya tsare hanya ina ka d'aura auren ya tamku gudun kada ya warware nan gaba."
Bappa Salihu ya ce
"Idan bazaki fad'i alkhairi ba kiyi shiru, babu ruwan ki kicire hannunki cikin lamarin."
"Na cire hanu na ai na cire hanuna kuje ku karata, ni ina ruwa na idan yaso kuje ku aura masa 'yar sarkin aljanu ma ni ina ruwa na."
Bappa Salihu ya ce
"Eh hakan ma yafi ki cire hannun naki, to ni natafi Allah ya sada mu da alkhairi."
Hajiya ta kawar da kai tana fad'in
"Allah ya tsare."
Bappa Salihu yayi gaba su Daddy suka bi bayansa.
a waje ya tsaya yayi ta sawa Abdulrahim albarka tare da nasihohi, da ban hakuri kan ya yi hakurin zama da zab'in iyayensa.
har airport Daddy ya rakashi sai da jirgin su ya tashi kafin ya juyo gida...

Mommy tana ganin dawowar Daddy tasan Bappa Salihu ya tafi.
ta kira Abdulrahim ta ce duk abin da yake yabari ya zo.
yana shirin fita office ya nufo sashin ta.
bedroom d'in ta ya wuce ya sami guri ya zauna saman kujerar da ke d'akin, yana duba agogon dake d'aure a hannunsa, da alama dai sauri yake.
Mommy dake zaune bakin gado ta gyara zama tana dad'a tamke fuska ta dube shi da kyau sannan ta ce
"Me kake jira da auren yarinyar can da aka kakaba maka,
baka guntule shi haryan zu ba, har kabari ya kwana a kanka."
ta jefo masa takarda da biro tana cigaba da fad'in
"D'auka yanzu ka rubuta mata saki uku nakaiwa uwar gayyarta da hannuna, na nuna mata na isa da kai."
kallon takarda da biron ya yi kana ya kalli Mommy sannan ya ce
"Mommy lokacin da kika nuna min Kuraiba a matsayin zab'in ki, ban bijere ba nayi miki biyayya,
to dan me zan bijire nakiyiwa Daddy biyayya tun da duk haka kuka zab'arwa rayuwa ta, shike nan sai na kare rayuwar tawa a haka,
bani da ikon aiwatar da hakan sai idan Daddy ko Bappa Salihu sun umurce ni,
ko yanzu suka umurceni zan aiwatar."
ya mike tsaye yana cigaba da fad'in
"Mommy ina da CS 11."
Mommy data daskare a gurin ta waro ido had'i da buga kirji ta ce
"Abdulrahim ni kake gayawa haka, au wanda ya aurama shi zai baka izinin sakin,
tun da bani na aurama wannan ba ban kai na baka izinin sakin ta ba,
Eh lallai ba'a barka banza ba, yazama dole na warware barbad'en da akayi maka."
baiyi magana ba yayi waje da sauri dan saurin yake,
aka tsare shi da wani batun da aka dame shi da shi tun jiya.
Chapter 2 · 0% Book details