← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 61

Sashe 35

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma karima ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta shiga wani mummunar bala'in tashin hankalin da bata b'a shigan irin sa ba.
tayi sintiri ta zaga cikin parlour'n ta yafi a kirga.
Siyama ce ta shigo kamar an jefo ta tana haki da fad'in
"Aunty Karima ta haihu an cire 'ya'ya biyu duka maza, yanzun nan su Ajmaal suka shigo da idona na gana hoton yaran!."
Umma Karima ta buga kirji ta d'aura hannu a ka tana fad'in
"Nashiga uku!."
takuma dannan lambar da tun d'azu take ta gwada shi ya ki shiga.
jin wayar tashiga yanzu ta sauke numfashi sanda aka d'aga kiran.
"Dr ya zakayi min haka, ko nawa nagaya maka zan baka in har ka aiwatar da abun da na fad'a maka."
daga cikin wayar ya ce
"Hajiya matsala aka samu muna tsaka da aikin Dr AA FIYA ya shigo, karshe ma dai shi ya karasa aikin, abun da ya bani mamaki kuma, kince min bata gidan bai ma san da cikin ba, to ya akayi yasan biyu ne a cikin ta, bayan ya ciro d'ayan da mahaifarsa, a yadda ya koma domin ciro d'ayan yasan da akwai wani a cikin,
naso da ya kauce da ragowar d'ayan zansan yadda zanyi da shi, in yaso sai asan yadda za'ayi ma dai duka."
Umma Karima data cire d'ankwalinta tana fifita da shi ta ce
"Ya b'ata komai yama akayi yasan an kaita asibitin bayan baya gidan san da aka fita da ita!."
ta kashe wayar tayi zaman 'yan bori a kasa, tare da d'aura hannu akai ta kurma ihu tana fad'in
"Wallahi tallahi bazan barka haka ba Abdulrahim, Feeryal gidan nan ba naki bane,
dukiyar Alhaji Abubakar AA FIYA nawa ne, da na dad'e ina farautarsa yau zankarasa farautar dana d'au tsawon shekaru ina yin sa."
Siyama ma zubewa tayi kan kukera, tana jin kamar itama tayi ihun ko zata sami sassauci daga d'acin da take ji cikin zuciyarta.
burin ta dana Aunty'n nata da banbance ita burin ta ta aure shi su zauna inuwa d'aya ne,
duk wani abun da 'yar'uwan nata zata fad'a jinta kawai take,
ba so take a kashe shi ba ita so take ta aure shi ya zamo mallakinta.
Umma Karima ta mike da sauri ta fita ta nufi sashin Mommy.
tun kafin ta shigo parlour'n Mommy take jin yadda Mommy take cewa
"Wlh karya ne in har kuwa akace 'ya'yan nan nasa ne, to bazai rike 'ya'yan aljanu ba, ai dole ma su san yadda zasuyi yayan suyi kama da shi,
wani suffa ne aljanu bazasu iya juyawa ba, d'ana bazai zamo uban aljanu ba kuwa!."
ta wurgawa Ajmaal wayar sa kad'an ya rage ya fad'i yayi saurin cab'e wa, yana cewa
"Mommy ki bar wannan maganar tun da ta haihu ai ya kamata yanzu ko mai ya wuce, basai an fad'a ba ana ganin yarannan an san na Ya Abdulrahim ne, yara gwanin sha'awa ya kamata kiyi maraba da jikokinki."
"Dan uban ka bazan yi ba fita ka bani guri anan!."
Ajmaal ya juya ya fita.
Umma Karima ta karaso tana rike baki.
"Hajiya Halima mai jikoki an haifo miki manya-manyan sarakunan aljanu, sai ki cigaba da rainon su suzamo gamashekar da zasu girma su sare wuyarki."
"Haba Hajiya Karima wace irin fatar tsiya ce wannan, ai wlh 'ya'yan nan baza su kwana a duniyar mutane ba sai dai duniyar aljanu, can in da suka fito."
Mommy ta shige bedroom d'in ta tana zuba uban masifa.
Umma Karima ta juya ta fita tana zaman jiran sakamako idan baiyi mata ba ta d'au mataki da kanta a yau d'in nan ba sai goge ba.

Motarsa ne yakuma shigowa asibitin.
suka fito shi da Dr Imran suka nufi room d'in da Feeryal take yana rike da laidar magunguna,
Dr Imran kuma yana d'auke da wani katon laidar shopping .
Sumayya da Miemie suna ganin su suka mike suna musu sannu da zuwa,
Aunty ko shigarta toilet d'in room d'in ke nan zatayi al'walar sallar azahar sukayi sab'ani.
Dr Imran ya tsaya suna gaisawa da su Sumayya, shiko ya tako bakin gadon.
ya tsaya a kanta idonta a lumshe tana bacci yaran a jere a gefenta suma baccin suke.
sosai ya zuba musu ido ita da yaran, a fili ya sauke ajiyan zuciya.
a hankali yakai hannu ya shafi gefen fuskarta, ajiyan zuciya ta sauke tare da juya kai ta kwantar da fuskarta atafin hannunsa.
a hankali ya lumshe idanunsa tare da bud'e su a kanta.
ya zare hannun nasa a hankali ya kai fuskan yaran ya shafa zuwa kawunan su.
Dr Imran ya karaso yana fad'in
"Wow masha'Allah see beautiful baby's I congratulate you."
Dr Imran ya masa kusa da shi cikin yin kasa da murya sosai ya ce
"Gaskiya mutumi na kayi kokari fa ka zuba jarumta sai da ka samo masu kama da kai."
ya yi kamar baiji abun da Imran ya fad'a ba ya juya yafice.
har ya tada mota Dr Imran ya iso da sauri dan yasan halinsa sarai sai ya iya tafi ya barsa.
suna fita Aunty na fitowa daga toilet, Sumayya ta nuna mata kayan da suka kawo.
Aunty ta fita ta ce zataje masallacin cikin asibitin tayi sallah.

Mommy ta fito da sauri tana gyara mayafinta, ta shiga mota direbanta yaja suka nufi asibiti.
suna isa ta fito da sauri ta ce wa direban
"Jirani yanzu ina zuwa juya da motar ta hanyar fita."
ta nufi ciki tana tambayar wata nurse wanda akayiwa C'S da safen nan tana nuna mata d'akin da take,
Mommy ta tura kofar babu ko sallama.
lokacin Feeryal ta farka tana kallon su Miemie da suke ta zayyano sunayen da za'a rika kiran yaran da shi.
Aunty kuwa bata dawo daga sallah ba.
Mommy ta bugawa Sumayya harara tana cewa
"Uwar me kika tsaya d'auka anan?."
Sumayya ta turo baki.
Mommy ta karasa bakin gadon ta rike kugu tana kallon yaran,
tare da aikawa Feeryal da mugun kallon .
sai kuma ta jinjina kai kana ta sa hannu ta d'auki d'aya ta rike shi ta gefe, sannan ta kuma d'aukar d'aya ta juya ta fita, Feeryal tabi bayan ta da kallo.
su Miemie ma haka.
tana fita ta shiga mota ta ce direban yaja su tafi da sauri..
Mommy na fita ba da jimawa ba Aunty ta shigo.
da mamaki ta kalli kan gadon ta ce "Ina yaran."
Miemie ta ce "Mommy ce tazo ta d'auke su."
da sauri Aunty ta ce "Ta kai su ina?."
"Mu ma bamu sani ba."
cewar Sumayya.
Aunty zata kuma magana aka turo kofa Ajmaal ne ya shigo cike da d'okin ganin yaran.
Sumayya tayi saurin cewa
"Ya Ajmaal Mommy ta zo ta d'auki yaran ko kuna tare da ita ne?."
"Mommy'n ina ta kai su!?."
yayi maganar hankali tashe.
Sumayya tace
"Muma bamu sani ba kawai zuwa tayi ta d'auke su ta fita, kafin Aunty ta dawo daga sallah."
da sauri ya aje shopping bag d'in hannunsa yafita da sauri.
yana kiran Abdulrahim a waya.
"Ya Abdulrahim kana ina Mommy fa tazo ta d'ibi yaran nan, yanzu na shigo asibitin wai bata jima da fita ba ta d'ebe su."
d'ip ya katse kiran.
Ajmaal ya zaro wayar yana binsa da kallo.
sai kuma ya juya da sauri ya koma room d'in.
yana kuma tambayar su Miemie yadda akayi.
Aunty ko hankalin ta ya kasa kwanciya ta kira Daddy ta sanar masa.
Abdulrami bai d'au minti 20 ba ya iso asibitin.
da karfi ya turo kofar room d'in yana ware idanunsa akan gadon.
Feeryal na kwance tun da ake maganar bata furta ko kalma d'aya ba.
da sauri Ajmaal ya ce
"Ya Abdulrahim nayi ta kiran wayar Mommy bata d'auka."
da karfi ya juya ya fita Ajmaal yabi bayan sa........!

Cikin hanzari ya shige mota, Ajmaal ya bud'e d'aya gefen ya shiga yana cigaba da kiran Mommy da har yanzu bata d'aga ba.
da karfi ya fige motar da mugun gudu, suka haura titi.
da sauri Ajmaal ya kunna computer motar yasoma tracker ya shiga lalub'o ta in da Mommy take.
da sauri ya d'ago yana nuna computer yana cewa
"Ya Abdulrahim kilomita 15 ta hanyar titi ta baya kilomita 10 tazaran mu da su, sun doshi Cea, sun sauka a titi suna bin hanyar kasa a lamu ya nuna ta baya zasu bi,
idan mukabi hanyar titi yafi garanti sai dai za'ayi jinkirin isa, ta baya hanyar ba kyau bazai yuwu ayi gudu ta hanyar ba."
kafin Ajmaal ya rufa baki ya juya sitiyarin motar yabi ta hanyar da yake gaya masa babu kyau, yaja sit belt ya d'aura.
Ajmaal ya kwalalo ido yana kallon yadda ya figi motar kamar zai watsar da su, ba shiri ya ja sit belt shima ya d'aura, yana gyara zaman sa idanunsa akan d'an'uwan nasa ganin yadda jijiyoyin hannun sa suka firfito damatsan sa suna bud'awa, yayin da fuskarsa ta juye ta rikid'e izuwa na tsananin b'acin rai, idanunsa sukayi jajir.
gudu yake baya sanin inda yake saka tayun motar tasa.
Ajmaal idanunsa akan computer yana gaya masa adadin sauran lokacin da ya rage su cim musu, da ta inda zaibi.
kiran Daddy ya shigo wayar Ajmaal, Ajmaal ya bashi adireshin in da su Mommy suke.
yana kashe wayar
da sauri Ajmaal ya d'ago yana cewa
"Ya Abdulrahim sun tsaya a kusa da gab'ar Cea!
muna daf da cimmusu."
kure gudun motar yayi wanda duk tsananin gudun da yake, ganin nawar gudun yake, da karfi ya naushi sitiyarin motar badun ingantacciyar mota ce mai tsadar gaske ba, da tuni ya tarwatse sitiyarin nasa.
sai da Ajmaal ya razana..
Chapter 35 · 0% Book details