← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 61

Sashe 60

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da Aunty ta mata arba'in ta koma sashinta kullum, 'ya'yan a wajenta suke wuni, ta had'a su duk uku Zahra Saddeeq Haydar.
dan Zahra dama tun daga yaye ta riketa,
shima Abdulrahim ya ce dama Zahra nata ne anbar mata.
Aunty ta zamo maman yara itama,
idan tana tare da su wani dad'i take ji, tayi ta wa Allah godiya da ni'imar daya mata da samin nagartacciyar d'iya Feeryal data samar musu 'ya'ya uku cikin shekaru biyu.
suma wata takwas sukayi tafiya kamar Zahra, gasu da wayo sosai.

Rayuwa mai tafi a sanu a sanu,
raruwa mai kyau da tsafta ake shinfid'a shi a wannan gida.
rana d'aya Daddy ya fidda sanarwar zai had'a Ajmaal da Miemie aure.
babu kuma b'ata lokaci akayi auren.
duk da zuciyoyi biyun basu amminta da junan su ba, amma a sannu a sannu suka sami kyakkyawar fahimta wanda har ya kai ga zuciyoyin su kulla alakar soyayya, mai tsafta.

Abdulrahim ya shirya musu tafiya Yelwan Shendam,
shi da Feeryal da Saddeeq da Haiydar, da yanzu suke da shekara d'aya.
dan Bappa Salihu kullum sai ya masa fad'a rabon da yazo musu ya jima.
ta jirgi suka tafi suka sauka a Jos.
koda suka sauka a airport na Jos motar daya zo taran su yana jiransu.
shi ya karb'i driving d'in da kansa, in da yasa
direban ya basu motar ya tari taxi shi ya tafi a ciki.
hanyar Yelwan Shendam suka d'auka, ba tare da ya biya gidan 'yan'uwan su dake cikin garin Jos ba, ya ce sai sun dawo zasu tsaya a Jos.
daga shi sai ita sai 'ya'yan su suka haura hanya.

Tun daga farkon shiga garin ta san cewa garin arziki ne,
garin da ya tara kabilu da yawa garin niman kud'i garin arziki.
manya manyan motoci ne suke kiliya da su,
sunyi lodin doya wasu sun loda shinkafa wasu gero wasu dawa, wasu masara.
ga wasu kuma lodin auduga, rid'i da kuma gyad'a.
ido kawai ta baza tana mamakin shin wannan wani irin gari ne mai tarin arziki,
ace duk wad'an nan manyan motocin daga cikin garin suke fita,
da kayan masarufe irin haka.
kai ta jinjina a fili ta furta
"Lallai wannan gari yaci sunan sa Yelwa, babu shakka garin Yelwata ne, ga yadda ake fita da amfanin gona lallai an jinjinawa al'ummar Yelwan Shendam, tabbas garin ku mai yalwa ne."
tayi maganar tana kallon fuskarshi.
karamar dariya ya yi tare da kashe mata ido ya ce
"Garin ya burge ki ko Yelwan Shendam d'in ke nan tushin Alhaji Shitu Fiya, a nan aka haifi Daddy da Mommy, mafarin AA FIYA ke nan nan."
murmushi tayi tana kwantar da kanta jikin kafad'ar sa ta ce
"Garin ya burge ni tun ban shiga cikin sa ba, lallai an tara manoma a wannan yankin."
murmushi ya yi yana shafo gefen fuskarta ya ce
"Bakiji an ce noma tushin arziki ba."
ido ta lumshe tana dad'a narkewa jikin ta ce
"Tabbas na sani."
"Kina dai ji ana fad'a me kika sani a kan noma."
ya yi maganar yana leko fuskarta
"Ai kaima baka sani ba Daddy ne yasan wannan."
"Digiri nake da shi a harkar noma, ko Daddy sai dai ya nuna min jimawa a harkar ba dai kwarewa ba,
Daddy baya so na gaje shi kamar yadda shi ya gaji mahaifinsa,
burinsa na zamo likita,
bayan na zamo kwararren likita natafi naje na karanci harkar noma har na yi digiri a fannin ba tare da ya sani ba."
baki ta bud'e ta ce
"Yanzu duk jimawar da kayi Daddy bai sani ba."
kai ya girgiza yana murmushi ya ce
"Ai baki sani ba wai ni b'oye masa nake ashe ya sani sarai,
ba'a jima da gaya min yasan me nake ciki ba, da san da na fara karatun da san da na gama har kasar da nayi karatun duk sai da ya gaya min."
dariya duk suka yi ta rungume shi tana cewa.
"Kai da kana ganin kayiwa Daddy wayo ashe kallonka kawai ya ke, har nayi niyyar muna komawa zan sanar masa."
kumatun ta ya ja ya ce
"Basai kin fad'a masa ba ya sani."
murmushi ta yi tana kuma lafewa jikinsa.
fuskarta ya leko ya ce
"Beauty kin d'au ciki fa mu koma a yaye Saddeeq da Haydar."
ido ta waro sai kuma ta mike a jikin sa da sauri tana kwab'e fuska da leka yaran da suke bacci a sit d'in baya,
ta dawo da kallon ta gare shi kamar zatayi kuka ta ce
"Sahab ciki kuma shekaran su fa 1 da wata 2 ne."
kiss ya manna mata ya ce
"Meye abin tada hankali yara da kuzarin su da kafarsu, Allah yasa biyun kika kuma d'auka, mu koma na duba mu gani."
"Ni dai wlh aa haba dan Allah duk shekara mutum yayi ta haihuwa."
"Ai kiji a ranki 12 zaki haifo min, kina haifo wad'an biyu na cikin zan kuma saka wasu biyun a cikin ki kara haifo su duk shekara."
kafa ta shiga bubbugawa tana ture shi.
ya rika dariya cike da shauki, kamar ba DOCTOR ABDULHARIM AA FIYA ba ne.

Koda suka isa taga karamci da soyyar agurin mutanen garin Yelwan Shendam, takuma ganin girman su, mutane masu karamci da son jama'a.
kwanan su biyu suka juya.
sukayi kwana d'aya a Jos suka bi jirgi suka koma legos.
a gidan sa da lokacin da ya karb'ota a hannun 'yan kidnapping ya kai ta can sukayi kwana uku, nan suka sauka.
washegari bayan sun huta, ya d'auke ta suka je asibitin sa.
yana gwadata yaga ciki wata biyu a jikinta.
daga asibiti suka nufi AA FIYA STREET.
suna tafe a mota yana rarrashi, dan kuka ta saka masa har da cewa a cire kicin.
ya ce abun da zai tab'a yuwuwa ba ke nan.
suna isa gidan ta sauka ta bar mishi yaran a gurin ta shige parlour'n Aunty da gudu.
Aunty na ganin ta tare ta da sauri.
ta saka kuka Aunty duk ta rud'e tana tambayar ta me ke faruwa.
cikin muryar kuka ta ce
"Ammie na ce ya cire cikin wai bazai cire ba."
a take Aunty ta fahimci wani cikin take da shi.
zatayi magana sai ga Abdulrahim ya shigo da yaran a hannunsa.
Aunty ta ce
"Yauwa Abdulrahim kawo su nan, aje a kawo min kayansu, ke kuma kar na sake jin maganar zubar da ciki a bakin ki,
in duk shekara zaki rika haifo 'ya'ya uku duk ki kawo mun su zan rike."
Aunty ta sab'i d'aya a baya ta d'au d'aya a hannu.
Zahra ta taho da gudu ta rungume ta tana
"Ammie nima ki goyani."
Aunty tayi dariya tana shafa kanta ta ce
"Aunty Zahra ai yanzu ke Aunty ce, ki bari anjima zan goyaki."
Abdulrahim ya yi murmushi ganin yadda yaran suka shaku sosai da Aunty.
ta ce a je a kawo mata sauran kayansu dan rabin kayan nasu yana wajenta.

Suna fita ya janyo ta jikinsa ya ce
"Kin ji da kunnen ki ko, bani kad'ai ke son yara da yawa ba, har da iyayen nawa."
fuska ta kwab'e tana turo lips.

A ranar ya d'auki matar sa suka koma gidan sa, a can suke yin rainon wannan cikin.....

Bayan wata tara.

Feeryal ce zaune a parlour ta ta saka cikin ta gaba, tana cin kayan fruit, ita kad'ai ke zaune a parlour, Abdulrahim ya tafi asibiti.
tun da cikin nata yakai watan haihuwa baya fita yana tare da ita, suna zaune ya sami kira daga Dr Omar High doctor of general hospital, kiran gaggawa yazo ya taimaka musu da wani C'S d'in da ya shige musu duhu.
karar dirowar abu taji a bayan ta, da sauri ta waiga.
ta wani irin zabura ganin wasu halittu biyu sun bayyana a bayan ta.
kafin tayi aune sun d'auketa sun b'ace da ita.

A can cikin fadar sarki bakaken aljanu, daya tura dakarunsu su d'auko masa Feeryal.
wan da Sarki Aljani Matip yake ganin komai,
a take ya bada izini wa dakarunsa da suka yi shekara da shekaru suna zaman jiran umurnin sa, kan kamo azzaluman nan,
kafin isowar su da ita sarki aljani Matip, ya umurci dakarun nasa sukaje suka kamo mishi sarkin babaken aljanu ad'aure.
in da sauran dakarun suka zarce kogon sarkin bokaye boka Lazzi da boka Mali, da sauran mabiyan su sauran bokaye masu b'arna a ban kasa.
aka durkusar da su gaban sarki Matip.
Feeryal da ke tare da dakarun sarkin babaken aljanu dakarun sarkin Aljani Matip suka kamasu tare da ita suka kaisu fadar sarki Matip.
a take a gurin Sarki Aljani Matip ya yanke musu hukunci dai-dai da laifukansu.
Sarkin bakaken aljanu aka d'aure shi cikin kejin karfen da akayi shekara da shekaru ana kerashi wanda babu makaren da zai iya bud'e shi har ya kare rayuwar sa ya mutu.
sannan aka d'auke shi aka jefa shi cikin tsakiyar tekun Matip.
sauran mabiyansa aka jefasu a kurkukun da shima babu fita, manya manyan aljanu ne majiya karfe ke kula da gurin,
su boka Mali suma aka kai su kurkukun da aka d'aure Umma Karima ciki, aka had'ata da su akacigaba da hukuntasu...

Tun da ya shigo bai ganta a parlour ba, da sauri ya shige cikin bedroom yana fad'in
"Beauty kina ina?."
ganin bai ganta cikin d'akin ba ya wuce bathroom nan ma taba ciki.
da sauri ya fito yana leka sauran d'akunan da kinan sunan ta.
amma wayam bata nan.
cikin hanzari ya fita ya nufi gurin mai gadi yana kiran wayarta yana shiga amma ba'a d'agawa.
ya tambayi mai gadin ko ta fita ne.
mai gadin yace tun fitar sa bata fita ba tana ciki.
shiru yayi da tunanin iri-iri cikin kwakwalwa da zuciyar sa.
sai kuma da sauri ya nufi gurin mota ya shiga da mugun gudu yafita a gidan.
ya kunna computer motar yasoma tracker yana tracker in da take ta hanyar bibiyar wayarta.
har ya kawo shi kungurmin dajin da take.
Chapter 60 · 0% Book details