← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 61

Sashe 15

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon kyakkyawan hannunta fari tass mai dauke da zara-zaran yatsu da tayi musu kwalliya da jan lalle ya yi, gami da wayar da take miko masa.
sannan ya mai sa idanunsa kan fuskarta.
da sauri ta yi kasa da kanta jin yadda idanunsa ya yi mata mugun kaifi da ganin ta.
lips d'in ta ta turo gaba ganin bai karb'i wayarba sai idon da ya tsare ta da shi.
ta kuma miko masa wayar, tana kuma cuno lips d'in ta.
ya miko hannunsa ya karb'i wayar kana ya sa kai ya shige.

Tana ganin shigewar sa ta kofar dake sakanin parlor'n ta da nasa, ta gyara mayafin kanta tawuce ta fita ta ainahin kofar fita daga gefen nata zuwa farfajiyar side d'in.
ta nufo get mai gadi ya gaisheta tare da bud'e mata kofa, ta fice.
sashin Aunty ta nufa tana ta kiliya da 'yan biki da gidan ya fara d'aukar jama'a.
wad'an da suka santa suka san da auren ta da Abdulrahim suka rika nuna ta, wasu su yaba wasu su kushe suce 'yar tsuntuwa ce ba'a san asalinta bama.
wad'an da basu santaba kuwa ta zame musu abin kallo da burgewa.
tana daf da isa side d'in Aunty suka had'u da Ajmaal.
murmushi tayi masa tun kafin suyi kusa da juna.
shima murmushin ya yi mata.
"Feeryal an fito ne."
"Ina kwana Ya Ajmaal."
"Lafiya lau Feeryal antashi lafiya."
murmushi ta kuma tana fad'in
"Lafiya lau."
da sauri yasa kai yawuce yana jin zuciya na kokarin kawo masa abin da bai dace ba a kan ta, da sauri ya kwab'i zuciyarsa da take bijiro masa da yanzu ita ce mallakinsa.
ya sanarwa zuciyar
ita d'in haramiya ce a gare sa mallaki ga d'an'uwan sa.

Da sauri ta shige parlour'n Aunty cike da son ganin ta, tun daga bakin kofa take kwad'a mata kira
"Ammie Ammie Ammie."
Aunty ta fito daga cikin bedroom da sauri jiyo muryar ta.
da sassarfa Feeryal ta tafi ta rungume ta tana dariyar murnar ganin ta.
Aunty ta rike baki fuska d'auke da fara'a ta ce
"Ke Feeryal waya ce ki fito?."
baki ta cuno cikin muryarta mai sanyi gami da shagwab'a ganin ta gaban Ammie'n ta ta ce
"Ammie ai ina so na ganki ne, idan nazo sai kiyi ta ce na koma, ni dai kwana zanyi yau, kullum ni kad'ai zanyi ta zama, danma Chuchu da Chulu suna zuwa, Miemie ma tana zuwa amma bata jimawa, ni kawai na dawo zan zauna a nan tare da ke."
Aunty tayi dariya ta ce
"To ke da kike da 'yan taya hira ma, kawayen ki suna zuwa kullum suna tayaki hira, bakiga ni kad'ai nake rayuwa ta ba, sai in Daddy ya zo ni nake samin mai taya hirar,
sai kuma idan kin haifo 'ya'ya dozen duk zan kwashe su na rike, kinga na sami 'yan hira ke nan ni ma."
kafad'a Feeryal ta make tana b'oye fuskarta jikin Aunty.
Aunty ta kuma yin dariya ta ruko hannunta tana cewa
"Zauna dai ki ci cake da yogurt yau bazan mai da ke a kan kafarki ba."
ta zauna kan kujera Aunty ta shige kitchen tana jin kewa gami da kaunar d'iyar tata,
bataki ace ta zauna sucigaba da rayuwar su ba, amma ina sawun giwa ya kere na rakumi.
ta fito mata da Cake da yogurt mai sanyi dai-dai misali, ta aje a gabanta kana ta zauna gefenta aiko da sauri ta gyara zaman ta ta soma ci, suna d'an tab'a hira irin na d'a da uwa.
a hankali take ci dan bata so taci da sauri Aunty tace ta tafi.
ai ko Aunty ta gane wayon ta ta tasan cikin ta duk son cin cake d'in nata bata ci yawuce yanka uku zuwa hud'u.
Aunty tana ganin ta ci yanka uku
koma kitchen ta d'ebo da yawa ta kawo mata tace.
"Tashi muje na rakaki ga wannan sai kije ki aje ki wuni kina ci."
kamar zatayi kuka tashiga bubbuga kafa kasa tana fad'in
"Ammie ni dai zan zauna."
Aunty ta ce
"Aa Feeryal ki koma d'akin ki, ta so maza."
ta ruko hannunta ta mike suka nufi kofa tana bubbuga kafa a kasa.
a bakin get na side d'in Aunty ta tsaya ta ce
"Maza ki koma d'akin ki karki kuma fito wa sai kinyi fin wata kafin ki to."
ido ta waro ta ce
"Ammie har wata to ai jibi ma zamuje dinner."
"Aa Feeryal ki zauna a d'akin ki a bin ki me zai kai ki wani gurin dinner."
"Ammie Daddy ne fa da kansa yamana ashobe."
"Ke dai jeki maza kar ki tsaya ko ina."
ta fita badan ta so ba.
a b'angaren Aunty itama ji take kamar karsu rabu, sai dai ta b'oye gudun kada Feeryal d'in tasami mafakar tuburewa..

"Ke Feeryal."
taji an ambata a bayan ta, da sauri ta waigo, Nabila ta gani.
Nabila ta wurga mata kallon banza sannan ta ce
"Kije ana kiran ki a can."
Feeryal takalli in da Nabila take nuna mata, mutane da yawa a gurin wanda ta gane cikin su Umma Karima da Siyama ce kad'ai.
Nabila ta juya a hankali tabi bayanta.
tun kafin ta karaso Siyama da Umma Karima suke aika mata kallon tsana.
har ta karaso gurin Umma Karima takuma wasa mata kallon banza tana fad'in
"Kunganta nan wannan kyawun duk na gaibu ne,
in banda aikin asiri me Abdulrahim zaiyi da tsintacciya, wacce tagama bin maza har cikin gidan nan an kamata da wani, wai ita ce surukar Hajiya Halima, ai Hajiya Halima ta bada mata wlh datayi sake aka mallake mata d'an da ta haifa a cikin ta,
in nice tuni ban shafe babin su ba, mujen ku dan Allah."
Umma Karima tayi gaba bayan ta kuma wasa mata kollon wulakanci.
Siyama ma haka harda jan dogon tsaki.

Feeryal tabi bayan su da kallo kana ta juya.

Umma Karima tun kafin su shige sashin Mommy take yab'a magana mai nuni da kaskanci gami da wulakanci, kan Feeryal har suka shige sashin nata.
Mommy ta tare su tana fad'in
"Meke faruwa ne Hajiya Karima?."
Umma Karima ta yamutsa fuska tana cewa
"Saken da kikayi ne ya bani mamaki, har yaushe zaki bar nagartaccen d'anki ya cigaba da zama da wancan kaskantacciyar yarinyar data gama tambad'e wa a waje, wlh Hajiya Halima kina bani mamaki."
Mommy ta ce
"Hmmm Hajiya Karima kibar wannan maganar tukun a gama bikin nan, ni nafi kowa son ganin naraba yaron nan da yarinyar nan, dan wlh ni banyi na'am da ita a matsayin sirikata ba, dole zai saketa dan ban shirya had'a jini da aljanu ba,
shiyasa ma na gargad'e sa kada ya sake yace zaije gareta da wata bukata ta aure, bari jama'a su watse daga gobe zuwa jibi gata zakiga hukuncin da zan yanke."
Umma Karima ta ce " Da dai ya fi gara ki farka daga baccin da kike."
kawayen nasu kuwa kowa ya cigaba da tofa albarkacin bakin sa wasu na fad'in
gara ta farka gida kamar wannan ace sirikar gidan ta kasance haka, wasu ko cewa suke tun da har an bari ta aure shi to a hakura kawai a barsu,
masu fad'ar haka kuwa Umma Karima ji take kamar ta nitsa musu mashi a zuci.

In da sabo ta saba tana shiga gefen ta takama wasu tsabgogin ta mance da duk tozarcin da Umma Karima tayi mata.

Bayan kwana uku ta kasance ranar d'aurin auren Yusuf da amaryar sa.
anata shagalin biki Feeryal tana gefen ta ko sha'awar fita bataji.
magana tajiyo a parlour tana kwance a bedroom,
ta mike tafito, ta tsaya daga bakin kofar bedroom.
su Ameerah ta gani da wasu 'yan'uwan su da sukazo daga Yelwa, 'ya'yan Kawu Sani ne kannen angon Yusuf.
duk 'yammata ne kansu d'aya, su uku sai ita na hud'u.
"To gata nan da kuke ta dami na nazo na kai ku ku ganta, ni fa kar kusa yarinya ta rainani."
cewar Ameerah tana yamutsa fuska.
tare da ci gaba da fad'in
"Idan kun gama kallon ta kamar TV sai ku fito."
ta juya tayi waje.
Feeryal tabi bayan ta da kallo tana mamakin yanzu Ameerah bata cika tsayuwa a gaban ta tana mata rashin mutuncinta data saba ba, sai dai ta tsaya daga nesa, tana mata kuma zata juya, ta kauce daga in da take.
hankalin ta ta mayar kan 'yammantan da taji suna cewa
"Ai kuwa da gaske ne kamar balarabiyar."
murmushi tayi musu ta ce
"Kuzauna nakawo muku ruwa."
ai ko suka zauna, ta shiga kitchen ta ta d'ebo musu drink's da donut da nama ta kawo musu.
suka karb'a suka kuma yi mata godiya.
tayi murmushi tare da zama a gefe.
suka kusa cinyewa kuwa kafin suka mike sukayi mata sallama.
tun kafin su fice daga side d'in suke maganar ta,
d'aya daga cikin su ta ce
"Ni kam banga aibunta ba da su Ameerah suke kushita ba, gata kyakkyawa kamar ita tayi kanta."
sauran suka ce ai kuwa kam suma basuga makusa a tare da ita ba.
suna koma sashin Mommy Ameerah ta harare su tana fad'in
"Ku har wani iya zama kukayi a gurin ta."
"Wlh tana da kirki har abinci ta bamu, ta zauna mukayi hira, ita wacce kike yabon nata ma ko kallo bamu isheta ba."
suka had'a baki wajen fad'a.
hararsu tayi ta ce
"Kwad'ayayyu sai kun ci abincin aljanu ai."

Ana sallar magriba Miemie ta shigo side d'in Feeryal da sauri.
tana zaune a kan sallaya ta idar da sallah ke nan.
Miemie ta rike hab'a tana fad'in
"Wai ke Feeryal ko da yaushe in dai za'aje wani guri kullum ke ce karshen shiri, dan Allah ki tashi ki shirya kafin ayi isha, 12 fa za'a tashi dan yau zasu wuce Jos."
"To yanzu zan shirya."
Miemie tafi tana fad'in
"Kiyi sauri zan kira ki idan muka fito."
ta ce tom.
Chapter 15 · 0% Book details