← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 61

Sashe 58

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk suka cika da mamakin jin tun jiya da 12 na dare ta haihu.
ya karb'i haihuwar ya yi komai da kansa.
bai sanar ba kuma har sai da rana tayi.
suka rika yi masa sannu suna yaba mata da kokarin haifo katuwar 'ya haka.
Hajiya tasa Goggo Bishira taje ta d'auko gabaruwa da lalle, tazo ta saka cikin babban tukunya ta zuba ruwa ta d'aura kan gas.
ana ta hira
Mommy tayi shiru tana ta sakar zuci
"Ina zai gayawa wani tana nakuda yana gudun kada wannan karon ma na kuma kashe masa 'ya, kauco na hakika ni Halima nayi asara, na kashe jikokina maza biyu da hannunan."
lura da halin da Mommy ta shiga Aunty ta miko mata jaririyar tana cewa
"Karb'e ta Mommy'n Ameerah wannan zata karya min hannu."
murmushi Mommy ta yi tana b'oye yanayin da ta shiga ta karb'e ta tana fad'in
"Ai Feeryal ta sha fama wajen d'aukarta a cikin ta, gashi sai karkata baki take wannan za'ayi acici a nan."
Ammah ta ce
"Ai kuwa dai ga baban ta ya hana a bata ruwa, idan maman tayi wanka tasha tea mai zafi, zata sami ruwan nono akan kari."
Hajiya ta fito daga bayi rike da bawun da ruwan wankan jaririyar ciki tana fad'in
"To taso Fatima kije ki wa mai jegon wanka, ga ruwa na had'a a bayi,
Bishira je ki juyo gabaruwan ya rika shan iska kafin a gama mata wankan, sai ki sa ta shiga."
Aunty ta dubi Feeryal tun d'azu take like a jikinta ta ce
"Taso muje kiyi wanka."
Aunty na mikewa kiran Abdulrahim na shigowa wayar Hajiya,
Hajiya ta d'aga tana kwad'a masa sallama, daga cikin wayar ya ce
"Yau wa Hajiya na mance ban gaya miki ba, karfa kuyi wa Beauty wanka da ruwan zafi sosai."
Hajiya ta ce
"Yoo ai ba ni zaka gaya min ba sai ka gayawa iyayen ka, kai tun kan a haifi uwan ka da ubanka nake karb'ar haihuwa,
kai zaka gwada min yadda ake wankan jego, yanzu zan tura Ajimi ma yaje ya ballo min dalbejiya, in dai so ake tayi kwari kuwa dole sai an bigi jikinta da ruwan zafi."
Hajiya ta kashe wayar tana cewa
"Jimin d'an nan ka rika sakowa mutane bidi'a cikin lamari."
Ammah ta yi dariya ta ce
"Hajiya kin san fa yanzu sai a hankali cututtuka sunyi yawa,
shi likita ne yafi mu sanin me yasa ya ce hakan,
a dai bi abun da ya ce d'in."
Hajiya ta soma mita
"Mu da da akayi mana mun mutu ne, yara da kalen fitina."
Aunty dai batayi magana ba taja Feeryal sukayi cikin bayi,
ta kara ruwan sanyi cikin ruwan zafin da Hajiya ta tara cikin bathtub.
tayi mata wanka sosai sannan ta sata ta shiga ruwan gabaruwa da lallen da Goggo Bishira ta dafa.
koda suka fito daga bayin
Mommy bata d'akin,
dan tun shigar su bayi ta fita a d'akin a matsayin ta na suruka.

Ammah ce ta shirya jaririyar bayan Hajiya ta mata wanka.
Feeryal na gama shiri, Aunty ta had'a mata tea mai kauri ta sha.
sai a lokacin Hajiya tabar su Ameerah suka shigo, dan ta koresu duka ta ce suyi waje sai an gama kafin su shigo.
suka rika d'aukar yarinyar suna santin katanci da kyanta.
Miemie ta matsa kusa da Feeryal tana fad'in
"Ke kinga wani kyan da kika kara kamar ba ke ce kika haihu ba, ke na fahimci ma fa haihuwa kyau yake kara miki."
murmushi Feeryal tayi tana hararar ta.

Ko da aka ragu a d'akin Aunty ta d'au 'yar ta ce ta bata nono, dan tun d'azu take ta kuka tana niman nono.
Aunty na tallafe da jaririyar, ita kuma ta saka mata nonon a baki,
ja d'aya ta fizge a bakin ta da sauri tana fad'in
"Wash!."
Aunty ta ce "Bata kafin ya kara tsami in yakai anjima baki bata ba zafi zai kara."
fuska ta kwab'e ta ce
"Ammie a barta kawai a bata tea."
"Tea kuma Feeryal jaririyar, kina dai ji baban ta ya ce ko ruwa bai yadda a bata ba,
daure dai ki bata tasha."
ansha dabi da ita kafin ta barta tana sha tana matse ido har da kwalla.
yarinya ko ta koshi har tayi bacci.

Bayan sallar azahar Ajmaal Shamsuddin da Faisal suka biyo bayan Daddy suka taho sashin Feeryal,
a parlour suka zauna Aunty ta fito musu da jaririyar.
sai da duk suka d'auke ta kafin suka bai wa Daddy, Daddy dai murmushi ya yi ta yi, ya ce
sun nuna masa wariyar launin fata saboda 'yarsu ce.
Feeryal ta fito suka gaisa Daddy yana ta sanya mata albarka.

Farida har da nama ta girkowa mai jego, ta kawo mana.
da daddare Zaraddin da matarsa Saddiqa suka shigo gurin mai jego,
suma suna zaune lafiya da mijin ta ba'a tab'a jin kansu ba,
sunyi wa kowa bazata.

Aunty ke zaune a kan d'iyar ta,
akai-akai ya ke shigowa duba lafiyar matar sa da 'yar sa,
sai dai da ya shigo baya zama zai fita sabo da Aunty da kuma 'yan barkan da suke zuwa.
kwana uku da haihuwar da safe ya shigo ya yi wa yarinya hud'uba da suna Fatima.
wayyo zo kaga murna gurin Aunty anyi mata takwara, taji dad'i kwarai da gaske na karamcin da ya nuna mata.
da zai fita ya ajiyewa Feeryal sabuwar waya a kusa da ita.
yana fita ta d'au wayar tana dubawa an saka komai cikin wayar.
tana rike da wayar kira ya shigo, ko da ta d'aga muryarsa ta jiyo yana fad'in
"Baby bata koshi da nono ba ki kara akan wanda kike bata, a gajeren kari tayi minti 20 tana sha, ki kula da kanki ki ci abinci sosai."
fuska ta kwab'e kamar tana gaban sa, ta ce
"Har minti 20 da zafi fa, ai zata iya shan tea a rika bata ta na sha kawai."
da karfi ya ce
"Beauty! sai kuma ya sassauta murya
"Please kar ki bata tea bata kai na shan tea ba."
shagwab'e fuska tayi tana sauke wayar.
Aunty ta dube ta ta ce
"Maganar tea d'in nan ya fita a bakin ki, kar watarana ki ce zaki bata."
fuska ta kwab'e ta gyara kwanciyar ta,
itafa maganar bada nonon nan bata son shi zafi yake mata.

Aunty takira Daddy ta gaya masa Abdulrahim ya mata takwara.
Daddy yaji dad'i sosai.

Ana gobe suna Aunty Zainab wato yayar Aunty da Maryam suka zo daga Lagos.
'yan Yelwan Shendam ma sun sami zuwa.
gidan ya cika ana ta shirya in da gobe zata kasance.
tun a yau d'in aketa yanke yaken shasu da raguna da aka kawo su daga gidan gona,
ma'aikata suna ta aiki.
da daddare suna tare a d'aki ya kirata a waya, ya ce ta zo ta same shi a gefen sa,
ta zame jiki ta nufi gefen sa.
tana shiga bedroom d'in sa ya mike ya janyo ta jikinsa ya rungume ta.
"Ina baby?."
ya fad'a yana janyo ta bakin gado.
ta ce
"Tana goye a bayan Ammie na."
kai ya jinjina
yana zama tare da zaunar da ita acinyarsa, ya tura hannunsa cikin rigarta ya cafko ababen kirjin ta da suka kara cika da girma.
ido ya lumshe yana matsotsu a hankali, a sannu itama ta lumshe idanunta tana dad'a shigewa jikinsa.
ya tallafo kanta ya had'e bakinsu yana sha da zafi-zafi, nan da nan ya birkice mata ya kwantar da ita, ya zare rigarta, yarika tsotsar ta yana matse ta a jikinsa.
hannunta ya kamo ya d'aura kan dick nashi daya mike samb'al ya kumbura, ido ta waro a tsorace dan yadda ta jishi sai da ya bata tsoro.
ya had'a da abar tasa da hannunta ya matse cikin muryarsa data sauya can kasa ya ce
"Zaki sha."
kai ta girgiza da sauri tana kwab'e fuska
"Ai baka rage girman sa ba ya yi kato zanyi amai."
"No ki gwada."
ya d'ago ya tura mata a baki.
sai da ya kawo kafi ya zare yana sauke numfashi da shafa kanta, yana manna mata kiss a goshi.
sai wajen 11:30 ya rako ta har kofar da zata shiga gefen ta daga cikin nashi, yana tsaye sai da yaga shigewar ta kafin ya juya.
a hankali ta turo kofar, duk idanunsu biyu suna ta hira.
Aunty na rungume da Mai sunan ta tana jijjigata da alama kuka ta fara.
Maryam ta ce "Yauwa karaso Feeryal kiga kayan da zaki fara sawa gobe."
ta d'ago wani dogon riga cikin d'inkin da aka mata na fitan suna kala 20.
ta ce "Wannan zaki fara sawa sannan wannan."
ta rika d'ago kayayyakin tana nuna mata.
Feeryal ta ce
"Aunty Maryam duk ta ya zan iya sakasu a rana d'aya, ai sai dai na saka kala uku na bar sauran."
"Ke dalla tafi can kala uku kala goma zaki saka duka in Allah ya kaimu."
"Karb'eta ki bata nono."
Aunty ta miko mata 'yar.
ta karb'e ta tasaka mata nono a baki tana matse ido sabo da zafi.
ta ce "Ammie Allah kad'an zatasha, gafa yadda take sha da karfi yana min zafi."
Aunty ta zauna gefen ta tana gyara mata rukon 'yar ta ce
"Bata dai."

Washegari ranar suna gidan ya cika ya batse da mutane,
ma'aikatan hotel da aka kawo, suna ta d'aura manyan tukwane anata dafe-dafe da soye-soye.
manyan raguna uku da shanu uku Daddy yasa aka kuma d'ebowa a gidan gona banda na jiya, da aka yanka su.
ya ce wannan shine na suna, na jiya kuma na mutane.
suna akayi na bugawa a jarida sunan da za'a jerashi cikin jiga-jigan hidimar suna da ake na alfarma a kasar nan.
kayan suna ta kowani fanni zuwa yake,
daga Lebanon aka turo da kaya ta jirgi, daga Abuja ma haka, Daddy ya yi shima nagani na fad'a.
uban tafiyar ma uban yarinyar shima haka, Aunty ma tayi har da na maka suna,
Mommy ba'a barta a baya ba, tayi kaya bana wasa ba.
tsabar yawan kayan har aka rasa a ina za'a saka su.
a babban Hall d'in da ke gidan aka shirya biki na musamman in da aka gaiyato mawaka.
suna fa sai ka gani da ido.
anshirya gift-gift ga duk mai zuwa suna sai ya fita da murmushi.
Chapter 58 · 0% Book details