← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 61

Sashe 37

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Daddy na fita asibiti ya tafi.
Aunty na tsaye a kan kafafunta hankalin ta a matukar tashe.
tun da tayi waya da shi ta sanar masa, Mommy ta d'auki yaran daga baya tana ta kiransa baya d'aga wayar.
tayi ta kiran Ajmaal shima haka.
Sumayya da Miemie hankalinsu ya kasa kwanciya suka nufo gida,
kasancewar babu motar gida dole taxi suka bi, suka b'ata lokaci a hanya.
Feeryal na kwance tayi shiru, Aunty na tsaye da kafafunta.
Daddy ya turo kofar da sallama,
kallo d'aya Aunty ta masa gaban kirjinta ya yanke ya fad'i.
tafi kowa sanin halin mijinta,
kallo d'aya take masa ta karanci farinciki ko bakinciki ke tare da shi.
da sauri Aunty ta nufo shi tun kafin ya karaso, ta ruko hannayen sa hankali a bala'in tashe take fad'in
"Daddy ina yaran suke ina ta kaisu?."
Daddy ya rumtse idanunsa yana jin zafi cikin zuciyarsa.
Aunty ta kuma jijjiga shi murya na rawa ta ce
"Daddy kayi magana, dan Allah ina ta kai su, dan Allah a dawo mana da su, ko nono basu shaba, a kawo mana su ta basu nono kar yunwa ya dame su."
Daddy ya kifa kansa a jikin kafad'arta.
duk yadda yaso ya daure ya gagara, sai kawai ya rushe da kuka mai cike da kuna da matukar tausayin su.
sai kawai itama ta fashe da kukan da tun d'azu take ta danne shi.
Daddy yayi saurin d'ago kansa a kafad'ar ta ya rungumeta.
yana bubbuga bayanta tare da fad'in
"Kiyi hakuri Fad'imatu nayi duk iya yina yau na gaza."
Aunty ta d'ago da sauri ta ce
"Daddy me kake so ka ce."
"Nagaza taimakon jikoki na Halima ta jefa su a ruwa ta kashesu."
ya yi saurin sakin Aunty ya jingina da jikin garu ya dafe kirjinsa yana tari, da sauke numfashi da sauri-sauri.
wani irin rumtse ido Feeryal tayi, jin kanta ya yi wani irin sarawa.
wasu siraran hawaye suka gangaro gefen idanunta.
Aunty da gaba d'aya ta firgice ta d'aura hannu a ka tana salati da fad'in
"Me sukayi miki Hajiya Halima idan ku bakwason su, kun wadata da 'ya'ya mu bamu samu ba, yanzu ke nan Allah ya bamu, mu muna son su."
gaba d'aya ta daburce cikin d'akin tana ta kaikawo da sambatu gwanin ban tausayi.
Daddy na dafe da kirjinsa ya mika d'aya hannunsa ya kamo nata sannan ya furta
"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un."
ai ko da sauri ta cab'e kalmar da furtashi ya samar mata da nutsuwar da har ta juya ga Feeryal dan son ganin halin da take ciki.
ta karaso bakin gadon da sauri ganin hawaye na gangara a fuskarta, ta shafa kanta tana cewa
"Kiyi hakuri, ita wannan kalmar bayan an cutar da kai ake gaya maka ita, idan kayi hakurin kuma zakaga ribar yin ta Allah yana bayan gaskiya."
Feeryal ta bud'e idanunta a hankali, idanunta ya sauka kan inda Daddy yake,
ta d'aga hannu ta nuna inda yake tana cewa
"Ammie Daddy."
da sauri Aunty ta juya numfashin sa na dad'a sama-sama idanunsa yana yin sama-sama.
da sauri Aunty tayi gurin sa ta rike shi tana kwad'awa likita da nurse's kira.
a guje suka shigo jin irin kiran bana kwanciyar hankali bane.
Aunty ta ce "Ku taimake ni ciwonsa ya tashi."
a ka kwashesa akayi da shi wani room d'in.
ranar Aunty taga tashin hankali mara misaltuwa.
ana shiga da shi Ajmaal na isowa, shi ya zauna a gunshi ita kuma ta komo gun Feeryal.
tana kaiwa da kawowa sakanin room d'in da Feeryal take da na Daddy......!

Cikin dare Daddy ya dawo hayyacin sa.
washegari da safe ya bukaci a sallame sa ya
koma gida.
Bappa Salihu da asuban fari ya baro Yelwan Shendam ya shigo garin Jos.
yabi jirjin da ya taso daga Jos ya sauka a airport na Lagos da karfe 9 dai-dai, na safiya.
bai fad'awa kowa zai taso ba shiyasa mota bata je domin tarar sa ba,
taxi ya shiga ya taho AA FIYA STREET.
yana isa ya buga get security suka leko ganin shine sukayi hanzarin bud'e masa karamar kofa ya shiga, suna yi masa sannu da zuwa.
sama-sama ya amsa musu ya shige ciki.
da su Nabila da Sahala da Ameerah suka fara cinkaro sun fito daga sashin Daddy.
shiko kai tsaye sashin Mommy ya wuce.
Ameerah tayi gudu taje ta gayawa Hajiya ga Bappa Salihu ya zo.
tun daga bakin kofar side d'in Mommy Bappa Salihu yake kwad'a mata kira har ya shigo parlour'n ta yana fad'in
"Ina kike mutumiyar banza shashasha wacce ta girma har yau batasan ciwon kanta ba."
Mommy ta fito daga cikin bedroom nata jiki na rawa
Bappa Salihu ya nufo ta ya na cigaba da fad'in
"Halima ke d'in nan da a asibiti aka haife ki da wlh cewa zanyi an canza min 'ya aka bani wacce zata kashe ni,
ban haifi 'yar da zata zo ta zame min fitina cikin ahali ba, gara tun marmaza na cire ki cikin 'ya'ya na tun kafin ki hallaka min ahali,
mutumiyar banza ni ban haifi makashiya ba!."
Bappa Salihu ya rufe ta da duka da hannu bibbiyu yana cigaba da fad'in
"Bani ba ke Halima kada ki sake ki d'aga ido ki kalleni a matsayin mahaifinki,
ke baki isa ki zame mana fitina cikin ahali ba, meye amfanin rayuwar ki ke baki cancanci zama uwa a gurin 'ya'yan ki ba, ke azzalumar uwace mai son kanta."
Sumayya Ameerah da Hajiya suka taho da gudu,
Ajmaal da ya shigo yanzu shima ya taho da sauri.
Hajiya ta shiga sakanin Bappa Salihu da Mommy tana cewa.
"Haba Malam Salihu mene ne haka, mata da girman ta ai ko 'ya'yan ta yanzu sun wuce duka."
Bappa Salihu ya ce
"Ai kin banza abun da ta aikata ai ko 'ya'yan nata bazasu aikata ba, wacce irin kwakwalwa ce da ita irin na dabbobi,
na cire ki a 'ya'yana Halima ke ba 'yata bace, ni ban haifi makashiya ba,
dad'in me zakiji ki kashe jikokin ki da hannun ki wace irin azzaluma ce ke,
na yafe ki Halima na yafe ki,
me ma kika zauna yi anan hukuma basuzo sun tafi da ke ba, hukuma zasu zo su d'auke ki yanzu,
bayan na nuna miki na isa da Abubakar na sashi ya sake ki,
sannan hukuma suyi gaba da ke!."
Bappa Salihu ya fita rai b'ace.

Hajiya tabi bayansa tana fad'in
"Kar ka kira mana hukuma anan, tun da abu ya faru ai shike nan, me ye na kiran hukuma."
sai da suka fito waje Bappa Salihu ya juyo rai b'ace ga Hajiya ya ce
"Ai ya kata hukumar su had'a har da ke su tatta, dan banga amfanin zaman ki a gidan nan ba,
ke Hajiya Hanne kina cikin gidannan b'arna daban-daban yana afkuwa ace har da kisan rai, meye amfanin zaman ki a tare da su, gara ma ki tattara ki koma can gida Yelwan Shendam, ki zauna babu amfanin zaman ki a nan, tare da su."
Hajiya ta mara baki tana fad'in
"Ahap ba yau aka saba min gorin na tafi ba,
idan abu Allah ya kadda zai faru ko ku mazan baku isa ku hana ba."
Bappa Salihu ya yi gaba yana cewa
"Duk hankalin ku d'aya ne da Haliman, Allah ya sawake irin wannan rayuwar."
ya wuce sashin Daddy.

Mommy ta zube kasa zuciyarta ya kariya,
tun da take da mahaifin nata bata tab'a ganin b'acin ransa irin na yau ba.
jikinta ya yi sanyi matuka.
Ajmaal da ya share kwalla yake fad'in
"Mommy meye hakan wlh baki kyauta wa Ya Abdulrahim ba, kin cutar da zuciyarsa dan kin san a zuciya yake barin ko wacce irin damuwar sa,
ba Ya Abdulrahim ba har da mu kika cutar Mommy, domin damuwar sa namu ne bazamu so ganin d'an'uwan mu cikin damuwa zuciyar mu ta sami nutsuwa ba,
muna murna da samin 'ya'ya kika hallaka mana su, Mommy kin san zafin da naji kuwa,
to ina ga shi Ya Abdulrahim mai 'ya'yan, da kuma uwar 'ya'yan,
da wacce ta raini uwar 'ya'yan,
da Daddy da ya zame mana garkuwa,
Mommy kin cutar da zuciyoyi da yawa,
kiji furucin da Bappa yake fad'a a kanki,
ina mu zamu saka rayuwar mu, ace muna tsaye mu 'ya'yan ki, mahaifinki yana kai hannu jikinki da munanan kalamai,
taya kike son mu goben mu tayi kyau, baki daidai ta sakanin ki da mahaifin mu da mahaifin ki da babban yayan mu ba,
Mommy bakiyi mana adalci ba!."
Ajmaal ya fashe da kuka yana kuma fad'in
"Mommy bakiyi mana adalci ba."
Sumayya da tuni ta fashe da kuka ta na cewa
"Ni gara ma na bar gidan nan natafi Yelwa, wlh tun da naga yarannan naji sonsu a raina, Mommy me yasa zaki kashe su,
Mommy da baki kashe su ba,
me yanzu mutane da kawayen mu zasu rika fad'a Mommy'n mu tayi kisa."
Sumayya ta kuma rushewa da kuka.
Ajmaal yayi waje yana share kwalla.
Ameerah da hawaye ya ciko idanunta ta zube jikin Mommy tana share mata hawayen da ke gangara kan fuskarta.
yayin da itama jikinta yayi sanyi..
Chapter 37 · 0% Book details