← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 61

Sashe 30

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana fita sukayi kiliya da Ajmaal zai shigo gurin Daddy.
Ajmaal ya yi masa gaisuwa na girmamawa kamar yadda ya saba, sannan ya wuce parlour'n Daddy.
a tsaye ya iske Daddy da alamar fita zaiyi,
ya karaso yana fad'in
"Barka da warhaka Daddy."
"Yauwa Ajmaal ya aikin kun dawo?."
Ajmaal ya ce
"Eh mun dawo Daddy ai ki Alhamdulillah, dama document d'in nan ne na kawo ma ka sa hanu."
"Shi ne kabar yayan ku ya wuce ai da shi ka bawa yasa hannun kawai, ka bisa ka kai masa ya sa hanu."
Ajmaal ya ce to, har ya kai bakin kofa Daddy ya ce
"Ajmaal kana da labarin kun sami d'a ko 'ya kuwa?."
da sauri ya juyo ya ce
"Aa Daddy haihuwa akayi ne wa ta haihu?."
"Ba haihuwa akayi ba tukun Feeryal ce ke da juna biyu, zaku sami d'a bada jimawa ba, in Allah ya yarda."
Ajmaal da farinciki ya lullub'e shi ya wani tuma tsalle yana fad'in
"Yes! masha'allah im very happy."
Daddy ya bishi da dariya ganin ya juya da gudu ya yi waje..
Ajmaal bai tsaya ko ina ba sai sashin Mommy.
yana shiga da d'in bin farinci ya ce
"Mommy albishirinki Feeryal na da ciki."
Mommy Umma karima Siyama Sumayya Ameerah duk suna zaune cikin parlour'n.
dukkanin su zabura sukayi tare da had'a baki wajen fad'in
"Ciki!."
"Wallahi da gaske ciki take da shi."
ya yi maganar da farincikin daya gaza b'oyuwa tare da shi.
Umma karima da maganar ya nasheta yakusa kashe ta a zaune.
ta kasa iya furta komai.
sai zazzare ido take kamar tsohuwar mayya.
Mommy ko zama ta gyara
tana murtuke fuska "To sai me zaka zo kana fad'a min, ai dama karshen alewa kasa an turata yawon bariki kam ta ya bazatayi ciki ba."
"Mommy yawon bariki kuma? ciki kam ai na Ya Abdulrahim ne."
da sauri ta ce
"Kai kutumar ubanka, idan na sake jin maganar nan a bakin ka sai na ci maka mutunci,
au tanan aka b'ullo taje tayi ciki za'a lankayawa Abdulrahim, shi da yake nan ita tana can wata duniyar, sabo da a b'ata masa suna to duk wanda ya fad'i maganar nan wlh bazan kyale ba."
"Allah ya baki hakuri Mommy amma ciki kam na sa ne, dan watannin cikin sun nuna nasa ne."
Sumayya dake ta washe baki tun san da ya fad'a
ta ce "Alhamdulillah zamuyi baby, Ya Ajmaal Feeryal d'in ta zo ne?."
"Tazo gidan uban ki wa ai wlh ba a isa a yi min wanna sakar zaren ba, zancen banza fita ka bani guri, naga uban da ya isa ya ce cikin nasa ne, dan uwar ki ke Sumayya da kike cewa zakuyi baby, d'an shegen ne abun alfahari,
tukunna ma yaushe Feeryal d'in tazamo dangin ki, ko kalen dangi kika soma, na sake jin maganar nan a bakin ku sai na ci ubanku dukan ku, shegu marasa mutunci da rashin sanin ciwon kai."
Ajmaal kam tuni yayi waje abinsa bai ma tsaya jin abun da take kuma fad'i ba.
sai yanzu Umma karima ta sauke numfashi had'a da mulmulo wani uban ashar ta d'auna.
"Tamd'ijam! wata sabuwa wallahi karya ne!."
ta fad'i tana buga kafa a kasa.
Mommy ta ce
"Zancen banza ne ma kawai."
Umma karima ta mike zumbur ta yi waje.

Hajiya ta rike hab'a bayan da Ajmaal ya gama fad'a mata zancen.
ta ce
"To ikon Allah yanzu ita yarinyar ciki gare ta, kuma na Abokin turawa ke nan, to ai shi ke nan Allah ya raba lafiya, amma wannan d'a ko ya zaizo haka zai fito irin uwarsa mutum-mutum aljani-aljani."
Ajmaal na fita Umma karima na shigowa.
ta nimi guri ta zauna tana fad'in
"Hajiya kin ji wani sabon labarin da ya fito a gidan nan kuma ko, wai Feeryal na da ciki ana son juya lamarin ya dawo kan Abdulrahim."
Hajiya ta ce
"Yanzu wannan yaro Ajimi ya zo min da batun, na ce ko wani irin d'a za'a haifo, jinsin aljanu da mutane."
"Hajiya cikin nan fa bana Abdulrahim bane, ko kin mace yarinyar nan a cikin gidan nan na kamata da wani kato ta sakashi cikin hijabi suna iskanci, sannan tun yaushe Abdulrahim ya sake ta, ba'a ce tana da cikin ba sai yanzu,
haba ai wannan zance hankali bama zai d'au ka ba,
duk shiri ne da son a b'atawa gida kamar wannan suna,
wlh idan aka bari akan cikin Abdulrahim ne aka karb'i d'an shege a gidan nan, daga lokacin mutuncin gidan nan ya zube, ta ya ma yariya tana wata duniya a lankaya masa ciki, baya tare da itan ma sai an bida da sharri, in dai cikin nasa ne da gaske me yasa ba'a gansa tun a nan ba sai da ta sa kafa ta tatafi dadironta tayiyo cikin sannan dan ana so ayi rufa-rufa kada duniya susan halin da ake ciki, ace wai cikin sa ne."
Hajiya ta ce "To nima dai shi ne na gani wanna zance babu lauje cikin nad'i kuwa, amma bari na nimi Abubakar dan ni bai zo min da zancen ba har yanzu."
"Hajiya idan kika bari aka karb'i cikin nan, wlh ke ce na gaba da za'a fara kwatancen ki dan ke ce gidan gaba d'aya, gara ki kwab'i zancen tun da wuri, suje can su nimi wan da ya mata ciki badai jikan ki ba."
Umma karima tayi ta iza Hajiya tana karawa wuta fetur nan da nan Hajiya ta d'au zugarta har tana fad'in
Ba'a isa a lakawa jikanta d'an shege ba, suje can su karata da tsiyarsu.
sai da taga ta gina Hajiya ta zauna daram kan maganar ta kafin ta koma sashinta.
in da ta tadda kanwar tata Siyama hankali duk a jagule, da bakin cikin lamarin.

A b'angaren Daddy ya shigo side d'in Aunty dan ya sanar mata, ya isketa tana waya da su Hajja Umma.
tana ganin shi ta rungume shi tana dariyar farinciki.
Daddy yaja kumatun ta yana dariya da fad'in
"Um musu an girma za'ayi jika."
dariyar farinciki Aunty ta kuma ta ce
"Jika kafi d'a wuya hausawa sun fad'i gaskiya, ban samu ba gashi d'iyata ta samar mana, Allah ubangiji ya kawo jika lafiya."
"Oh Fad'imatu ba bu kunya ana murnar an sami jika."
Daddy ya yi maganar cikin zolaya.
Aunty ta zame jikin ta tana fad'in
"Tare dai muke murnar kai ma ga murnar a fuskar ka."
ya yi murmushi mai nuni da zallar farinci.

D'iyanin Hajiya ta sa aka kira mata Daddy a waya.
yana shigowa tun kan ya zauna, ta ke fad'in
"Wai wace magana ce nake ji ne ha, wanna yarinyar tayi ciki ake son d'angwalawa Abokin turawa, to wlh tun wuri ka kwab'i maganar nan, dan basu isa su miko mana d'an da ba namu ba, su nimi uban cikin tun kan dare ya yi musu."
Daddy ya zauna yana fad'in
"Dama Hajiya ina da shirin zuwa gaya miki,
ai Hajiya bamu isa muce cikin nan ba nashi bane, dan likita ya tabbatar da cikin wata uku da sati biyu ke nan,
kin ga kuma yanzu wata d'aya ne da sati biyu da karewar auren su, sauran watanni biyun a gidan nan tayi, basai an tsauwala bincike ba ciki ya tabbata nashi ne,
mu dai kawai muyi fatan Allah ya raba lafiya, kar muyi wata maganar da zai zubda mana kima a d'auke mu kananun mutane."
Hajiya tayi shiruuu sannan ta ce
"To me yasa basu fad'a ba sai yanzu, ni fa kar aje a d'auki d'an wani a bashi, dan irin wad'an nan yayan su ke kashe iyaye ayi ta cewa d'a ya kashe ubansa alhalin dama ba uban sa bane."
"Babu ko mai Hajiya insha'allah hakan ma bazata faruba ciki kam nashi ne."
"Eh ai dama haka zakace in dai magana akan abun da ya shafi Fatima ce, duk in da aka bi da kai zaka b'ulle."
Daddy dai bai kuma cewa ko mai ba dan yasan yana kuma cewa wani abu Hajiya zata b'alle.
Chapter 30 · 0% Book details